*_Mbh_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7*_45-46_*
_____________________________
_____________________________Duka na sosai kalamansa sukayi Mata Wanda suka sanya zuciyarta lugude itakam wannan abu na wannan fam yana bata ciwon kai ta rasa meye laifinta meye ta tsare musu, shirun da yaji tayine yasashi cigaba da cewa “Al'amura sai lalacewa sukeyi gashi wadda zatayimin wannan alfarmar daga Badi'ah sai Karimah to Badi'ah mahaifiyarta ta hanata dazun take fadamin ta siyi gadon Amma Hajiya Kaltume tace idan ta bada Allah ya daidaitata ita Kuma Karimah babu ita a jadawali saboda kasancewarta qarama a gidannan na rasa ta Ina zan bullowa lamarin nan Allah kibani mafita"
Numfashi taja tare da yunqurawa ya taimaka Mata ta tashi zaune ta dubeshi tace “in advise ka cire jinin bayi Kuma karfa daga sashinka hakan zaisa ka rinqa samun matifa cikin rayuwarka Ja'afar don Allah kayimin wannan alfarmar inaji ajikina idan naci gaba da zama matsayin mata a gareka zamu wanzu cikin rayuwar qunci Koda kasancewar nasan duk wani Abu daya fado rayuwata to yardar sarkin sarkice Wanda baa masa dole,Ja'afar bandamu da nakasance cikin farin ciki ba indai farin cikina zai tafa darajar wani shiyasa a rayuwata bancika damuwa da dole saina rabi wani ba tabbas abinda Hajiya Kaltume ta fada maka gsky ne Koda akasin hakan ne Toni na gasqata maka Ni yar bayice Amma ba qasqantattun bayi ba bayin Allah wadanda suke yarda da duk wani hukunci nasa a ban qasa Ina jiran ka yanke duk hukuncin da zaka yanke Allah na roqeka kada bakawa kowa ikon kawo gadon daraja idan hakan ta kasance ku koremu daga garin azare...."
Saurin rufe Mata baki yayi yana girgiza Mata Kai ta zabura ta miqe cikin bala'in da baitaba tunanin ta iyaba ta nunashi da yatsa tace masa “saime Ja'afar shine me danka kirani baiwa kuka ka kirani karfa Ina taka baiwar daka halitta sannan Ina taka karfar to duk abinda zakace ko a fada maka ka fadamin na shirya karbarsa Allah ya tsinewa Wanda ya fas...." Dauketa yayi da Marin daya sanyata kifewa a gadon daidai lkcn da Hajiya Innah ta shigo ta rafsa salati tace “meye hakan magaji bakada hankali zaka Kai hannunka jikinta yarinyar da ba lfy ta isheta ba meye ma ya farune"Huci yakeyi kamar Wanda ya hadiyi maciji ya sake nunata da yatsa kawai sai ya juya ya fice a fusace Hajiya Innah ta matsa da sauri ta riqo Rafi'ah tace “meye ya farune kun ninkeni baibai fah" cikin kuka ta rinqa zayyanewa Hajiya Innah abinda ya faru taja fasali tace “to shine zaki tada hankalinki har kina daga muryarki sama da tasa bayan kinsan halin mijinki ko qalau yake ba hqr ya cikaba balle yanzu da kansa yake dawa Rafi'ah dole ke hqr ya Kama domin ke aka cuta"
Sosai ta rinqa kwantar Mata da hankali harda tayi shiru ta dauki jaririn ta fice dashi tunanin duniya ya damu Rafi'ah gabadaya komai ya daukar Mata zafi tanason ta samu wanda zatayi Hira dashi taji dadi babu Hajiya Innah ta saka Mata ido ko yan'uwanta ne sukazo bata barin dakin saboda kada ta fadi wata mgn da zata fallasa sirrin gidan sarautar tayi kuka kamar ranta zai fita ita daya kamata a rarrasa ita akewa tsawa harda mari saboda gskyrta wannan dare dukka bangarorin babu Wanda ya rintsa Ja'afar tunanin maganganun da Rafi'ah ta fada masa ne da Kuma mafitarsa da dansa ya hana idonsa rintsawa ita Kuma alhinin wannan jarabar rayuwa ta zaman qasqanci da boranci tun zamanin quruciya sune suka hanata rintsawa Hajiya Innah kuwa tunanin ta inda zasu bullowa wannan al'amari da yanda zaayi su samu gadon daraja ne ya hanata bacci inda Hajiya Fatsum Kuma bokanta yace daga ita har Ni'imah su tube tsirara kowacce a bangarenta su tsaya a tsaye su kwana a haka kada suyi gyangyadi domin sunayin bacci asirin da suka qullo na haukata Rafi'ah kansu zai koma itakuwa Hajiya Kaltume neman ta inda zata fara bullowa Ja'afar da iyalinsa ya hanata rintsawa Abu na farko daya kamata tayi shine tasan yanda zatayi ta qara shiga tsakaninsa da Rafi'ah sannan ta sace wannan jariri kafin wayewar gari.Kiran sallar asubar farko Rafi'ah ta tashi da wani matsanancin ciwon Kai ta riqe kan da sauri tare da fara karanta izaja'a ta dan samu relief daidai lkcn da taji an bude qofar an shigo kasancewar da duhu bataga me shigowar ba ana gama shigowa Kuma sai aka haskenta ido da wata fitila me masifar haske ta yunqura zata miqe abinka da mara cikkakiyar lfy sai tashin ya gagara ta rintse idonta daidai lkcn da taji an watsa Mata wani ruwa anyi baya da sauri.
