MY BESTIE'S HUSBAND

2.7K 104 14
                                        

*_Mbh_*


*_Oum Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7


*_59-60_*

________________________________
________________________________

Yana fadin haka ya fice da sauri ya dauki motar Jamal ya nufi gdan Alh Hashim Saida yaje bakin get din sannan ya Kira Alh Hisham yace masa yanason ganin Rafi'ah mamaki ya cika Alh Hashim wannan wanne irin mara kunyar mutum ne a wannan tsohon daren yazo Wai yanason ganin matarsa, to dake ba me zafafawa bane haka ya kalli Rafi'ah yace "kije ki karbo saqo gurin mijinki a waje" Saida gabanta ya fadi tayi qasa da kanta ya sake kallonta yace "jiranki fah yakeyi yace sauri yakeyi"
Miqewa tayi a sanyaye ta fito megadi ya bude Mata get ta nufi motar yana tsaye jikinta ya harde hannunsa a qirjinsa ta iso kanta na qasa yayi murmushi ya bude Mata yace "shiga" kallonsa tayi tace "Alh yace saqo zaka bani" baice Mata komai ba ya Kama hannunta ya jefata a motar ya shiga shima ya zauna ya zubanta ido yanajin wani sanyi a zuciyarsa cikin sarewar zuciya yaji hawaye na zubo masa ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa yace "baayi ba bakuma zaayi kamarki ba matata ke kadaice ke Jan ragamar zuciyata dana rasaki saina zabi na rasa kowa da komai don Allah ki mulkeni bisa adalcinki kinji?"
Sanyi jikinta ya qarayi yana qoqarin tada motar tace "naji JM Ina zaka kaini a tsohon darennan don Allah" yana murzu sitiyarin motar yace "kowa zai kwana bargo daya da matarsa gwauro zai rungumi pillow Ni Kuma sai abarni da tufka da warwara kema kinsan bazai yuwu ba dole yau sainaji dumin da na dade Ina maraici"


Magiya ta shiga yimasa Amma dake ance Mai hali baya fasawa kuma Koda shekara dari ka rabu da mutum tambayeshi wani abun ba hali ba, hakance ta faru yayi biris da ita Saida sukaje qofar wani hotel ya shiga yayi parking ya fita ya kulleta ya jima sannan ya dawo ya bude ya riqo hannunta Sai matsar hawaye takeyi baiko kulata ba yajata suka shiga ciki ya bude qofar dakin suka shiga ya kulle tare da zare mukullin yayi miqa tare da salati yace "haba yammata ke yanzu bakifi jin dadin yanayin ba?"
Zama tayi ta hade kanta da gwiwarta tanaci gaba da sharar hawayenta batasan me yakeyi ba saida taji ya dagota ta miqe tajita a qirjinsa ta lumshe idonta tare da Jan ajiyar zuciya shima yaja yace "kullum Ina addu'ar sake juyowar wannan lkcn" daga haka ya fara qoqarin zare Mata hijjab dinta ta riqe tare da bude baki zatayi mgn yace "karki hanani wife don Allah kibarni na huta" sake langwabe Masa tayi tace "amma JM kowa fah zai gane ka bari mu koma gida man..." Manna bakinsa yayi a nata yace "haqiqa bazan iyaba jira na mara rabone Rafi'ah nikam inada rabo saboda haka in bakyayi kibarni nayi" daga haka ya fara zare Mata hijjab din bayan ya cire ya dagata cak ya dorata a gadon tare da hade bakinsu Yana aika Mata da wani zazzafan kiss da yake nuna asalin maitarsa gareta duk yanda taso hanashi jin dadin daren nan Saida yaji tayi kuka da magiya har ta gaji ta lura Ja'afar din ya qaro wulaqanci da idan tayi masa magiya yakan saurara Mata Amma yau magiyar tata sai tazama kamar zugi.


Haka suka kwana yayi kwanan farin ciki rayuwarsa ta dawo daidai ita Kuma tayi kwanan wahala dakansa ya hada musu ruwa sukayi wanka ya tayata ta shirya yanata rarrashinta ita Kuma sai fushi takeyi haka suka fito suka nufi gdan Alh Hisham a harabar gdan suka tarar da Alh Hisham ya qarasa suka gaisa itakam wuf tayi ta shige ciki ya fada gadonta tana mayar da numfashi Bari'ah ta shigo ta sameta ta rinqa yimata tsiya kunya ta hanata cewa komai, komai batajin dadinsa sai bakin shayi kawai Tasha ta fito suka sake rankayawa gdan si Hajiya Rakiya daganan suka dunguma sai azare, aka taresu cike da murna kowa yana tayasu murna a gidan sarautar bayan komai ya nutsane Mai martaba ya dubi Fiddausi yace "ina babarku Kaltume?" Sunkuyar dakai tayi tana matsar hawaye tace "Allah ya qara maka lfy jiya bayan tafiyarku ta fice itama ita da Jakadiya Indo suka tafi unguwa a hanya sukayi hatsari aka dungumesu sai asibiti itadai Indo ta cika bayan ta tona musu asiri Wai Ashe barin Yarimah Ja'afar masarautar Nan duk shirinsu ne sune sukayi masa kurciya shida matarsa Amma ba sune suka haukata Rafi'ah ba yanzu dai zancen da nake maka innanmu tana asibiti qafarta daya ta fita fit dayar Kuma ta karye an dorata haqoranta kusan goma sun fice bayan mummunan ciwon data samu a fuskarta"


You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 09, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MY BESTIE'S HUSBANDStories to obsess over. Discover now