LUBABATU
07
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabirEWF.
Kaduna
Bayan mako guda
Da safe misalin karfe tara duk sun hadu a dinning da yake ranar lahadi ne suna gida, Ummi da sun hada Ido da Hydar sai ta sakar masa murmushi shima ya mayar mata, babu wanda ya kula dasu kasantuwar kowa yana harkar gabansa. Bayan gaishe gaishe Rahima to mike tayi serving dinsu, wajen ya yi tsit sai karar cokali da plate ke tashi, Hydar shi ke kallon kujerar da Sarah ke zaune, duk dago kai da zata yi sai sun hada Ido da shi sai kallonta yake kamar ya samu madubi, hakan yasa Sarah taji ta gundura da zaman gurin bata gama karyawa ba ta mike tace ta koshi tare da komawa sashinsu, Ubaidu shima ya mike yabi bayan matarsa, a haka dai suka watse suka koma falo suka kafa wata hirar Amma banda Abba da Ummi domin sashinsa suka wuce tare.
Bayan Sallar la'asar.
Ubaidu ya fita zuwa wajen wani abokin akinsu akan wata matsala daya taso, wutar wani anguwa ce ya lalace har an cire transformer din ta yi bindiga sai an gyara, kuma alhalin hakan yana karkashin office din Ubaidu ne, sannan mutanen anguwar sun matsa musu lamba akan gyaran shiyasa ya fita dan ya samu a daidaita lamarin a maida musu transformern. Umar kuwa ya fice zuwa filin kwallo dan duk yamma yana fita motsa jiki, Rahima tana daki tana barcin asara wanda ta saba zuwa anjima kuma ta raba dare tana kallo, Ummi tana sashinta, Mami tana kitchen tare da Mai aikinsu suna daura tuwon dare. Hydar dake zaune a tsakar gida ganin fitar Ubaidu akan idonsa ya sashi mikewa ya shigo falo, nan ma ba kowa sai kawai ya wuce sashin Ubaidun, ya yi sa'a kofar a bude take dan haka yasa kai ciki ko sallama bubu, Sarah dake kwance bisa kujerar mai zaman mutum uku ta mike da sauri tana kallonsa, Hydar ya bita da Mayan kallo yana kara karantar zubin halittarta, sai a lokacin Sarah ta tuna da irin kayan dake jikinta, vest ce fara da guntun siket brown color sannan ba birezia a jikinta, da sauri ta koma ta zauna ta rungume hannunta a kirji don ta kare kirjinta, tace cikin rawar mirya.Lafiya? Me ya kawoka side dina? Kuma ya kamata in zaka shigo ka Nima izini in an baka dama sai ka shigo, dan Allah ka fita.
Ni ba wani abu ya kawoni ba sai dan in san dalilin da yasa baki nuna farin ciki da zuwana ba, ke kadai ce a gidan banga kinyi d'okin ganina ba.
Ni babu wani abu a raina, kuma in da bana farin ciki da ganinka ba zan maka magana ba, in da kayi hakuri kajima a gidan zaka fahimci halina haka nake.
Ok naji, bani ruwa mana na sha saina wuce.
Cikin sauri ta mike tare da karamin filon kujera ta rungume a kirjinta ta nufi kitchen dinta, tana shiga ta sauke numfashi tare da dafe kai.
Wannan wani irin mutum ne mara tunani? Ko da yake tashin turai ne ba arabi.
Tace a ranta sai ta ajiye filon a gefe ta fara tunanin abinda zata samu ta sanya, apron ya fado mata a rai sai ta juya da sauri danta dauko ta daura a jikinta, sai kawai taga Hydar tsaye bakin kitchen din yana kallonta, sam bata ji motsinsa ba balle tasan yazo, ta yi baya ta dafe kirjinta saboda mugun tsoron daya ziyarci.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Meye haka?
Kalau, kawai na jiki shuru ne nace bari nazo na dubaki ko kin manta dani ne.
To ka fita bana son ganinka gaba daya kuma ruwa ne bazan bada ba.
Ta fada tana juya masa baya cike da tsiwa, sai dai cikin zuciyarta cike take da tsoron kar wani yazo ya gansu a haka, musamman Mijinta da take shakka. Hydar ya kutso kai ciki bata yi aune ba taji ya rungumeta ta baya, ta runtse Ido jikinta yana rawa so take tayi ihu amma tasan hakan ba mafita bace sai kawai ta saki kuka tana yi masa magiya daya saketa, Hydar ko sai fidda murmushi yake shaidan yana kara ingisa masa tururin sha'awarta, ya kai bakinsa kusa da kunnenta yace a hankali.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...