MY BESTIE'S HUSBAND

2.1K 79 5
                                    

*_My Bestie's Husband_*



*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_13-14_*

_Ina mamakin mutane da basawa rayuwa uzuri, shin Ina tunaninmu yake tafiya da muke manta komai yana gudana ne bisa iko da sahalewar Ubangiji bawai ra'ayinmu da_ _iyawarmu ba? Am sorry to say sisters and brothers mgnr addini babu ra'ayi a cikinta, idan har kunya zata saki kibar halal to shakka babu aure shine Abu na farko daya kamata ki bari saboda babu abinda yafishi rashin_ _kunya a duniya Amma Kuma shi Ubangiji da kansa yake cewa_ _(WALLAHU LA YASTAHAYI MINAL HAQ) tabbas Allah bayajin kunyar gaskiya saboda haka mu cire son rai mu tunkari gaskiya komi dacinta da ciwonta, Oum hairan ba son rai take rubutawa ba gaskiya take rubutawa wannan karon🤗_

___________________________
___________________________

Miqewa tayi tsaye ta zuba masa manyan idanunta masu saukar masa da kasala a mamakance take kallonsa yayi murmushi ya juya yana tafiya yana cewa wani abune zaikaini Indonesia Amma dole zan bari sai angama komai na bikinmu saboda bazan ballo ruwa nabarki da tarewa ke kadai ba, tabbas bakida laifi a cikin wannan lamarin amma duniya bazatayi Miki adalci ba hakanne yasa na shirya sanya qafar wando daduk Wanda ya nemi uzzurawa rayuwarki"
Baijira cewarta ba ya fice daga garden din Nina dake zaune tanajinsu ta taso tace “tabdi nidai bantaba ganin nataccen mutum irin JMW ba shi ko tsoro bayaji baya ko tunanin me zaije yazo?"
Jinjina Kai tayi tace “so yake ya yankemin duk wata walwalar rayuwata Nina yacika son kansa da yawa duk wani Abu da zan nusar dashi ya kasa ganewa wai har takai ga yaje ya fadawa Dad mahaifin Ni'ima wannan haukan nasa...." Zaro ido Nina tayi tace “wht? Da gaske tabdi kina ruwa Dan kuwa duk juyin da duniya zatayi indai manya suka shiga mgnr nan to kuwa saikin aureshi Kinga aminta zata qara qarfi gaku aminai gaku kishiyoyin juna...."


Batason shirmen Nina don sosai zuciyarta take tuquqi har wani daci takeji a saman harshenta  itakam ta gamu da alaqàqai ya zatayi ne Ja'afar ya gane Kuma ya yarda batasonsa zama tayi dabar bisa gado tana jin kanta na wani juyawa yau duk arhar hawayenta ya qafe qaf yaqi zubowa namiji hankaka tabbas namiji buhun qayane namiji ciwon yatsa, tama rasa da wacce kalma zata fassarashi tayi daidai dashi Ja'afar ko iya haka yabarta ya gama da ita ya rusa alaqarta da Bestie dinta, wayarta ce ta dauki ruri tayi firgigit ta duba saitaga number Bestie gabanta yabada wani rass tunaninta lbr yaje Mata aikuwa ta kasa daga wayar sai lkcn kuka ya qwace Mata ta rinqa kuka me shiga rai itakam tana ganin masifa a rayuwarta yanzu badan mutuwa data dauke Mata Yassar ba da tuni ba wannan zancen akeyi ba.
Ji tayi an dafata ta dago ganin Nina yasata sake rushewa da kuka tace “bansan me zance da Ni'imah ta yarda dani ba a lkcn da wannan qazamin lbrn yaje Mata Nina kaina ya kulle wlh narasa gane mafitar rayuwata sai nakejin kamar na kashe kaina na hut...." Rufe Mata baki tayi tace “subhanallahi wannan ba kalmace ta Muslumci ba Rafi'ah ki daina idan fah Allah ya qadarta aurenki dashi bakida tsimi bakida dabara idan Kuma bai qaddara ba ko kinaso bazai yuwuba to ki fawwala masa komai duk wani motsinki yana yuwuwane da amincewar lillahi"

Shiru tayi kafin daga baya ta dago tace “amma mijin aminiyata Nina haba abin ya wucce tunani yakasa saurarona ya fahimci nufina wlh Koda baya auren Ni'imah ni baimin ba bawai don baikai ba aa halinsa ne baiminba banasonsa Nina ya zanyi ya gane banasonsa" murmushi Nina tayi tace “aa fah qaryane wannan wlh duk inda namiji ke kaiwa asoshi JMW yakai kawai dai kice saboda Ni'imah ne bakiji kinasonsa ba kuma ma badan dai mu Mata bamuda lissafi wlh mijinta tunda yaji a ransa batakai masa ba har ya darsa aure aransa to kuwa sai yayi ni sainaga da a auro maka bare da bakasan halinta ba ai gara wacce kasani tasanka in zata iya cutar dakai kasani idanma bazata iyaba kasani namiji fah idan yasa kansa Abu idonsa rufewa yake kunnensa toshewa yakeyi,
Sannan nifa sai nake ganin kamar itama bazata tashi hankalinta ba tunda tasan ba haramun bane" dago idonta tayi tana share hawayenta tace “bakisan Ni'imah ba bantaba baki lbrnta ba Nina Ni'imah qawatace aminiyata tun bamusan kanmu ba tun muna qanana nasani tanada zafin kishi ni da ita Tasha fadamin tsaf zata iya kashe mijinta ta kashe kanta indai yace zai qara Mata kishiya saboda bazata iya sharing din miji ba da wata to balle ni da ni kaina nasan indai na yarda na auri mijinta to naci amanar qauna kuma qauna bazata yafemin ba Ina tayata kishin mijinta saboda nasan tanasonsa fiye da yanda kike zato, nifa dana auri mijinta gara na mutu babu aure yafimin sauqi wlh ko bansan Ni'imah ba lbrn kishinta aka bani zan guji mijinta domin dawwamar lfyta da kwanciyar hankali na balle ni nice me bada lbrn"



MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now