*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_23-24_*
____________________________
____________________________
Hayewa sama yayi yana yan waqoqinsa tabisa da idanunta daya kawo ruwa wai itace zata gabatar da tarihin amarya Kuma har yana iqirarin idan taqi zai qara sakinta zubewa tayi a gurin zuciyarta na hantsilowa tace “allah wannan wannan irin dan iskan mutunne" ta jima tana kuka kafin ta tashi gwiwa a salube ta shiga dakinta Hajiya Sahura ta Kira take fada Mata abinda yake faruwa ta danna Mata ashar tace “ke me kikace masa?" Shiru tayi tana tsiyayar hawaye tace “idan nace zanyi mgn Mom sakina zaiyi nikuma wlh bazan tashi a banza wata tazo taci bulus ba"
Shiru Hajiya tayi daga bisa taja ajiyar zuciya tace “Hakane Kinga bari na Kira uwarshi naji ko zata iya wani Abu" ajiye wayar tayi ta zauna tayi sukuti saida wajen awa daya ta wucce ta kirata tace “ki kwantar da hankalinki kije kiyi idan kin tashi ki zagesu tsaf dagashi har ita wannan shawarar uwarsa ce Kinga ko banza kin bata musu taro...." Katse Mom tayi da cewa “mom bakisan Ja'afar ba itama Barebari batasanshi ba wlh duk abinda ya furta baya masa wahalar aiwatarwa saura fa igiya biyu auren idan na kuskura nayi abinda kukace nasan biyun zai tsinke a bainan nasi"
Tsaki Mom tayi tace “to kiyi abinda ya dace nikam wannan tujararren mijin naki ya fara kaini qarshe wallahi idan na waiwayeshi saiya Raina kansa ace aure ko wata uku baayi ba tashin hankali ya cikashi daga wannan sai wannan kayy wannan Ja'afar din jarfa ne gsky Hajiya Fatsum ta haifo mugun iri irin tsiya irin jaraba" haka suka hadu sukayita zaginsa bata ankara da yana tsaye akanta ba Saida suka gama tana juyowa taganshi harde da hannu a qirji.
Saida taji qirjinta kamar zai tsage tsabar tashin hankali ya shafa gashin bakinsa ya juya ya ficeTsaki taja sosai yaji tsakin amma dake miskili ne bai juyaba ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta yanata juyi babu mataimaki takaici ya cikashi ya sake gyara kwanciya kawai yaja pillow ya rungume.
Amarya Rafi'ah kuwa tananan kullum cikin quncin zuciya take ta kasa karbar auren Ja'afar a qasan ranta kowa dai daya shafeta a salube yake hidimar bikin saboda damuwar da tayiwa amaryar tasu yawa duk wata kwalliya da akewa amare taqi yarda ayi Mata hatta lalle da wankin Kai qememe taqi duk wani daya Isa ya fada Mata taji ya fada tayi kunnen uwar shegu shikuwa Abba dama da aka fada masa cewa yayi a qyaleta kukanma kansa yakeyi babu meyi Mata maganin damuwarta sai Allan daya jarabceta, ranar ranar alhamis akayi kamu juma'ah takanas Hajiya Innah ta turo me kwalliya akan ayiwa amarya nanma tayi tsalle ta dire itafa bazaayi Mata ba dole haka aka qyaleta da yamma likis aka turo wasu arnan motoci domin daukarta wai Prince's day tana kuka tana komai Aunty Murja da Aunty Raziqa suka fito da ita cikin alqabbar da Saida akasha dambe sannan ta yarda ta saka suka sanyata cikin daya daga cikin motocin.
A cikin gidan Sarautar aka ware wani bangare aka kashe masa manyan nairori aka tsara gurin dinner tunda suka shigo sautin sarewi da algaitu ya cika Mata kunne suna busawa da bugun zuciyarta daqyar ta samu ta fara kamo addu'o'i tanayi wasu matane su hudu suka nufo matar da take suka bude suka fito da ita suka kamata anata yi musu ruwan kudade da turare itakam sai ruwan hawaye takeyi da shassheqa.
Wani bangare suka nufa da ita suka shiga Basu tsaya ba Saida sukakai qarshe suka qwanqwasa wani daki aka bude musu suka shiga Saida sukayi Mata guri a gefen gadon sannan suka russuna suka kwashi gaisuwa suka fice matsowa yayi gabanta ya jima yanajin sautin kukanta tanata shassheqa yanajin diran gunjin kukan nata har tsakiyar ruhinsa ya tsugunna a gabanta ya sanya hannu ya dage hular alqyabbar.
