*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_15-16_*
_Ina qara jaddada muku kada wata ta bini pc tacemin please to beginning wlh bazan tura maki ba ki tambaya a duk groups din da kikaganshi My Bestie's Husband is Free book_
_____________________________
_____________________________
An dade sosai kafin Rafi'ah ta saki jikinta taci gaba da rayuwa kamar kowa kyawunta da nutsuwarta yasa take samun masoya ta ko Ina ita Kuma tayi kicin² ta sanya shuni da tabo ta liqe idonta taqi kallon kowa taqi sauraron kowa dake autace babu wanda ya matsa Mata duk da abin yana damun Abba sosai ga aminiyarta da samarinta tana sauraro Amma ita ko samarin Ni'imah bata kulawa duk wanda yazo saidai tace ta gaisheshi qarshe ta dage aka sama Mata admission a ATBU ta fara karatun medicine itakuwa Ni'imah daqyar saboda Rafi'ah ta yarda ta fara diploma a mass communication shima don ta rasa tsayayyen saurayine ne yawancinsu yan Shan minti ne sai suzo su lallabeta su matseta su tafi Saida sukayi kaca² da Rafi'ah akan hakan sannan ta hqr ta daina kulasu suka duqufa karatunsu.
Dayake taga bacin ran Bestie dinta abinda bata taba ganiba tsahon rayuwarsu yasa ta shiga taitayinta ta mayar da hankali a karatunta ashe dama tanada qwaqwalwar iskanci ke hanata karatun da gatan taga idan bata iyaba Rafi'ah zata koya mata yanzu Rafi'ah bata zama Kullum saitaje cikin garin Bauchi daga Azare ta dawo sai kadaici ya fara damunta ta zauna tayi zugum tana tunanin wataran fah rabuwa zasuyi kowacce ta tafi gidan mijjnta, haka sukaci shekara daya sukaci biyu Ni'imah ta gama diploma dinta tayi saa kuwa ta samu point me kyau.
A lkcn ne karatun Rafi'ah ya fara zafi hakance tasata yanke shawarar komawa cikin makaranta da zama saboda tana cinye lkcnta a go and come sannan ga surutun Ni'imah ya fara isarta Kullum mgnrta aure aure shiyasa tasa Abba ya Kama Mata hayar hostel ya zuba Mata komai da komai ta koma can da zama amma duk weekend tana dawowa gida idan har ba lkcn exams bane babban abinda yake damunta shine yawan mugun mafarkin da takeyi da Bestienta da wani mutum da bata ganin fuskarsa kullum mafarkin baya zuwa Mata da siffar alkhairi da farko takan dauka shirmene na mafarki amma da abin ya ta'azzara saitake fadawa Abba.
Shine yake cewa da ita mafarkin shirme baa riqeshi gabadaya dole ya kasance an manta wani bangare nasa ko an mantashi gabadaya yakance Mata ta dage da addu'a Allah ya rangwanta qaddararsu tabbas mafarkin da abinda yake nuna Mata zuwanshi dama akan samu haka indai mutum ya kasance me taqawa da miqa lamura ga Ubangiji to allah a yanayiwa wasu ludufi na nuna musu abubuwan da zasu faru gaba a mafarki domin su roqeshi sauqi da rangwame"
Wannan dalilin yasa ta qara matsa qaimi wajen roqon Allah sauqi rahma da taimako cikin kowacce qaddara me kyau ko akasinta, suna tsaka da kakar exams ne lkcn tana level 300 Ni'imah ta kirata da murna suka gaisa tace.
“Albishirinki Bestie" amsawa tayi da zaquwa tayi dariya sosai tace “nakusa zama amarya shekaran jiya Sarki Muhammad Wakil ya kawowa Dad ziyara shine yaganni bayan ya tafi ya Kira Dad yake cemasa, idan baiyimin mijiba yanaso ya bawa danshi Prince Ja'afar Wakil aurena wai shekarunsa sunyi nauyi 36 amma bayada niyyar fitar da Mata duk angama nuna nasa yammatan dangi yace basuyi masa ba ance ya kawo sama da shekara yaqi cewa komai har yayan abokai sarakai duk ya kaishi ya gani duk yace basuyi daidai da text dinsa ba"
Numfashi Rafi'ah ta sauke cikin murna tace “Alhmdllh ranar da muka dade muna jira tazo amma kedin kinyi masa?" Murmushi tayi tace “to ganinan dai yazo jiya dake yana gari yazo weekend Amma ko 5 minutes baiyi ba ya tafi Kuma bayan gaisuwa ko kalma daya Bata shiga tsakaninmu ba Saida zai tafi yabani hundred k wai nasa Kati ke kinganshi kuwa hadadden guy dan gayu ga DATA a hannunsa motar da yazo da itama jiya naga ansa tallanta a JAA LIFESTYLES 60 millions Kinga kuwa ai zan fantama ko?"
Rafi'ah bata fiye dariya ba saidai murmushi amma kalaman qawar tata Saida suka bata dariya tace “kullum burinki a kudi ya qare kamar wacce kika tashi da haushin talauci meyesa ne Ni'imah ki bari don Allah kudi basuda wani muhimmanci a aure soyayya tafi komai indai da rufin asirin ci dasha da sutura da gurin zama majority's na Mata tunanin kudi sune jin dadi shine ke wahalar damu bance kudi ba abinso bane aa nima inasonsu Amma banaso su zama abin duba a mizanin auratayya ki auri mutum domin Allah da Kuma cancanta Bestie Kuma kada ki auri namijin da baya sonki ki auri wanda yakesonki idan kinji kinason dole saikin aureshi to kiyi qoqarin koya masa sonki tanyar kwadaita masa kyawawan halayenki qwaqwalwar namiji tanada fadi Amma zuciyarsa jaririya ce an halicceta dason me rarrashinsa da faranta masa yanason tarairaya da tattali uwa uba hqr domin soyayya da rayuwar aure tafi komai buqatar hqr Bestie Ina tayaki murna da samun irin mijin da kikeso Allah ya daidaita yasa kizama tauraruwa a zuciyarsa Kuma ya baki ikon kula dashi"
Numfashi ta sauke tace “amin sarki wa'azi idan sweet yazo zan bashi lbrnki da nasiharki gareni ke har record nayi fah zan kunna masa" murmushi Rafi'ah tayi tace “bakya girma bakya rabo da shirme ki gaisarmin da angonmu bazan dawo ba saina gama exams" sallama sukayi suka aje waya Rafi'ah tanajin farin ciki Bestienta zatayi aure Amma idan ta tuna rabuwa zasuyi sai taji hawaye ya wanke Mata fuska washegari Ni'imah ta kirata ta fada Mata mgn fah ta girma har ansa lkcn biki wata daya Amma angon yabar qasar bazai dawo ba sai ana saura sati daya biki.
YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomantizmMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...
