MY BESTIE'S HUSBAND

2.2K 100 13
                                        

*_My Bestie's Husband_*


*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_21-22_*

*_Dedicated to Real Ladingo and  Feedyn Bash_*
_Wannan page din nakune kuyi yanda kukeso dashi🤗_

_____________________________
_____________________________

Wani matsiyacin kallo tabisa dashi ya matseta sosai ya cafki hannunta yajata qasa bayan ya kwarawa wutar ruwan dispenser suka sauka qasa tana turjewa tana kaimasa duka baiko saurareta ba ya cillata daki yabita gadon ta zame jikinta na rawa tana wani irin kuka ya qarayin murmushi ya shammaceta ya janyota qasa ta fado rikicaa yabita ya dannan dukansa takeyi tana yaqushinsa shegen qarfine dashi takasa tureshi saima qara luguiguiceta da yakeyi duk ihun da takeyi Masa bai qyaleta ba Saida ya wahalar da ita sosai sannan ya janye tana kuka me tafasa zuciya yayi murmushi tare da shafa gemunsa yace “Qawarki ce ta motsani Kuma ta tsorata shiyasa na hucce akanki ni ai naga hankalinki ma wlh banzaci iyanan kishin naki ya tsayaba aurene dai anriga an daura suna daya kuke amsawa idan Kinga dama ma ki qone gdan babu abinda zaa fasa jahila kawai"  ficewa yayi daga bangaren ya shiga daya bangaren kasacewar shima a gyare yake ya haura saman yayi wanka ya dawo yayi kwanciyarsa tunanin Rafi'ah ya dameshi ta dauko wayarsa ya bude hotunan da sukayi dazu kamar masoyan gaske yayi murmushi ya danna numberta ya kirata lkcn Aunty Murja tana dakin tana bata lbrn tujarar da Hajiya Sahura da Ni'imah sukazo sukayi musu abin ya wucce tunaninta shiyasa kukanma ta kasayi Ja'afar ya cucesu ya raba musu zumunci shi ko tsoron Allah ma bayaji kawai burinsa yake cikawa baruwansa da damuwar wani.

Kiranne yasasu duban wayar gabadaya ganan an rubuta My Bestie's husb yasata jan tsaki dubanta Aunty Murja tayi tace “ki daina wannan abun da kikeyi zai iya rabaki da Ubangijinki Allah babu ruwansa da mijin aminiyarki tunda ya qaddara ya zamo mijinki to dole kiyi takatsantsan sosa masa ran da zakiyi ke Kuma Allah saiya sosa naki kinsan kuwa radadin dake cikin ace Allah ya sosa ranka Rafi'ah?" Girgiza Kai tayi Aunty Murja tajata jikinta ta shafa bayanta tace “duk wani farin cikin duniya zai iya hanaki ya hanaki kwanciyar hankali saboda wannan abinda kike rainawa Rafi'ah ki taushi zuciyarki Ja'afar Wakil bazai taba janyewa qudurinsa ba tun kafin kukawo yanzun ma ya kafe balle yanzu da kike amsa sunan matarsa idan kika cika matsawa wahala zakisha"
Kawar da kanta tayi tace “nifa banasonsa ne Aunty banajinsa a ko saman halshena bare zuciyata don Allah ki qyaleni" daquwa tayi Mata tace “kin dade baki tsaneshi ba yanda ya nace Saida kika zama matarsa zai nace saikin soshi har kinyi kishinsa namiji irin mijinki shigarai gareshi wlh namiji me naci tsayawa araine dashi garama kibi a sannu kada kizo kema ki rifta harma ki fishi ruftawa" sake tsuke fuska tayi daidai lkcn da wayar Ni'imah ta shigo gabanta ya fadi ta kalli Aunty Murja itama kallonta tayi tace “daga Mana kiji abinda zatace"

A tsorace ta daga tare dayin sallama bata amsa sallamar ba sai wata uwar ashar data lailayo mata girjin Rafi'ah yabada wani dam ta miqe jikinta na rawa kuka ya balle mata tace “wlh Bestie bantaba son mijinki ba na fada masa yaqi amincewa abinda kikeji nafiki ji ke kishine yake damunki da tunanin naci amanarki nikuwa qiyayyace Ni'imah na tsani mijinki banasonsa wlh bantaba mafarkin kasancewar wannan gwamutsin ba bantaba mafarkin zuwan wannan cukurkudadiyar ranar ba...."
Ashar ta qara danna Mata sai Kuma ta fashe da kuka sukayi Shiru kowacce na kuka abubuwa da yawa na dawo musu can Ni'imah ta zabura tace “wai kece kishiyata matar mijina mijin da kinfi kowa sanin irin son da nakeyi masa Rafi'ah kin yaudareni kun cutar dani keda Ja'afar wlh ko zan mutu saina hanaku jin dadin wannan auren cin amanar gakinan gashi ku zauna nagani muddin Ina raye sai kunyi nadama sai kunsan kunci amanata zaku ganine dagake harshi dagayau zamu fara wasan abun da nakeso ki fara cirewa a ranki shine aminci da zumunci daga wannan ranar na yankeshi har abada kisa aranki zan iya kasheki da hannuna duk inda kika ganni kiyi qoqarin barin gurin donni maqiyiyarki ce ta gaske akan mijina ko kece Sahura uwar data haifeni wlh sai naga bayanki...."

MY BESTIE'S HUSBANDStories to obsess over. Discover now