*_My Bestie's Husband_*
*_Oum Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Dedicated to Mom twins and Ummu Safnah🤩_*
*_9-10_*
Da wani irin sauri ta dago ta kalleshi ya miqe tare da daganta gira yace “wannan shine matakin qarshe da zan dauka indai burina ya kasa cika to zan rusa farin cikin kowa Rafi'ah kinsani kinsan nasani aurena dake ba haramun bane shin bayan Allah da manzonsa wa kikeso ki birge, wa kikeson farantawa da zakiyiwa kanki asarar masoyi?"
Kallonta yayi na dan lkc kafin ya hadiye wani yawu me zafi yace “dole cikin sharrudana idan na kiraki ki daga indan kikaqi na rantse da kadaitar zati saina dawo Miki da qawarki gda domin batada wani amfani a gurina ba ita nake buqataba ke nake buqata haba haba Rafi'ah shin waima kintabajin inda akayiwa namiji dole ne nifa a duniya ke na faraso tayaya zanyi sake damata ta kufcemin?"Baijira cewarta ba ya juya Saida yaje qofar hall din ya juyo yace “zan kiraki anjima ki kula da kanki" yana ficewa ta zube a gurin cikin toshewar qwaqwalwa da rashin madafa tabbas tana cikin ha'ula'i tama kasa tuna abinyi sai jujjuya biro da takeyi idonta hawaye nata sitirya tanajin yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi kwantar da kanta tayi saman kujerar tanajin wani zazzabi yana sauko mata ita dama bata iya sanya damuwa aranta ba yanzu zata fige ta lalace, tananan zaune kamar hoto batasan sanda hall din ya cika da mutane ba saiji tayi an dafata ta dago idanunta da yayi jajir saboda kuka ta saukesu akan Nina.
Nina tace “naga mayenki ya fita dame yazo?" Numfashi ta sauke tace “ya akayi yasan inda nake?" Shafa Kai Nina tayi tace “guy dinne kwarjininsa ya Isa yanda baka Isa ka Raina masa hankali ba wlh tambayarki yayi akazo aka nemeki baa ganki ba shine yace a samo masa wata da takeda kusanci dake so shine akazo aka kirani Ina zuwa na raina kaina Ashe ma Prince Ja'afar ne tabdi aikuwa kina ruwa don wlh soyayya da yayan sarauta bala'i ne baqin naci ke garesu indai su suka furta sunasonka Amma idan aka samu akasi Basu sonka ai ka kade har ganyanka"Fasali ta sauke ta share hawayenta ta miqe saboda ta haqiqance komai ma yauma bazata gane ba wani garden ta nufa ta samu guri ta zauna ita kadai qwal kowa yana gurin daukar darasi ita kuma zuciyarta tanata kaiwa da komowa wajen tunanin mafitarta akan wannan sarqaqqen lamari daya tunkarota babu shiri tunda ta zauna ta kasa samawa kanta mafita ji tayi gabadaya makarantar ta daukar Mata wani masiffafen zafi idan taci gaba da zama komai zai iya faruwa da ita.
Wannan tunanin yasata tashi ta koma daki ta dauki hand bag dinta da kudade ta fice batare da tabari Nina taganta ba ta samu shatar mota har Azare babu zato kawai Ammi sai ganinta tayi Aunty Murja ta miqe ta tareta tana cewa “subhanallahi uwar manya meye ya sameki a goshinki haka?"
Fadawa tayi jikinta ta rushe da kuka ta kasa furta ka kalma daya hakan yasa tajata suka shiga ciki Ammi ta miqe tabi bayansu kanta ta dora a saman qafar Ammi tace “Ammi..." Amsawa Ammi tayi tana shafa kanta tare da zame Mata dankwalinta tace “kinasona Ammi?" Mamaki tambayar tabasu suka kalli juna anti Murja tace “to uwar manya waye zaice bayasonki wlh munasonki"Ajiyar zuciya tayi tace “meyesa yakeson kasheni da kalamansa?" Abin ya daurensu Kai suka hada baki sukace “waye?" Kuka ta sake sawa tace “my Bestie husband" a razane suka dago dukkansu sukace me yayi miki?" Cikin matsanancin kuka tayi musu bayanin komai Ammi ta rinqa sallalami tana tafa hannu inda anti Murja tayi shiru itama tana mamakin wannan tashin hankali.
Dagowa anti Murja tayi tace “no wonder biri yayi Kama da mutum wlh tun ranar da yazo ya kaiki makaranta na fahimci wani Abu gashi kullum sai yazo yagaida abbanku" Ammi ce tace “tabdi Amma wannan yaro yakai mara kunya to yasaketa Mana ba kansa zaiwa asara ba shashasha ya dauka ke sakarya ce da zaki biye masa kuci amanar aminiyarki har wani da aure aa da uban aure yakesonki" fada Ammi takeyi ta inda tashiga ba tanan take fitaba kamar ta ari baki tare da yiwa yar tata kashedi me qarfi da nasiha Saida taga hankalinta ya dan kwanta sannan tace “kiramin shi na tsawatar masa" daukar wayar tayi da murnarta zata kirashi Aunty Murja tayi saurin riqe hannunta tace.
YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomanceMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...