Aikuwa saita wani yi tsalle ta miqe ta qwallah qara tare da damqar jaririn ta qanqame Hajiya Innah da Ja'afar har gware sukeyi wajen shigowa, Hajiya Innah ta kunna glub ta rintse idonta da sauri saboda tashin hankalin data gani inda Ja'afar ya nufeta a guje yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Rafi'ah meye hakan lfyrki kuwa tsirara fa kikayi...." Daukeshi tayi da wani mahaukacin mari tana qara matse danta a qirjinta tana wata dariya me hade da kuka tana cewa “ina ruwanku munafukai azzalumai algungumai dukkanku saina kasheku duk Wanda yazo gurina saina harbeshi danane ni na haifi abuna babu me rabani dashi daga yau nasa masa suna mai martaba Muhammadu Mahir eh sunansa kenan sunansa kenan Allah sunansa kenan dana sunansa kenan Ja'afar ya mutu Mahir maraya ne hhhhhhh Ja'afaru ka mutu ka huta nima na mutu na huta kowa ya mutu ya huta..."Wani baqin tashin hankali da dimuwa Ja'afar ya shiga ya matsa gurinta saikuwa ta rarumi kaskon wuta ta jefosa dashi tana qyalqyala dariya tana cewa “bazan baka danaba nawane ni kadai kufice ku fice nace ku fice ko na yankaku na shanye jininku hhhhhhh suwaye nan kowa bayasona Ni inason kowa kowa bayaqina ni inaqin kowa..….."
Tashin hankali yasa Ja'afar yin kanta a guje aikuwa suka Kama kokawa daqyar yayi nasarar karbar yaron ya miqawa Hajiya Innah da taketa sallallami da kuka ya dauki doguwar riga yasa Mata ta hankadeshi ta miqe ta nufi qofa a guje shima ya bita yasawa qofar key ya daka mata tsawa itama kuwa saita daka masa tsawa tare da fuzge ribbon din data kame gashinta dashi ta kurma ihu tana wani dukan iska tana cewa “ni kubani dana Babu inda zaa kaimin dana abani abuna ...." Hadata yayi da jikinsa ya rungumeta sosai a jikinsa kawai saiya fashe da kuka ya bude baki yace “wai... Waime kikeyi ne haka Rafi'ah meye yake damunki ne bakiga bakida lfy bane...." Hannunta ta dora a bakinta tace “shitttttt ni qalau nake nafika nafi babanka nafi babarka lfy ba sunana Rafi'ah ba sunana Deluwa yehhhhh Deluwa takan bola Deluwa takan titi Deluwa ta kowac...."
Hade bakinsa yayi da nata ta kuwa gasa masa cizo ya janye da sauri harshensa har saida ya tsage ya koma gefe yana kallonta Hajiya Innah daketa salati ta Kiran sunayen Allah tsarkaka tace “sai hqr Ja'afar sun haukata maka Mata innanillahi wa innah ilaihirraji'un....." Dagowa yayi da sauri yace “wht hauka Kuma Innah wanne irin hauka" sake kwashewa Rafi'ah tayi da dariya tace “eh da gaske ni mahaukaciya ce daga yau sunana Deluwa mahaukaciya yar macukule...........Zubewa yayi rijib a qasa sumamme tsabar tashin hankali Hajiya Inna tayi wajen gdan a guje tana ihu tana Kiran a kawo Mata dauki nan hadimai sukayo ciki a guje daidai lkcn da Jamal ya shigo gdan shima isowarsa kenan daga Rasha ya tawo ganin dansa dan yayansa da matar yayansa da baitaba gani ba ya siyo gadon da aketa badaqala akan samuwarsa sannan ya hadowa matar yayansa kayan fitar suna akwatu guda.
Tun daga bakin qofa yasan gidan babu lfy yana shigowa yaga wata mace ta fice qunshe da Abu a hijjabinta da mugun gudu ganin yanda gidan yake a hargitse ga Kuma gajiya yasa baibi takanta ba ya nufi cikin gidan inda ya hangi mutane dodo guda a qofar bangaren Hajiya Innah haka ya rinqa kukkutsawa har ya Isa cikin part din wata muguwar faduwar gaba yaji lkcn daya riski yayan nasa warwas a qasa kamar matacce aikuwa wata alkafura yayi ya dira kansa ya fara danna Masa qirjinsa tare da neman ruwa ya fara quga Masa tsayin lkc sannan ya fara sauke ajiyar zuciya ya bude bakinsa da sunan matarsa.
Sai lkcn aka ankara da bata cikin dakin aikuwa nan aka bazama nemanta lungu da saqo Amma Babu ita babu lbrnta Jamal ne yace lkcn da Yana shigowa yayi karo da wata mace ta fice daga gdan a guje Amma baibi takanta ba ya zaci mahaukaciya indo ce, salati Innah da Mai martaba dama sauran mutanen dake gurin suka dauka Ja'afar kam hade Kai yayi da gwiwa duk wani tunani ya qwace masa baimasan meye zai tuna ba a hankali yace “suwaye suka haukatata me tayi musu suka azabtar da ita da ciwo me cin zuciya da lalata ruhi Ina zata Ina take me suke nema me tayi musu sun illatata......."_Hqr My Fan's am sick wlh_
_More comments_
_More Typing_*_Ummuh Hairan_*
YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomanceMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...