*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_25-26_*
_____________________________
_____________________________Tasowa dogarai sukayi da sauri sukayi Mata cahhh suna fadin “Saita kalami yar talakawa...." Saurin daga musu hannu yayi ya miqe ya taka cikin cikar Izzarsa ya Isa gabanta tanata huci tana cije lebe, dafa hannu yayi tsammaninta marinta zaiyi sai taji ya sauke hannunta a kafadarsa ya janyota jikinsa ta fara qoqarin fincikewa yasa dukkan qarfinsa ya mannata da qirjinsa ya karbi abin mgnr yayi gyaran murya cikin sauti me nuna asalin izzar sarauta yace “da farko inayiwa baqinmu barka da zuwa tare da baku hqr a bisa abinda wannan zautacciyar tayi muku akasi aka samu baasan ta fito ba tadan hadu da matsalar brain ne idan abin ya motsa tana fuzga so do Allah kowa yayi calm down komai zai wucce am Sarkin gda da Sarkin qofa ku mayar da ita bangarenta a qara Mata tsaro don gaba kadan duka zata fara"
Yana fadin haka ya dago sakar Mata murmushi ya daga Mata yatsa ya barta tsaye sororo kafin ta ankara taji an cafeta sama an fice da ita daga gurin aka cillata a wani killataccen bangare a gdan shikuma ya koma gurin amaryarsa yana zama ta miqe ta fice daga gurin a guje ya sa aka bita itama aka riqe masa ita ya taso ya iso gareta yasa hannu ya kamota ya fice da ita daga cikin taron bangaren da aka fara kaita nan ya nufa da ita ya cillata saman kujera ya fara bala'i yana cewa “kema mahaukaciyar ce irinta da zaki biyeta ku watsarmin da mutunci a bainan nasi?Miqewa tayi tana huci tace “akanme zakace mata mahaukaciya bayan kafita hauka da kana tunanin zaka samu wannan damar ka gama shimfida son zuciyarka a banza ne kana tunanin ko ita ta qyaleka duniya zata qyaleka ne? Ja'afar Ka cutar damu Allah ya isa wlh bazamu yafe maka ba Kaine Ummul aba'isin kowacee masifa ta rayuwarmu da dadi da wuya mun jurewa juna har kawo lkcn daka riskemu Ashe Kaine qaddararmu Kaine bala'in da zai fado rayuwarmu ya rusa mu kacina son kanka da son zuciya Wanda na tabbata duk Wanda yabi son zuciya qarshensa nada......"
Wata fusga da yayi Mata ta hanata qarasa kalaminta ya cillata gadon yabita ta zulle a guje ta nufi bathroom yabita ya sake wartota ya hadata da bango yace “qarya kikeyi Rafi'ah bazan taba nadama ba a rayuwata giya nasha ko caca nayi kokuwa zina na nemeki da ita da zakice zanyi nadama? Oh God" ya fada tare da bude qofar a fusace ya fice daga dakin ta koma ta zauna tana wani irin kuka me ciwo tana tambayar kanta me hakan yake nufi kenan ya kawota bangare babu kowa ya ajiyeta babu kowa nata.Tana wannan tunanin taji an bude qofar an shigo ta dago da sauri ganin qanwar Ammi Bushira da Aunty Murja da Aunty raziqa yasata miqewa da sauri qarasawa sukayi gabanta Aunty Bushira ta Kama hannunta ta zaunar da ita tace “bazaki daina kukannan ba ko gashinan kinjawa kanki Ja'afar ya rantse bazakibar gdannan ba kinzo kenan...." Dagowa tayi da razane tace “ban gane ba?" Aunty Raziqa ce ta harareta tace “wannan haukan da kukeyi Kuna gwara kan mijinku babu abinda zaija muku sai raini da wulaqanta ita idan kishi yasata ta haukace ke mene hujjarki na haukacewa to wlh Abba yace ki kiyayi fushinsa sarai zaku raba hanya indai akan aure ne kowa ma yasan mijinku bai kyautaba to Amma shima ya zaiyi da zanen qaddararsa tun kafin a haifeshi sukayi alqawari da Ubangiji na duk wani Abu dazai faru dashi tun daga ranar da ya fara shaqar iskar duniya har zuwa Rana ta qarshe a rayuwarsa haka kema haka Ni'imah to akanme zaku haukatashi ku mayar dashi ball a tsakaninku ita ta bugashi nan ke ki bugashi can ko kin dauka saboda ya aureki don yana mijin aminiyarki babu alqalami tsakaninku to wlh ki dawo hayyacinki nasan iyayenmu basu barmu da jahilci ba saidai kana sane ka take sani sakarya kawai da takeson wasa da damarta"
Durqushewa tayi a gurin sosai kalaman Aunty Raziqa suka ratsata Aunty Murja ta dora da nata itama me ratsa bargo kafin Aunty Bushira ta cafe da cewa “gashi Allah ya baki mijin da yake sonki duniya ta shaida hakan Amma kinason yin sakacin sane masa kibi a sannu duk abinda hqr Bai bada ba to tashin hankali ma baya badashi dole yace yau a gdansa zaki kwana Ammi da Abba basuda damar sake ganinki wannan dalilin yasa zamu ari bakinsu muci musu danyar albasa Rafi'ah gdan yawa kika shigo Kuma gdan sarauta akwai qalubale a gabanki musamman daya kasance surukarki bata maraba da zuwanki dama yan uwan mijinki da suke daki daya dayan dakin Kuma su bama asan inda suka dosa ba Fulani Innah ce kawau take maraba dake sai mijinki to aikine ja a gabanki ki nutsu ki gane masoyi da maqiyi ki Kama masoyanki shima maqiyin karki canza Masa kallo karbeshi ki riritashi idan ya zaqe kai qararsa gurin Allah zaiyi Miki maganinsa abokiyar zamanki ma yanzu cikin sahun maqiyanki take yanzu haka mun barota tana alwashin saita kasheki saboda haka itama iya zama da ita zauna da ita da kyakkyawar zuciya zakiga ribar hakan anan duniya da gidan qarshe"
![](https://img.wattpad.com/cover/252522858-288-k897191.jpg)
YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomansaMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...