Babu kwalliya a fuskarta ga hawaye ya bata fuskar Amma bai hana asalin kyaunta fitowa ba, yaja ajiyar zuciya yana qara sauke injin idonsa akanta idanunta a lumshe suke sosai kukanta yake tabashi ya miqe ya zagaya dakin ya dawo fuskarsa a daure ya sanya hannu ya miqar da ita ya fara qoqarin zare Mata alqabbar ta riqe da sauri ya furzar da iska me zafi ya bude baki yace “ance rabonki da wanka tun shekaran jiya tunda bazaki iyaba ni zanyi Miki yanzu saboda banson qazanta"
Batasan sanda ta bude idanunta akansa ba yaci gaba da qoqarin cire mata rigar ta sake qanqame jikinta tana kuka tace “don....don Allah ja'....." Rufe Mata baki yayi ya dago kanta yace “ki roqeni wani abun Banda wannan tunda Ammi da Abba Basu Isa su saki kiyi ba ni na isa nayi miki"
Baijira cewarta ba ya faketa ya dagata cak tana kuka tana shure² yaqi sauketa Saida ya dangana da ita bathroom din dama ya shirya terming dinsa kawai ya tsomata cikin ruwan alqyabbar kawaiYa cire Mata nanfa suka Dora kokawa kowa naji da taurin kai takaici ne yasa baisan sanda ya keta riqar sabuwar atamfar sharratone din ba ta rintse idonta da qarfi jikinta na rawa ganin ta saki Masa tanata ajiyar zuciya yasashi kunce zanin ya zare Mata komai na jikinta pant da bra kawai yabar Mata ya fara wanketa tayi tayi ya qyaleta tayi yaqi.
Aikuwa ta Raina kanta ta dirzu miqewa yayi ya bare sabon towel ya miqa Mata fuskarsa kamar Bai taba dariya ba yace “ki tashi jiranmu akeyi ki fito banson sakarcin nan naki" yana fadin haka ya fice daga bathroom din yama fice daga bangaren gabadaya qarasa wankan tayi jikinta har yanzu rawa yakeyi tana jera masa Allah ya Isa dama Wanda ya fada mass batayi wanka ba, towel din ta dauro ta fito ta ishe wannan matar da taje yimata kwalliya taqi da wata me kamala a zaune a dakin tsoro ya cikata amma sai taga wannan kamilar ta matso ta kamo hannunta tace “na zaci can zaa kaiminke Ashe Baban Innah ya murda kambu to hakanma yayi Salamatu kiyi ki shiryata goma na dare zaa fara walimar naga yanzu har takwas kinsan Magaji ba hqr ya cika ba" zaunar da ita tayi Salamatu ta miqa Mata Mai ta fara shafawa har yanzu ta kasa tsayar da ruwan idonta bayan ta gama salamatu ta fara aikinta ana kwalliyar hawaye na gogewa daqyar Hajiya Innah ta rarrasheta tayi shiru akayi kwalliyar tabata wani arnen leshi tace tasa ta sanyashi yayi masifar yimata kyau kasancewarsa maroon daurin dankwalinta ma an dauki kusan 30 minutes sannan aka gama Hajiya Innah ta bata sabuwar alqabba milk da akayiwa ado da Marron tasa Mata takalmin alqabbar shima milk ne sai awarwaro na gold masu tsadar gaske dayan hannun Kuma agogo sai zobba da dankunne da sarqa habawa wannan rana ta musamman ce duk da bata cikin nutsuwar zuciya data kalli kanta a madubi Saida tayi hamdala tare da ajiyar zuciya.
Bude qofar sukaji anyi jakadiya ce tazo ta fadi gaban Fulani Innah tace “Allah ya qara Miki lfy Mai martaba Magaji ne yace ayi muku mgn taro fah yayi taro ku kadai ake jira" dago Rafi'ah tayi tace “mun gama yanzu zamu fito" turaruka ta fesa Mata ta Kama hannunta suka fito kicibis sukayi dashi a qofar shigowa bangaren ya kalli Rafi'ah ya kawar dakai yace da fulani Innah “sannu mun wahalar daku" murmushi tayi tace “nadai fada maka idan kun tashi yanda zakuyi" kallon Rafi'ah yayi yayi murmushi yace “natsani wannan kukan wlh ki daina babu abinda zai hana saima tunzurani da kikeyi"
Tsakaninsu da gurin zamansu babu nisa ya janyota jikinsa ya shaqi qamshin turarenta ya sauke ajiyar zuciya suka fara takawa a haka tanata qoqarin janyewa yaqi bata dama takan wani farin carpet sukabi wasu dogarai na takensu gaba da baya sunata kirari da ihu tuni sautin dake tashi a gurin ya canza akasa na gidan sarautar saida suka zauna sannan mutane suka rinqa tasowa suna zuwa suna kwasar gaisuwa suna zuba mawa amarya da ango kari Ni'imah na gda batasan wainar da ake toyawa ba.
Saida lkc yaja sosai ta samu labari aikuwa kishi da baqin ciki ya tunzurata ta dauko mota ta fito tana rayawa a ranta wato ita bata isaba shiyasa baiyi Prince's day a aurenta ba sai wannan auren cin amanar ya tarawa mutane, anacan anata shagali biki yayi biki taro yayi taro ango sai washe baki yake yana satar kallom Rafi'ah da tayi kicin² da fuska taketa jan zuciya shi hakanma nishadi yake bashi, batare da sunyi tsammani ba kawai saiji sukayi an wankesu da ruwan Sanyi qarara abinda yaja suka miqe gaba daya MC baisan me akeba yanata zuba babatu saiji yayi ance “ku dakata yaku taron tsinannanu Wanda kuka taru saboda auren tsinanne da tsinanniya to ku sani dukkanku kunyi kadan kuci mutunci na harni zaaci Amana a cuceni........
_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomanceMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...
