EXQUISITE WRITER'S FORUM(EWF)
LUBABATU
01
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabirMARUBUCIYAR:-
Rayuwar Suhailat
D'an Amana
Kad'aici
So ne Sanadi
'Yar Shugaba
Mai Hakuri
Karshen Makirci
So Sartse
Da iyayena
Kaddararren Al'amari
Akan Idona
Hantsi.*SADAUKARWA ga SAFIYYA HARUNA (Mrsjmoon). Mace me kirki, bazan manta da halarcinki ba, me fadan Alkhairi, kina da matukar kima a gareni domin a duniyar marubutan online kin shayar dani mutunci, yarda, aminci, gaskiya. Allah ya cigaba da faranta miki ya kara miki fikra ya raya mana Noor ya albarci rayuwarsa.*
*Bazan manta da karamcinki ba KHADIJA CANDY, Na aminta da kirkin ki da amana, ba ki da kyashi, mai son ganin cigaban mutum. Allah ya cigaba da faranta miki ya kara kaifin basira ya baki zuri'a nagari masu albarka.*
_Ban yarda a sauya min labari ta ko wani irin fuska ba, dan haka a kiyaye_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*YOLA*
Lubabatu kwance take tana karatun wasikar jaki wanda ta kwashe awa guda a wannan yanayi, ta rasa meke yi mata dadi saboda duk gabobinta tsananin ciwo suke yi mata, zuciyarta tana cike da kunci da radadi in ta tuno da zantukan yayarta Jidda. Wayarta ce ta soma ruri alamar kira ya shigo hakan shine ya katse mata tunani, cikin azama ta dauka taga sunan Mijin Anty jidda akan wayar, gabanta ne ya yi mummunar faduwa sakamakon wani al'amari daya fado mata a rai, wadda take zargin kiran da Haruna ya yi mata baya rasa nasaba da jin sakon mutuwar Jidda. Hawaye ne ya wanke mata kunci tun kafin taji sakonsa domin jikinta ya gama bata cewar zai sanar da ita mummunar labari. Kiran yana gab da tsinkewa ta dauka ta kara a kunne tare da yin sallama cikin sanyin muryata da yake nuna tsantsar damuwa, ya amsa sannan suka gaisa ya daura da cewa.
"Lubabatu sai dai muyi hakuri domin Allah ya yiwa Jidda Rasuwa dazun nan wajen haihuwa, yanzu haka an kammala yi mata sutura zamu kaita makwancinta".
Ya kare maganar cikin kuka da sassheka, bata iya furta masa komai ba ta janye wayar a kunne ba tare data kashe ba, numfashinta ne ya fara barazarar barin jikinta, zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri tamkar zata faso kirjinta ta fado kasa.
'Innalillahi wa inna ilaihir rajiun'
Shi ne abin da kwakwalwarta ta tuno mata ta soma ambata a hankali, hakan shi ne yayi sanadiyar dawowar ta cikin hankalinta.
"Shikenan Anty Jidda, Allah ya jikanki ya yi miki kyakkyawar sakamako"
Hawaye ne masu zafi suka shiga bin kuncinta, nan take ta soma tuna awa biyar da suka shude lokacin da take waya da Anty jidda take ce mata.
"Lubabatu kaicona dana bi son zuciyata, na yi dana sanin auren Haruna"
"Anty ban fahimce ki ba, me yake faruwa? Ko jikin naki ne? ki min bayani kin hautsina min tunanina"
Bata iya bata amsa ba sai ta rushe da matsanancin kuka harda kunji, Lubabatu ta shiga bata hakuri da lallashi da kyar tayi shuru ta cigaba da yi mata bayani.
---"Ke Lubabatu tunanin me kike yi haka ina ta kwala miki kira daga tsakar gida shuru ba amsa"
Umma ce ta katse mata tunaninta, cikin sasshekar kuka ta mike tare da isa gabanta ta kama hannunta ram duka biyun, ganin ta a haka yasa Umma ta kara firgita.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...