MY BESTIE'S HUSBAND

1.3K 89 11
                                    

*_Mbh_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7


*_51-52_*

_____________________________
_____________________________


Jinjina Kai Hajiya Rakiya tayi ta dubi Rafi'ah ta miqe ta Isa gabanta lkcn ta idar da sallah ta zauna kusa da ita ta Kama hannunta kuka takeyi sosai, cikin yanayi na tausayi Hajiya Rakiya tace "kiyi hqr kinji yata Allah yasan komai Kuma shine yakeda maganin komai" kwantar da kanta tayi a kafadarta ta sake rushewa da kuka cikin yanayin da batasan ya akayi ya wanzu ba ta bude bakinta da cikin watanni hudun baya iya furta komai tace.
"Wlh banida wata alaqa da Hisham a baya ne ma yakemin Kama da uban Dana Ja'afar amma yanzun ya daina...." Miqewa Hisham da bari'ah sukayi tare suka Isa gabanta yakai hannu zai tabata sai ya tuna da mgnrta uban danta Ja'afar tuni ya dawo nutsuwarsa yaja fasali yace "dama bakinki Yana mgn kikaqi yimin mgn tsayin wata hudu?" Cikin kuka tace "aa yaune naji Ina iya furta wasu kalmomin sannan inajin kamar inason tuno wani abu game Dani Amma na kasa don Allah wacece ni ya akayi nazo nan Kuma inane nan?"


Hawayen tausayinta Alh Hashim ya goge ya fice daga dakin saboda zuciyar Mata ke gareshi abin kuka bayayi Masa wuya Kuma yin kukansa zai qara karya mawa Rafi'ah zuciya, zama yayi yana tunanin abubuwa da yawa da bashu da amsarsu bai ankara ba yaji Bari'ah nayiwa Hajiya Rakiya magiya akan kada ta tafi da Rafi'ah tayi alqawarin kulawa da ita tare da dauke Mata kewa taci alwashin taya mijinta ida wannan kyakkyawan aiki da yayi niyyar aiwatarwa.
Daqyar Hajiya Rakiya ta yarda tabar Rafi'ah a gidan tun daga wannan ranar zaman Bari'ah da Rafi'ah ya koma gwanin sha'awa komai tare sukeyi Bari'ah macece me surutu amma tanada hqr da Kuma sanyin hali wannan abin ya dawwamar da qauna tsakaninsu, yauma kamar ko yaushe suna parlourn sunata hirarsu Bari'ah tanayiwa Rafi'ah koken matsalarsu ta dubeta tace "akwai wani magani da wani Malamin mu ya sanar damu idan akayi amfani dashi indai da rabo zaa dace ki bani bero da takarda zan rubuta Miki mu fita pharmacy mu nemeshi insha Allahu idan kikayi amfani dashi Allah zai dubemu ya bamu babie"


Murna ce ta cika Bari'ah ta tashi ta dauko biro da paper Rafi'ah tayi rubuce rubucenta da rubutunta na likitawa mamaki ya cika Bari'ah ta dubeta tace "dama kinyi karatu ne Rafi'ah?" Murmushi tayi tace "jiya na tuna cewa Ina da medicine certificate a garinmu Amma na kasa tuna a makarantar da nayi karatu Ina takurawa zuciyata akan tuno wani Abu game dani nakasa kawai abinda brain dina take fadamin ni matar aure ce Kuma ni ba matar qaramin mutum bace"
Shiru Bari'ah tayi tana nazarin kalamanta kafin ta miqe tace "idan ance asiri akayi Miki aka haukataki aka baroki da garinku da Mijinki sai kice aa ke ba asiri bane Mijinki ya mutu Kuma a kalamanki kina bayyana ke matar aure ce na rasa wanne zamu dauka a ciki to Allah dai muke fadawa Kuma munsan zai amsa bari na Kira Yallabai idan yana kusa sai yazo yakaimu


Shigewa dakinta tayi ta canza kayanta zuwa doguwar riga tayi rolling mayafin ta fito lkcn da Alh Hisham yake shigowa ya dubeta ta rusuna tace "barka da dawowa" murmushi yayi yace "kun dawo dani ku dole da kukeso to Wai inama kuka samo sunan maganin?" Sunkuyar dakai tayi Bari'ah tace "gulma itane ta rubutamin...." Kallonta yayi da sauri yace "ina kika samoshi?"
Qasa ta sakeyi da kanta tace "akwai wani lecturer dinmu da yake yawan yimana bayani akan abinda ya shafi matsalar haihuwa dayake a bangaren daya shafi matsalolin Mata nayi degree na..." Shiru tayi Alh Hashim yana qare Mata kallo yasan daganan bazata iya sake tuna komai ba shi tausayi na sosai take bashi musamman idan tace Ja'afar dinta ya mutu. Ficewa sukayi kowa jikinsa Babu qwari suka inda suke sakaran zasu samu Basu samu ba sukayi Shiru a mota na tsayin lkc kafin yatada motar yace "na tuna a titin government house naga an bude wani sabon katafaren Pharmacy R&J naji ance na wani babban doctor ne Kuma kamar ance dan Bauchi ne akwai yuwuwar zaa samu acan"
Nufar Pharmacy din sukayi sukabar Rafi'ah a cikin mota Bari'ah na riqe da Mahir a hannunta yaron kyakkyawa dashi Masha Allah fari tass kamar ubansa ta ratsa jininsa ta fito yanda duk Wanda yasan ubansa yana ganinsa zai iya shaida hakan, suna shiga pharmacy din suka miqa takardar da aka rubuta maganin wani matashin saurayi da alamun shine mamallakin gurin ya karba ya dago ya sauke idonsa akan Mahir gabansa ya yanke ya fadi.


MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now