03

81 7 0
                                    

LUBABATU

03

Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir

_Daga fejin farko zuwa na biyu naga tsantsar kaunarku a gareni masoyana, lamura sunyi min yawa bazan iya bin comments dinku ina nuna godiyata ba, sai dai ga tarin godiya da jinjina a gareku bisa ga nuna kauna Allah ya saka da alkhairi ya biya muku dukkan bukatunki. Rahmarku ce, son so fisabilillahi_


*MAFARI... Waiwaye*

YOLA

Baihari local government
_Na kirkiri sunan Baihari a matsayin karamar hukuma tare da rigar ardo, duka kirkira nayi_

Karamar hukuma ce dake cikin garin Yola, wanda yake cike da tarin makiyaya fulanin asali sosai da al'adarsu, akwai wayewa ta yan boko masu riko da addini. A Baihari akwai kauyuka sosai a karkashinta wanda suke hade da hausawa da kuma wasu yarika daban daban, sai dai fulani sunfi yawa kasantuwar garin ya kafu dansu ne.

*Rigar Ardo*

Riga ce daya daga cikin kauyukan dake karkashin Baihari, yana da tarin tarihi wanda ya ginu tun zamani mai dogon zango, akwai matukar yalwar mutane da kuma arzikin makiyaya da manoma, hakan yasa rigar ya kara habaka sosai wanda kananun riga dake kewayensu suka maida rigar Ardo babban birninsu. Sai dai mutanen ciki akwai duhun kai ba suda wadataccen ilimin addini komai nasu sunfi sanya al'ada sama da addini, sannan boko bai je musu ba babu kuma wutar lantarki, suna da karancin rijiyoyi dole sai a rafi suke dibowa. Kadan ne suke iya fita suje cikin Baihari yin siyayya musamman wasu daga cikin masu siye da siyarwa da mata masu tallar nono, akwai wanda ma basu taba fita cikin birnin Adamawa ba.

Mahaifinmu Malam Adam ya kasance daya daga cikin mutanen wannan riga wanda nan ne asalinmu, ya kasance kuma babban makiyayi.

Tun ina yar shekara bakwai zuwa takwas na fahimci ni banda amfanin yin rayuwa a dorar duniya har kawo da nake shekara sha shida, kasantuwar na taso cikin wani irin ahali masu wuyar sha'ani da duhun kai wanda basu yadda da kaddara ba, ina samun tsangwama ta ko ina a cikin rigarmu ta Ardo, musamman mahaifina daya ke kyarana da nuna kyama a gareni, saboda yana ganin tunda aka haifeni na zame masa matsala kuma silar karayar arzikinsa, hakan yasa mutane da danginmu suke guduna saboda a ganinsu ni annoba ce, a gurin Ummanmu ce kawai nake jin dadi sai yar uwata Jidda. Umma ta yi ta yi da Baffa a kaini asibitin birni a dubani ko ciwon na can ne, amma fir yaki ya ce ciwon bana asibiti bane sai dai mu cigaba dana gargajiya.

Mu biyu rak suka haifa, sunan mahaifinmu Adamu, mahaifiyar mu Haajara, Naci sunan Kakata Lubabatu mahaifiyar Ummanmu, mun taso duk kakanninmu basa raye sun kwanta dama, auren hadi ne aka yiwa Ummanmu da Baffa, duk kuma haifaffun rigar Ardo ne, Baffa yana da kani guda Ibrahim yana zaune a cikin Baihari tare da matarsa guda daya mai suna Asma'u, 'ya'yansa uku, Muhammad sani, Hauwa'u itace tsarata sai takwaran Baffanmu Adam shine autansu. yana kasuwancin tumaki cikin rufin asirin Allah.

Adda Jidda ita ce babba sai kuma ni ke bi mata daga kaina Umma bata sake haihuwa ba duk da Baffanmu yaso ya samu yaro namiji amma saboda ni an haifeni da nakasu, sai ya roka Allah daya tsaida masa haihuwa in dai za a cigaba da ba shi irina to ya yafe, haka kuma Allah ya amsa adduarsa basu sake haihuwa ba har kawo girmanmu, duk da ya sake auren wata mai suna Aisha ko zai samu karuwar haihuwar namiji amma shuru kamar dan sanda yaci shirwa, zamansu bai dade ba ya rabu da ita. Adda Jidda ta taba aure sai dai bata kaiga Haihuwa ba mijinta ya rasu shekara uku kenan, akwai masu niman aurenta sosai amma ganin tana samawa Baffa kudi wajen tallar nono sai ya dinga jawa manemanta rai, har ya kaiga wasu sun hakura, masu naci ne dai suketa zarya da kara mita wajen ganin sun samu aurenta.

LUBABATUWhere stories live. Discover now