*_Mbh_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7*_53-54_*
_____________________________
_____________________________Shiru tayi batare da tace masa komai ba ya zuba Mata ido yana jiran tace Amma taqi cewa sai ya miqe yace “kiyi tunani akan manufata ta alkhairi ce gareki dani baki daya idan kin yanke hukunci zan kiraki sai naji ya ake ciki saboda nasan mataki na gaba" tabe baki tayi ta miqe itama yabita da kallon mamaki tunda yake baitaba ganin birkitacciyar mace irinta ba tama saurareshi din babu dama.
Qwafa yayi daidai lkcn da Alh Hisham ya shigo suka qara gaisawa yace “yadai ta amince kuwa?" Murmushi yayi yace “aa batama cemin komai ba inaga barinta zanyi ta nutsu tukunna saita yanke hukunci" numfashi Alh Hashim ya furzar yace “haka takewa kowa bazatace maka komai ba saidai kawai zan baka dama ka turo magabatanka ayi mgn inaganin hakan zaisa ta samu nutsuwa"Kallonsa yayi da sauri yace “da gaske?" Murmushi yayi yace “eh da gaske mana" hamdala yayi yace “Amma naji dadi sosai gobe kuwa zan tafi Azare zan sanar da Mai martaba abinda ke faruwa idan ya amince jibi ma zamuzo"
Jinjina Kai Alh Hashim yayi suka fita ya rakashi har gurin motarsa cike da kulawa inda yabar shirgin sha Tara ta arziqin daya hadowa mahir sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama ya tafi Alh Hashim yana komawa gida ya Kira rafi'ah balbaleta da fada yayi abinda Bai tabayi Mata ba yana tuhumarta dalilin wulaqanta Jamal.Hawaye ta rinqa sharewa tsayin lkc yana fadan nasa kafin ya sauko ya zauna yanayi Mata nasiha taci gaba da matsar hawayenta kamar tana daukar abinda yake cewa, Saida ya dakata sannan ta dago tace “bazanyi jayayya da abinda ka zartar ba Amma inason ki fahimceni wlh bansan komai game dani ba inaji a jikina Ni matar aurece Amma bana iya tuna komai so kuyi hqr ki qyaleni na rayu a haka har zuwa lkcn da Allah zai kawomin qarshen matsala ta tabbas akwai wani Abu da kullum zuciyata ke qoqarin tunawa ta kasa"
Shiru yayi na dogon lkc Itakam Allah yayi Mata baiwar saita kalami idan ya biyeta bazasu tsinanawa rayuwarta abin arziqi ba dubanta yayi yace “amma da sharadin zaki daina fita ko Ina don na gaji da mazan dakemin sinturi a gidana" saurin daga Kai tayi tace “na amince da hakan" dariya ma taso ta bashi saidai ya dake ya tashi ya shige ciki miqewa tayi ta shige ciki ta Kama danta suka kwanta ranar kwana tayi bata rintsaba ta takurawa kwanyarta son tuno abinda ya goge a cikinta hakan yake haifar Mata da matsanancin ciwon kai.Kwanaki suka rinqa tafiya cike da abubuwa masu rikitarwa duk yanda Jamal yaso ta bashi hadin Kai taqi yaje ya samu Mai martaba da maganar auren shine yace masa ya fara samun soyayyar yarinyar tukunna gashi abinda yake tunanin bamai wahala bane yayi masa wahalar samu, duk da bata bashi damar soyayya ba Amma tana sakin jiki dashi suyi hira.
Abinka da abinnan da hausawa suke cewa me da Wawa soyayyar da yake nunawa Mahir tasa takejinsa a jikinta idan yaga haka yakan dauka fara sonsa tayi Amma da yayi mgn sai tace itafa uban danta kawai takeso bayanshi bata ra'ayin kowanne namiji a duniyaWannan kalma na Sosa zuciyar Jamal saidai bashida wata madafa shi s hakanma dadi yakeji duk da ya zurma da yawa yakan taushi zuciyarsa akam ta sassauta Masa kar yaje yayi saukon bukukuwa ya Gina zuciyarsa da qaunarta Rana daya ta juyansa baya Da wannan tunanin yake ragewa kansa shauqi game da itaAl'amarin Ja'afar kuwa tunda Rafi'ah ta Bata ya shiga kwale²n masifa tun suna sakaran ji ko ganinta har suka fara fidda rai tsayin wata guda shikam yaqi lfy kullum cikin faduwar gaba da ciwon qirji yake, dadin dadawa Ni'imah da taketa qoqarin dole wai ita saita gogensa tunanin matarsa da dansa yakanyi Mata kashedi me qarfi game da hakan saidai taqiji wannan yasa suka rinqa samun sabani idan taje ta isheshi da mita wani lkcn idan takaici ya isheshi ya ware qwanji yayi Mata mugun duka ranar saidai ta kwana a bangaren Hajiya Fatsum.
Ana haka watarana ya zaneta cikin dare tazo ta isheshi aikuwa ba arziqi ta gudu bangaren Hajiya Fatsum tana kuka anan hajiyan take fada Mata tayi hqr bayin kansa bane aljani sukasa ya cire masa tunanin Rafi'ah sannan ya batar dashi shine suketa fada da zuciyarsa da aljanin idan ya ciks takurawa ma haukacewa zaiyi shima, suna tsaka da wannan tattaunawa kawai sukaga wani jan haske ya keto bango ya nufosu gadan gadan take suka watse suka rinqa tsere Amma Saida ya cimma Hajiya Fatsum kawai saiji sukayi ta fasa qara ta fadi qasa Tim tundaga wannan Rana ta zama kamar mutum mutumin babu motsi babu magana babu komai a wannan ranar ne Kuma bakin Rafi'ah ya bude,
YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomanceMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...