02

106 12 1
                                    

LUBABATU

02

Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir

EWF.


Baba dama ina so Lubabatu ta zama makofin Jidda ce in ba alkawarin wani akanta.

Yayi maganar cikin jan fasali da sunne kai a kasa tsabar biyayya.

Au to to wannan tunani naka yayi matukar kyau, Kuma koda akwai maganar wani ai dole a jiye shi gefe a dauki naka tunda kai mun sanka kuma ka cancanci a baka. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kasan dai Lubabatu tana dauke da lalura zaka iya da ita kuwa?

Baba nasan da haka, domin in baka manta ba nine nayi silar da aka gano abinda ke damunta, dan haka aurenta kamar jahadi ne, sai dai zan so kafin a yanke maganar a ji ta bakin Lubabatun

Rabu da ita in dai mu mun yarda bata isa tace a'a ba, domin a musulunce ni keda hakkin zaba mata miji kuma kai kayi min tunda tuwo na mai na za ayi, sannan kusan taimaka mata zaka yi saboda lalurar da take fama da ita.

To shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairinsa.

Ameen, Ina ga kafin ka tafi za a tsaida kwanakin biki kawai tunda abu na gida ne, sadaki ka bayar ko nawa ne Albarka kawai muke bukata.

Nagode Allah ya saka da Alkhairi

Baba ya amsa da amin tare da sanya masa albarka. Haka Haruna ya sauke masa yan dubu dubu bandir uku ya kama dubu dari uku kenan.

Ga wannan dubu dari na sadakin, sauran kuma ayi hidimar biki dasu.

Yauwa Allah ya yi Albarka. Na tsaida bikin ranar sadakar arba'in din Jidda, ana gamawa sai a daura aure, insha Allah zan sanar da yan uwa kaima sai kayi kokari ka sanar da manyanka. Sannan batun kayan dakin Jidda ka barsu kawai a matsayin na Lubabatu sauran abinda ya dace ka saida sai ka kawo mana kudin.

To insha Allah ba damuwa Allah ya kara girma. Ni zan tafi sai ana gobe addu'ar arba'in din Zan zo.

Masha Allah Allah ya yi maka Albarka ya tsare hanya.

Haruna ya amsa da Amin yana godiya, har waje Baba ya rakashi ya hau a taxi ya wuce da shi filin jirgi zuwa kaduna.

Baba ya shiga gida cike da fara'a fuskarsa, Umma dake zaune bisa tabarma a baranda ta bishi da kallon mamaki harya zauna kusa da ita ta ce cikin zakuwa.

Malam rabon da in ganka a irin wannan yanayin tun kafin rasuwar Jidda, lafiya kake ta fara'a haka kamar anyi maka kyautar hajji.

Baba ya dire mata kudi a gabanta.

Amina Allah ya kawo min karshen wahalata, wannan kudin da kika gani na auren Lubabatu ne.

Ban gane ba, me kake nufi? Mu da muke cikin alhinin rashin Jidda me zai kawo maganar auren Lubabatu kuma?

Haruna dai shine mijin domin ya bukaci da a bashi aurenta.

Haba Malam ni kam ina ganin a bar wannan maganar, dan bai kamata a tauyeta ba.

Wlh karki sake ki kawo min gargada a wannan auren, ko kin manta ita Lubabatun matsala ce ke gareta, ba tada wani mashinshini daya ce yana sonta saboda lalurar ta, ina ganin ai Huruna kamar taimakonmu zai yi dan haka in ba zaki fadi alkhairi akan wannan maganar ba to gwara kiyi shuru kawai.

Hmmm shikenan Allah ya zaba abinda yake Alkhairi.

Yama zaba insha Allah, daga ni har ke saukinmu ne yazo wahalarmu ya kare. Tashi ki kiramin ita na sanar mata.

LUBABATUWhere stories live. Discover now