MY BESTIE'S HUSBAND

1.4K 83 13
                                    

*_Mbh_*


*_Ummuh Hairan_*


*_43-44_*

_Special gift to my Luvly daughter ki Jima kiyi qarko sannan kiyi albarka Allah ya albarkaci rayuwa yata ta kaina Ummi son qauna fisabilillah😘_

_____________________________
_____________________________


Tunda ya shiga dakin ya hade Kai da gwiwa kuka yakeyi sosai kamar yaron goye zuciyarsa na azalzalar sa ya tafi Azare ya gano lfyr matarsa da cikin jikinsa Amma babu dama tsoro yakeji kada Ni'imah ta fahimci inda ya dosa ji yake kamar idan ya bata Mata rai qonashi Ubangiji zaiyi dabara ce ta fado masa ya miqe da sauri ya rufe qofar ya shige bandaki da waya a Hannunsa ya fara duba number Rafi'ah Amma Babu a wayarsa tsoro ya qara cikashi gami da mamaki duk inda zai duba baigani bs hakan yasashi kiran Hajiya Innah ta  jima tana ring sannan ta daga daga yanayin muryarta yasan akwai damuwa.
A gaggauce yace “Am Innah Ina Rafi'ah?" Numfashi taja cikin tausayawa halin da dan nata yake ciki tace “anya magaji kana addu'a kuwa" katseta yayi da cewa “inayi Inna please kibani Rafi'ah magans nakeson yi da ita" murmushin qarfin hali tayi duk jikinta yayi sanyi tabbas akwai alamun nasara wata biyu an tafi uku ita kanta baya kiranta tunda ta kirashi tayi masa nasiha tare da fada masa halin da matarsa take ciki na yawan damuwa da kuka ga ciwon Kai daya sata a gaba ko abinci tasa a gaba saita kasa ci idan ta tambayeta sai tace  ita ba damuwarta yazo gareta ba damuwarta ya daga wayarta taji lfyrsa Amma yayi block contact nata kota Kira baya shiga.
Sake katse Mata tunani yayi da cewa “don Allah Inna kibani ita wlh inajin idan banjita ba komai zai iya faruwa Inna ko wani abu ya farune?" Numfashi ta sauke tace “akwai damuwa me tsanani a tattare da Rafi'ah yanzu dai ma kar naja maka zance bata gidannan tana babban asibitin Bauchi suna treatment nata sakamakon jininta da ya hau yaqi sauka yau kwana uku batasan waye akanta ba Amma sunankia take ambata dazu ma da mai martaba yazo sunce indai jininta bai sauka zuwa wayewar gari ba to zasuyi Mata Cx su cire cikin jikinta me watanni bakwai saboda idan aka basshi zaa iyayin biyu Babu ba itan babu shi...."


Katseta yayi da cewa “Wht Innah Amma shine baku fadamin ba" murmushinsu tayi na manya tace “ai Wai da mukaga ba sune a gabanka ba Ja'afar duk da nasan wani abun bayin kanka bane Amma yana ishe hali nidai banga abinda yarinyar nan zatayi maka ba ka dauki wannan matakin akanta kafi kowa sanin yanda akayi auren nan bataso iyayenta basaso rabone kawai me gaggawa ya baka saar mallakarta Amma tazama abar wulaqantawarka kada ka sake kakai hqrn mutum me haquri da zurfin ciki qarshe idan ya kwance maka rawani duk duniya babu Wanda ya Isa ya daura maka so ka kiyaye"
Kashe wayar tayi ta shiga dakin da Rafi'ah take kasancewar itace a gurinta taqi bari a fadawa iyayenta abinda yake faruwa koda sukazo asibitin kafin jikin ys rikice tace kada a fadawa Abbanta idan yaji akwai matsala, hakan tasa sukayi Shiru Mai martaba da Hajiya Innah da Karimah sune suketa jele sai Badi'ah yar Hajiya Kaltume ce Amma itama zakkace batayo halin uwa ba  zuba Mata ido tayi cike da tausayi duk ta kumbura ta dashe kamar bayan hawan jinin ma akwai wani abin dayake damunta daidai lkcn ta wani zabura alamun allurar ta saketa idonta a rufe Amma sai bige bige takeyi ta qarasa da gudu ta riqeta abinda ya janyo hankalin Karimah ta shigo da sauri ganin yanda matar yayan nata ta datse harshenta tana make make jikinta yana jijjiga yasata fita a sukwane ta Kira likita ya biyota da sauri suka shigo daqyar ya samu yayi Mata allurar kashe jiki sannan ya Kira sauran ma'aikatan ya dubesu yace.


“Wannan bazatakai gobeba a yau ayi Mata aiki arabata da cikin nan idan ta qara awa daya zata farka alamominta sun nuna zata iya kamuwa da ciwon jijjiga Wanda zai iya haifar Mata da depression domin kuwa akai damuwa danqare a zuciyarta" Babu bata lkc suka sanya Mata kayan theater suka turata suka shiga da ita dakin theater  sai a lkcn ne Hajiya Innah ta Kira Mai martaba ya daga take fada masa halin da ake ciki tare da cewa “Ranka ya dade fah abinnan yafi qarfin Shiru a fadawa iyayen yarinyar nan likitoci sun shiga da ita dakin aiki Amma sunce sai wani shaqiqinta ko mijinta ko mahaifinta yasa hannu sannan zasu tabata" miqewa yayi daga kishingidar yace “to bari yanzu zan fito" dakansa ya tuqa mota hankalinsa a tashe sai office din Abba ya rakitosa suka tafi asibitin Abba baisan meye yake faruwa ba Saida sukaje likitan yayi masu bayani ya shiga rudu da tashin hankali ya dago yace “ina mijin nata to ranka ya dade ai huruminsa ne wannan" qasa Abba yayi da kansa yace “bayanan yana Abuja baimasan abinda yake faruwa ba Amma zamu sanar dashi yanzu dai kasa hannu a ceto rayuwarta yafi komai muhimmanci.

MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now