MY BESTIE'S HUSBAND

1.4K 87 12
                                    

*_Mbh_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

*_47-48_*

_____________________________
_____________________________

Shiru ce ta ratsa gurin na dan wani dogon lkc kowa zuciyarsa na searching abubuwa da dama mabambamta, zumbur Ja'afar ya miqe ya nufi qofa zai fita Mai martaba ya rufa masa baya shima Jamal miqewa yayi suka fita daga gdan duk wani guri da suke tunanin rafi'ah sun kasa samunta wasa wasa sai ga lkc yanata tafiya har goma na safiya shikam Ja'afar ya zamana kamar wani robbot ko bakinsa bai iya budewa sai tafasa da zuciyarsa takeyi.
Mai martaba ne yace da Jamal su juya suje gdansu Rafi'ah sugani ko taje can hakan ce ta faru suka nufi gidansu Rafi'ah Mai martaba yasa akayi masa sallama da Abba dake asabar ce Abba ya fito ganin Mai martaba da kansa yasashi qarasowa da saurinsa yanayi musu sannu da zuwa yanda yaga dum jikinsu  a sanyaye ya fadar masa da gaba yace “meye yake faruwa ne naga kamar Kuna cikin damuwa?"
Ja'afar ne ya magantu a karon farko yace “Rafi'ah batazo ba ko Abba shikenan na shiga ukuna ta shiga duniya Ina zataje hannun wa zata fada....." Jiri Abba yaji yana dibansa yayi saurin matsawa jikin motar yace “ban fahimta ba Ina Rafi'an ta tafi da danyan jego?"

Mai martaba ne ya zame rawaninsa ya goge gumi yace “wato yau mun tashi da wani iftila'i ne Alh Nuhu lfy Lau muka kwana da Yarinyar nan Amma da asuba sai ta tashi da wani yanayi me kama da samuwar tabuwar kwakwalwa hakan tasa mijinta yanke jiki ya fadi wai kafin a samu  a shawo kan tashi matsalar baa ankara ba ta sulale ta dauke danta ta fice munyi yawo sosai a garin nan tun asuba muke zagawa ko zamuyi katarin ganinta Amma Babu ita babu alamarta duk inda muka tambaya sai ace baa ganta ba to shine mukayi tunanin ko nan ta taho Kuma gashi alamu sun nuna batanan"
Durqushewa Abba yayi yana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin mummunan tashin hankali miqewa yayi ya bazama gidan da sauri ya zaro wayarsa ya fito suka sake fita sune police station sune transport agent Amma Babu wani lbr me dadi saina godiyar Allah kawai ranar yini sukayi ko ruwa basusa a bakinsu ba Basu suka hqr ba sai taran dare suka koma gda kowa zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa suna komawa gida Ja'afar ya shige bangarensa abin mamaki saiya tarar da Ni'imah a parlourn taci uwar kwalliya tana jiran dawowarsa.

Baikobi ta kanta ba ya shige ciki ya bude dakinsa tare da dauko key din daya dakin na Rafi'ah ya datse ya koma dakinsa ya haura kan gado ya hada tagumi yanajin wani zugi da radadin zuciya da bashi da misali baiji shigowarta ba saiji yayi tana wani shafa sumarsa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur ya saukesu akanta take taji tsoro ya lullubeta Amma saita dake tace “we meye na tada hankalin hakane bafa wani hauka da takeyi tsabar iskanci ne dama ba sonka takeyi ba shine take neman hanyar rabuwa dakai cikin sauqi...."
Dagowa yayi ya sake saita injin idonsa akanta sosai take a tsorace Amma batason tabar zuciyarsa ta zauna kurum kamar yanda mahaifiyarta ta qyara Mata idan ya dawo tasan duk yanda tayi tasashi jin haushin Rafi'ah ta hanyar nuna masa tana sane ta Kama hauka don ta samu damar guduwar masa da dansa, hawaye ta dauke tace “na dade Ina jiye maka zuwan wannan ranar saidai Kai ka kasa fahimta Koda yake nasan bayin kanka bane asiri ne ke dawainiya dakai badon haka ba mema zakacj da Rafi'ah Ja'afar nidai Ina baka shawara ka cireta a ranka muci gaba da rayu....."

Tsawa ya daka Mata tare da daga hannu zai dauketa da Mari sai Kuma ya fasa ya miqe tare da shigewa bathroom ya sakarwa kansa ruwa yana furzar da iska ya fito tana zaune inda ya barta yaja dogon tsaki ya dauki doguwar rigarsa yasa ya fice daga dakin ya bude Wanda ya rufe dazun ya shiga ya tada sallar nafila ya nata jerawa ba qaqqautawa bayan ya idar ya jima yanayiwa Rafi'ah da Mahir fatan fadawa hannu na qwarai.
Alqur'ani ya dauka fara karantawa zuciyarsa na karyewa sosai yanajin yanda ruhinsa ke ciwo tabbas yasan a zaman da sukayi da Rafi'ah wata ukune kawai sukaji dadinsu watanni biyar duk sun tafi a banza ne to ko watsin da yayi da ita da rayuwarta a lkcn da tana da cikin ne yasats yanke Masa wannan hukuncin na rabashi da kanta da gudar tsokarsa Mahir?
Tambayoyine da bashi da amsarsu hakadai ya rinqa zauniya Koda yayi abinda ya sawwaqa cikin karatun qur'anin saiya rufe ya rafsa tagumi yanajin yanda jikinsa ke daukar zafi alamun damuwa ta fara ratsa bargonsa ta zuba Masa ciwon gabobi da zazzabi me zafin narkar da nutsuwar ruhi.Zamewa yayi ya haye gadon ya kwanta yanajin yanda jijiyoyin kansa suke wani tartsatsin wutar azaba qwanyarsa tana neman tarwatsewa gashi Babu mataimaki sai Allah yaji sanda Ni'imah ke buga qofar yayi Mata banza saboda baisan meye yasa ba tunda ya dawo Azare ya barota a Abuja ganinta ma bayason yi idanma ya kalleta gabansa faduwa yakeyi.

MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now