*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad- realfauzahtasiu_*
*_Gmail-fauzahtasiu41@gmail.com_*
*_YouTube- Open eyes multimedia_*
*_Telegram_*
👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7*_31-32_*
_____________________________
_____________________________Batace masa qala ba Amma ta qudurce a ranta ko wuta yake fesarwa qarshen bala'i bazata bisa yayi Mata uku babu ba da wannan ta janye ta shiga bathroom ta tsarkake jikinta ta fito ta iskeshi yayi bacci ta zubawa fuskarsa ido da gaske kyakkyawa ne kamar yanda Ni'imah tasha fada Mata Amma bata taba ganin kyansa ba sai yau ajiyar zuciya taja ta haye gadon zata kwanta ya janyota jikinsa yace “kin gama kallon nawa?" Kunyace ta kamata tayi luf a jikinsa da haka bacci ya kwasheta Basu suka farka ba sai asuba shine ya fara tashi ya tsarkake jikinsa yayi alwala ya dawo itama tayi sukayi sallar ya koma ya kwanta ita Kuma ta shiga kitchen tana hada musu abin karyawa bayan ta gama da qarfin hali da komai tayi wanka tayi kwalliyarta sosai yau jin kwalliyar takeyi musamman badan kanta ba sai domin kalaman Ni'imah da suka kwana suna yawa a kwanyarta Wai snatcher itace snatcher, bayan Allah shaidane tayi duk me yuwuwa taga ta gocewa wannan qaddarar hakan ya kasa samuwa ta qudurce a ranta tunda har ta yarda ita snatcher ce to zatayi duk me yuwuwa ta boye Mata baraka tsakaninta da mijinta bazata yarda Koda wasa ta fahimci akwai rashin jituwa tsakaninta da Ja'afar ba, da kanta ta tambayi kanta Ashe da gaske ne abinda Ni'imah ta dade ta fada mata ita Koda uwarta zata iya raba gari akan mijinta,
Murmushi tayi ta matsa inda yake kwance tabbas yakamata ta nutsu aikine ja a gabanta da gaske batajin Ja'afar a ranta shafa fuskarsa ta rinqayi da hannunta cikin baccinsa me hade da mafarkai masu dadi yaji qamshinta ya cika hancinsa ga wani dumi da yakeji a tsakiyar hannunta ya saki ajiyar zuciya tare da bude idonsa ya saukeshi akanta, mamakine yasashi sakin baki ta sunkuyar dakai tana murmushi tace “jiya naji kana waya kana cewa zaka hadu da wani a fada 9:00am Kuma naga takwas harta wucce Ina fatan tashin da nayi maka banyi laifi ba?"Zuba Mata ido yayi kamar me nazarin wani Abu sai yaga ta zame qasa cikin sanyin jiki tace “kayi hqr idan hakan ya bata maka rai bazan qar....." Rufe Mata baki yayi tare da miqewa ya miqar da ita yayi hug nata tare da dora kansa saman nata yaja fasali yace “koma kin batamin na yafe Miki muje ki shiryani ki bani abinci" zaro ido tayi yayi dariya shima murmushi yayi yace “matsoraciya ba komai zanyi Miki ba"
Noqe kafada tayi tace “aa kaje ka shirya bari na qarasa hada break din bata jira cewarsa ba ta fice da sauri yayi ajiyar zuciya ya fice ya shiga nasa dakin ya jima kafin ya fito ya isheta a parlourn tana fesa room freshness zama yayi a dinning yace “abar aikin nan azo ayi Break" ajiye gongonin tayi tazo ta zauna ta hada masa ta miqa masa itama ta hada nata sunacin abincin Amma idonsa na kanta yana yabawa da baiwar da ilahi yayi Mata ta kowanne bangare tabbas itadin macece da yake fatan alfahari da ita,Miqewa yayi yace “alhmdllh kitchen ya karbeki fatan nasara saina dawo" fatan alkhairi tayi masa ya fice ya shiga bangaren Ni'imah da alamu ma batama tashi ba parlourn duk abin Apple da lemo yayi qwafa ya nufi saman ya shiga tana kwance a gado tayi daidai abinda sai baccinta takeyi bathroom ya shiga ya ganshi a bushe ya dawo ya qure Mata A.C tare da kure gudun fanka yaja ya tsaya shi kansa sanyin ya damesa.
Murmushi yayi yanda yaga tana neman duvet din daya janye hakan yasata miqewa ganinsa a tsaye yasata jin wani dam yaja numfashi yace “baki sallah ne 8:40 baki tashi ba" harararsa tayi tace tunda Kai ka tashi dai ai shikenan Ina ruwanka da sallah ta" bai damu da abinda tace ba ya matsa jikin gadon yace “ki tashi kiyi sallah ki Kuma sabarwa kanki tashin asuba nagaji da fada Miki zan fara daukar mataki akanki shari'a tace yaroma idan yakai shekara bakwai yana qin yin sallah a dakeshi Kinga kuwa kema zaki iya shiga sahun"
Ta bude baki zatayi mgn ya dora Mata hannu a bakinta yace “bakinki ma wari yakeyi bakiyi brush ba kije ki gyara kanki idan kinason na saurareki inason mace me tsafta Rafi'ah kafin na tashi ma ta gama komai na gidanta yanzu dana fito in mutuwa zatayi da dawo ma saitayi tanada lkc kafin na dawo Amma ke bakida aiki sai bacci da hauka"

YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomanceMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...