MY BESTIE'S HUSBAND

1.8K 92 12
                                    

*_My Bestie's Husband_*


*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_17-18_*

___________________________
___________________________

Ficewa tayi da sauri har tana neman kifawa yabita da ido yana fitar da wata iska me zafi shima ya fito megadin ya Kira ya tambayeshi ko me gidan yananan ya amsa masa da “Eh yau yana hutu" ajiyar zuciya yayi yace “kayimin sallama dashi" da sauri megadin ya nufi cikin gidsn domin yasan waye Ja'afar Wakil a parlourn ya tarar dasu aunty Raziqa tanata rarrashinta tana tambayarta abinda ya faru.
Dubansa sukayi yace “Abuh Aulad ake Kira a waje" fitowarsa kenan suka fita tare da mamaki suka rungume juna Dr Naseer yace “Prince JM yau a gidana Amma dai ba zuwana bane wannan don nasan bakamasan gidana ba rabona dakai tun a Victoria I-land 3 years kenan" hularsa ya cire yace “wlh amaryata na kawo gdanka shine nace a kiraka nasan gdanka mana bandaisan matarka ba Ashe yayarmu ce?" Mamakine ya cika Dr Naseer yace “wa kenan?" Harararsa yayi yace “wace baquwarku yau?" Saita nutsuwarsa yayi yace “pretty nagani a parlour tana kuka dama tare kuke?" Murmushi yayi yace “itace amaryata wlh yarinyar tana wahalar dani sosai narasa ta Ina zan bullo Mata ta fahimceni" sake dubansa yayi yace “amaryarka ko budurwarka?" Dagowa yayi yace “duk daya itan budurwa tace Kuma amaryata saura kwanaki 29 idan ka cire yau saura 28 idan banda gobe saura 27 so ba laifi bane donna kirata matata fatane da Allah zai cikashi"

Wani numfashi Dr Naseer yaja yace “amma yaushe kayi aure inace baafi 3 mouths ba?" Daga Masa Kai yayi yace “eh ai kasan hudu Allah yace muyi ni ba zuwa nayi kayi jaridarka akaina ba ka kula kuma kayiwa matarka kashedi kada ta kuskura tabar Rafi'ah ta tafi ko nakai goman dare banzo ba zanzo ta jirani nazo na mayar da ita gida" yana fadin haka ya miqa Masa hannu yace “ka Bata kulawa sosai itadin rayuwata ce" mota ya shiga yabar Naseer tsaye shanye da baki Saida ya fita daga gdan megadi ya kulle qofar sannan ya juya ya shiga har yanzu kuka takeyi ya zauna ya zuba Mata ido ya dade yana nazarinta kafin ya furzar da iska yace.
“Ina kika samo wannan dan Izzar Rafi'ah Ja'afar Wakil fah?" Miqewa aunty Raziqa tayi tace “wai dama shine ai mijin aminiyarta ne meye hadinta dashi?" Kallon Raziqa yake yace “soyayya Mana harma da ranar aure yacemin saura 29 days a daura aurensu ni abokinane tun muna secondary bashi da sauqin mu'amala Izzar masifa ke gareshi indai ya nuna abu yace yanaso to ko zasusha wahala dagashi har abin saiya sameshi baya kula mace duk kyaunta nayi mamaki da akace zaiyi aure yasha fadamin shifa mace bata gabansa zai iya rayuwarsa shi kadai saboda baison damuwa to sai gashi baifi 3 mouths da aureba ya dauko wani aure ya akayi Rafi'ah?"
Matsawa tayi gsbansa ta Kama hannunsa tana kuka na fitar rai tace “wlh bansani ba bansan tsautsayin da yasa yasanni ba Uncle kayi wani abu akai mijin Bestie dinane ya yakeso nayi idan taji wannan baqin qudurin nasa?"

Miqewa Naseer yayi yace “hmmm ai kawai hqr zakiyi don wlh tunda kika kuskure kika fada komarsa to sai ya samu ko ta tsiya kota tsiya-tsiya" sake zubewa tayi a gurin ta riqe qafar Aunty Raziqa tace “nashiga ukuna meyesa kowa abinda yake fadamin kenan wlh banasonsa" kamota Raziqa tayi tajata dakinta tunda taga qanwar tata tasan tana cikin tashin hankali amma batayi tunanin yakai hakaba, zaunar da ita tayi tace “ya akayi haka Rafi'ah garin yaya har kika bashi dama ya tura gda Abba ya amsa har suka karbi kudinsa bayan kinsan mijin aminiyarkine"
Tsayar da kukanta tayi tace “kina zarginane aunty Raziqa yaushe na zama maci Amana da zan yarda da wannan hargitsin hatsin barar wlh bantaba bawa Ja'afar dama ba komai nasa iko yake gwadamin banasonsa Amma yace dole ne ma nasoshi Ni Kuma tsanarsa nakeji"
Shiru sukayi na dogon lkc kafin aunty Raziqa tace “Hmmm! To Allah ya kyauta Amma akwai qura Wakil family basuda sauqi akan qudurinsu tare mukayi karatu da Karimah qanwarsace babansu daya itama haka take indai tace tanason abu ta saita sameshi kiyi addu'a kawai Allah yasa hakan shine yafi alkhairi sannan kisa a ranki miji yafi qawa duk kuwa girman shaquwarku to wacce shaquwa ma ta rage ai babu ita tunda namiji ya shiga tsakiyarku kishine zaku fafatashi na mutuwa wannan shi ake Kira ranar biyan buqata rai ba abakin komai yakeba qanwata bazan zugaki kici amanar aminiyarki ba Amma idan ya dage ki hqr ki karbeshi dama wani lkcn ana samun haka garashi ma aurenki zaiyi wasu lalacewa sukeyi a titi yaqine yake tunkaroki qarfinki bazai qwaceki ba sai taimakon Ubangiji da samun yardar mijinki...."

MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now