MY BESTIE'S HUSBAND

1.5K 93 18
                                    

*_Mbh_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_41-42_*

_Special gift to all fan's tun daga WhatsApp Facebook telegram da Wattpad inajin nishadi idan naga comments dinku Ina gdy ku huta da wannan😘_
_____________________________
_____________________________

Numfashi ta sauke tana qoqarin shanye kukanta tace “amma me nayi maka JM don Allah kayi hqr tun kafin ka fadamin laifina inasonka bazan iya jurewa wannan sauyin da kake neman wanzarwa tsakaninmu ba" numfashi shima ya sauke yace “calm down please ki kwanta ki huta babienmu nason hutu da safe zamuyi mgn"
Bata iya jayayya ba hakance tasata cikin sanyin murya tace “shikenan kayi bacci cikin aminci Allah ya tsaremin Kai" kashe wayar tayi ta koma ta takure a saman gadon tana saqe saqe ta rasa tuno abinda tayiwa mijin nasu kwanciya tayi tana shafa cikinta da ya fara motsi jiya ta sauke ajiyar zuciya tanajin qaunar abinda ke cikinta a wannan daren dai daga ita har Ja'afar babu wanda yayi bacci shima din daya fita bai iya nufar gidansa ba asibitinsa ya nufa yayi parking a mota ya qarasa kwana saida yayi sallar asubz sannan ya juyo ya dawo gidan sarautar, a fada ya tsaya akayi zaman fada dashi sannan ya shiga gidan tana kitchen sanda ya shigo ya shige ciki yayi wanka ya canza kaya ya dawo parlon ya zauna,
Saida ta gama shirya breakfast dinta ta fito tana jerawa a dinning taji gyaran murya juyawa tayi da sauri suka hada ido ajiyar heart tayi ta fadada murmushinta ta nufishi duk wata gaba ta jikinta tana rawa tana zuwa ta zube a qasan carpet din ta Kama kyawawan yatsun qafarsa tace “barka da safiya mijina" janye qafarsa yayi yace “ki bani abinci yunwa nakeji" miqewa tayi ta nufi dinning din ta hado masa   kunun gyadar da tayi ta dauko masa doya data soya sai farfesun kifi tarwada ta kawo masa ta ajiye a gabansa ya sauko qasa cike da zumudi ya faracin abincin, cokalinsa uku a kunun ya ture ya sake Kai doyar bakinsa ya furzar tana kallonsa gabanta na faduwa ya ja farfesun yakai bakinsa kawai sai taga ya ture plate din yaja tsaki ya miqe ya shiga ciki.


A mamakance Kuma a tsorace ta miqe tabi bayansa ta bude dakin ta shiga ya juyo ya kalleta itamma shi take kallo ta matsa a hankali dan nesa dashi saboda har yanzu tanajin Marin da yayi Mata jiya tace “kace kanajin yunwa naga Kuma bakaci abincin ba ka tashi" a hasale ya dago yace “me kikasawa abincin nan yake daci..." Da sauri ta kalleshi ya dakanta tsawar da Saida tasa dan cikinta ya dunqule yace “magana nakeyi Miki kin kafeni da ido" idonta ne ya cicciko da ruwa tace “wlh bansa komai ba...."
Figarta yayi yace “qarya kikeyi kice bakisa komai ba kinsa komai muje kici kiji" a gaban abincin ya dangwarar da ita yace “kici kiji" daukan kunun tayi takai bakinta tasha ita bataji dacinba ta dago tace “ni banji ba" masifa ya rinqayi ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba itadai babu abinda takeyi sai kuka ya juya zai fice tabishi da sauri ta riqoshi ta fada jikinsa yasa hannu ya rungumeta sukayi Shiru na dan lkc kafin ya dagota yasa bakinsa yana lasar hawayenta yajata zuwa ciki ya zaunar da ita yace “me kikewa kuka?" Kwantar da kanta tayi a jikinsa tana shafa bayansa ya gane abinda take nufi hakan yasa ya dagata cak ya nufi ciki da ita ya kwantar da ita ya kwanta a gefenta ya zubawa fuskarta ido.

Murmushi yayi yace “meyesa ne Rafi'ah" a hankali ta bude idonta tare da janyo jikinta ta hade bakinta da nasa ya sukaja numfashi tare sun dade a haka tana shafa sumarsa shima yana shafa nata sosai suka tsuma juna kafin su Kai ga cimma burinsu sun jima sosai sannan suka saki juna suna mayar da numfashi ya shafa fuskarta yace “so sweet babe" murmushi tayi masa a rayuwarta batason fada balle mara dalili irin nasa hakanan dai babu wata walwala suka yini Abu qalilan ya rufeta da fada hatta Hajiya Innah data shigo duba lfyrta Saida ta fahimci akwai  matsala Amma bata zurfafa ba dake dama tasan fadan halinsa ne, da dare suna zaune duk ta takura saboda Motsin kirki idan tayi rufeta zaiyi da fada wajen Tara na dare wayarsa tayi ring ya wani zabura ya miqe ya Kara wayar a kunnensa bataji me akace ba taji dai yace “to angama ganinan 20 minutes" miqewa yayi ya fice batare da ko ya kalleta ba taja ajiyar zuciya.

MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now