06

81 7 3
                                    

LUBABATU

06

Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir


Bayan sun isa airport ba bata lokaci jirginsu ya sauka aka gama duk wani bincike da akewa kayan matafiya kana Hydar ya fito ya kira numbern Umar sai ya hango shi ya daga wayar yana helo, da haka ya gane shi ne sai ya karasa gunsu, suka gaishe shi cikin mutuntawa cike da fara'a, Umar ya sanya trolley a bayan mota kana duk suka shiga ciki, Ubaidu ke tuki Umar yana gefensa sai Rahima a baya tare da Uncle Hydar, haka suka kamo hanya suna hira cikin nishadi.

Lokacin da suka isa gida motarsu tayi parking duk suka fito, mai gadi ya rugo da gudu ya kwashi gaisuwa kana ya isa bayan boot da nufin ya dauki trolley, Umar ya dakatar da shi yayi masa nuni daya wuce, shine ya dauki jakar suka kama hanyar falo su duka. Ummi dake cike da zumudi ta mike da sauri dan ta riskesu a tsakar gida saboda ta gaza hakurin su shigo.

Alhaji sun iso fa, bari naje.

Haba Hajiya wannan irin sauri haka? Ki bari su karaso ciki mana.

Abba ya katseta da sauri, sai ta koma ta zauna badan taso ba amma saboda makirci sam fuskarta bai nuna bacin rai ba sai ma washe baki da ta yi tana cewa.

Wlh zumudi ke fizgata, kasan jini ba wasa ba, na kosa naga d'an uwana.

Kafin ya bata amsa sun shigo falon da sallama. Ummi ta mike da sauri fuskarta fal farin ciki sai washe baki take tana zubawa Hydar sannu da zuwa, shima murmushi kawai yake mayar mata annurin fuskarsa ya bayyana sosai, har suka zauna gaba daya, nan suka kwashi gaisuwa ya gaishe da Abba cikin tsantsar mutuntawa da nuna farin cikin ganinsa, hakan yasa Abba yaji kaunarsa a ransa ya saki masa fuska sosai, haka ya gaisa da Ummi cikin nuna kulawa, suna cikin wannan yanayi sai ga Mami ta fito falon fuskarta wasai kamar dazun basu bata mata rai ba, ta zauna kusa da Ummi tana cewa.

Lale da bak'onmu mutanen turai, da fatan ka sauka lafiya ya hanya?

Lafiya lau Hajiya, na sameku lafiya?

Allhamdulillah duk kalau, ai mun ji dadin zuwanka domin zamu huta da maganar da Hajiya take akan zancenka

Hydar ya sunne kai yana murmushi bai ce komai ba, Ummi taja guntun tsaki ta mike tana cewa.

Hydar muje na nuna maka masaukinka kayi wanka sai kazo ka karya, abinci na jiranka. 

Ok yace sai ya mike, Rahima ta dauki jakarsa zata bisu Ummi ta amshe.

Bani nan, yau ku barni na sada zumunci, da kaina zan bawa dan uwana kulawa ta musamman, domin jini yafi ruwa kauri.

Sai duk suka sanya dariya Abba yace cikin zolaya.

Auta samu guri ki zauna yau ummanki idonta a rufe yake, kaunar zumunci ne ya motsa, iyeka namu ido.

Sai duk suka sanya dariya suka mayar da abin ba'a, Abba ya mike shima ya wuce sashinsa yabar su Rahima zaune, Ubaidu shima ya mike zuwa wajen matarsa, su Mami suka cigaba da hira tare da kallon tv. Ummi suna isa dakin data baiwa Hydar bangaren sashin da dakin Umar yake, ta ajiye trolley a gefe ta isa inda yake a tsaye gefen gado yana kokarin cire rigarsa ta rungume shi ta baya tare da sauke gauron numfashi.

Nayi tsantsar kewarka sosai Hydar, hop zamanka a gidan nan zaka sanya ni farin ciki.

Nima nayi kewarki fiye da tsammaninki, shiyasa na kasa hakuri nazo gareki, sai dai nazo na iske gidanki cike yake da al'umma hop ba zasu bani matsala ba.

Karka ji komai ka saki jikinka tamkar gidanka, domin nice ke da ikon komai a gidan nan babu wanda ya isa yaja dani.

Naji dadin jin haka yanzu hadamin ruwa na watsa.

LUBABATUWhere stories live. Discover now