MY BESTIE'S HUSBAND

1.7K 80 4
                                    

*_My Bestie's Husband_*


*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_35-36_*

_Maganin sanyi! maganin sanyi!!_

_Mata sai _fa kun tashi tsaye wlh duk maganin matan da zaki sha idan har da sanyi ajikin to  bazai taba_ _miki aiki ba saboda sanyi  yanzu ya adabi kowa ba yara ba manya  ba_ _zawarawa ba yammata ba mazan ba matan kowa yiyake Dan haka Yar uwa  kizo ga magani_ _nazo miki dashi me kyau sadidan ba karya, Koda yake Ni bazance Miki komai ba saikin gwada  zaki bawa wasu labari._
_Yana maganin sanyi mai_ _sa kaikayin gaba da kuraje dadewar gaba daukewar niima karancin shaawa kaikayayin jiki ciwon jiki da ciwan Mara yawan Ciwan kai idan sanyi ya busa maza Yar uwa ki hanzarta kine mi_
_naki_
_Muna aikawa ko wani gari a kano kuma kowace unguwa Dan Allah idan kinsan baki shirya ba karki mun magana mubatawa juna lokaci._
_Serious buyers siyan daya ko sari ki shiga nan Domin qarin bayani_

_____________________________
_____________________________


Numfashi yaja yace “shikenan Dad Babu komai Amma aja Mata kunne abubuwa da yawa Ina hqr dasune dominka kada takai hqr na qarshe" godiya Dad yayi masa suka aje wayar ya zubawa Rafi'ah ido tayi luf da ita ta lafe a katifar yanayinta ya kalla kawai ya fahimci da abinda yake damunta Amma dake miskili ne saiya shige bathroom ya fada wanka sanda ya fito tayi bacci,
Shima kwanciyar yayi yanajin yanda dumin jikinta yake hauhawa da hakadai shima bacci ya daukeshi washegari taso zuwa school ya fitittike ya rinqa ruwan bala'i waishi yayi aure Amma bazai samu lkcn matarsa ba da anyi mgn sai tace school, dole tanaji tana gani ta hqr aikuwa ranar tasan ta zauna a gda duk wata nutsuwarta Saida ya rabata da ita ko bakin qofar dakin yaqi zuwa wannan Abu ya dameta hakadai taketa daurewa har yammaci yayi wanka ya fice itakuma ta gyara bangaren ta sake kwanciya.

Yinin ranar sur bataji Motsin Ni'imah ba to dayake itama taji maza batako leqoba har dare yayi da daren ne ya shigo da murnarsa ya zauna a parlour yana shafa fuskarta ta bude idonta akansa yayi murmushi yace “ina fatan kin gama ready na tafiyarmu jibi zamu tashi" lumshe idonta tayi kawai batare da tace masa qala ba lamarin daya bashi mamaki yasan dai ba wani Abu ya fada Mata da zai dameta ba farin ciki ma ya kamata tayi.
Juyowar da zaiyi yaga hawaye yana zuba a idanun nata dagota yayi da matsanancin mamaki yace “mene Kuma ya faru daga mgn?" Hawayen ne ya qara qarfi tace “amma dai nazaci kasan cewa Ina karatu Kuma kanada lbrn burina akan karatuna meyesa ka dage saika tafi dani bayan bani kadaice matarka ba meyesa bazaka dauki Ni'imah ba tunda ita free take Ni ka qyaleni na qarasa karatuna kace 3 mouths kafin three months munyi exams mun gama don Allah ka qyaleni badon...."

Abinka dame zuciya a kusa sosai ranshi ya baci Amma Bai nuna Mata ba ya miqe ya haye sama tabisa da kallo jin shirun tayi yawa bai dawo ba itama ta miqe ta nufi saman ta bude dakinsa ta hangesa kwance kan gado matsawa tayi ta zauna kusa dashi ya zubawa selling ido Kama Hannunsa tayi ya janye ta bude baki a hankali tace “bansan bazaka fahimceni ba da ban fara fada makaba kayi hqr...."
Daganta hannu yayi yace “fita Rafi'ah" da sauri ta dago ya tashi zaune yace “ki ficemin a daki nace" miqewa tayi a tsorace ta fice daga dakin da sauri ya furzar da iska me zafi ya tashi ya kulle dakinsa  nata dakin ta shiga ta fada gado tayi kwanciyarta zuciyarta na tafasa ta tsani mutum mara fahimta a rayuwarta, da wannan tunanin ta tashi kawai ta dauka qur'ani ta fara karatu ta Jima tana karatunta sannan ta bari ta koma ta kwanta aikuwa bacci ya dauketa me dadi hankalinta kwance bata farka ba sai asuba tayi sallarta ta fito parlourn ta fara shirya breakfast tana kitchen din taji saukowarsa ta fito ya zubanta ido harta qaraso kusa dashi ta durqusa tace masa “barka da fitowa" wani gwauron numfashi ya sauke komai na me ilimi dabanne da oo ce sai suyi sati suna gaba da juna Dagota yayi ya hadata da jikinsa yace “na fahimcek...." Rufe masa bakinsa tayi tace “na hqr da karatun kayi duk yanda kakeso dani" wani dadine hade da tausayinta ya mamayeshi  ya qara matseta da jikinsa yace “are you sure?" Dagansa Kai tayi yayi murmushi me sauti ya sauke lips dinsa a goshinta yace “Allah yayi miki albarka zuciyata tafi aminta dana tafi dakene saboda inads tabbacin zamu qara samun kusanci da fahimtar juna bazan katse Miki karatunki ba jiya na gama Miki komai insha Allahu wannan daya dai bazai hanaki samun abinda kika Dade kina muradi ba sai kinzama doctor din da zaayi alfahari da ita a fadin Nigeria ki shirya yau zamu wucce Abuja gobe saimu tafi kinji amaryata?"


MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now