LUBABATU
04
Freepage.Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
*Ranar asabar*
Rahima ta gama shiryawa zuwan Hashim, sai rawar kai take yi da zumudi, duk kan mutanen gidan babu wanda bai san da zuwansa ba hatta Abba Ummi ta sanar masa. Rahima ta shirya masa hadden abinci sakwara miyar agushi da farfesun kayan ciki sai juice din kankana, ta kai dakin baki kana ta zuba wanka ta sanya Riga da siket yar kanti ta yane kanta da farin gyale, ta yi kyau Masha Allah sai zuba kamshi take. Karfe Sha biyu da minti goma dai dai mai mashin na sauke Hashim a kofar gidansu Rahima, da yake Alh. Lukman Giwa sananne ne sosai shiyasa gidansa baida wahalar ganewa Kuma sunan layin da Giwa street aka sanya masa, ya sallami Mai mashin ya isa bakin gate ya buga, Mai gadi ya bude ya kare masa kallo dan bai wayeshi ba.Wa kake Nima?
Wajen Rahima nazo, in banyi batan hanya ba nan ne gidan Alh. Lukman Giwa ko?
Eh Nan ne bari na isar da sakonka
Saiya rufe gate din ya wuce cikin gida, ya samu Rahima zaune a falo da hajiya Babba suna hira ya isar da sako ta ce tana zuwa sai ya wuce. Rahima ta mike ta kalli kanta da kyau.
Mami na hadu kuwa?
Rahima ai fade batawa, kinyi matukar haduwa sai kiyi maza ki tafi ki kaishi masauki.
Nagode Mami, in Ummi ta fito ki sanar mata da zuwan bakona, in yaci abinci Zan shigo dashi ku gaisa.
To ba damuwa Allah dai ya tabbatar da Alkhairin dake tsakaninku.
Ta amsa da Amin ta wuce, tana isa gate ta fita waje ta ganshi tsaye ya sanya duka hannunsa a aljihun wando yana kallon titi, ta tsaya tana kare masa kallo bata yi zaton zata ganshi a kafa ba saboda yadda yake nuna mata shi dan mai hannu da shuni ne, sallama ta yi ya juyo fuskarsa cike da mirmushi jajayen hakorarsa suka bayyana, dam kirjin Rahima ya buga ganinsa cikin munin kama domin yadda yake nuna mata kansa a waya gaba daya yasha bamban da wannan sai ta bayar ba shi bane bai rika yazo ba, cikin sanyin jiki ta soma magana.
Malam kaine me nima na?
Ya dage gira sama yana murmushi.
Nine, ko kina nufin baki gane Hashim ba.
Rahima ta waro ido waje tare da sakin baki cike da tsantsar mamaki.
Kana nufin kaine Hashim? Amma ya akayi kamanninka yasha bamban da yadda nake ganinka a hoto?
Wancen camera ne wannan kuma zahiri ne.
Tafdijam ta fada sai ta gyara tsayuwa ta rungume hannu a kirji gaba daya guiwarta ta sale da kuzarinta. Hashim ya matsa kusa da ita da sauri taja baya domin wani irin wari da kamshin turaren da yasa ya hade ya daki hancinta, ta toshe hanci tare da tsirtar da miyau. Rahima ta kasa danne kunci da bakin cikin da zuciyarta ke ciki saboda tsawon lokaci data dauka tana batawa akansa ba tare da tasan cewa shine Hashim ba a zahiri, ta hana idonta barci ta hana zuciyarta sukuni kullun cikin son ganinsa take a zahiri, tayi chart da shi na batsa sosai wanda take imagination dinsa tamkar a zahiri, kuka ne ya kubuce mata ta soma zubda hawaye kamar an bude famfo, ta kalleshi cikin tsana ta soma magana tare da zayyano masa duk kalmar data zo bakinta.
Wallahi da nasan haka kake a zahiri da ban bata lokacina ba akanka, Allah ya isa ban yafe ba, har abada bazan taba sonka ba wawa kawai kazami, ashe duk hotunan daka turo min ba Kai bane a jiki, kayi amfani da sune ka yaudareni, to Allah sai ya saka min macuci kawai, kuma ka bar kofar gidan nan tun kafin nasa a sakar maka karnika.
Ta juya a fusace zata koma gida, Hashim ya dakatar da ita cikin tsawa, ta tsaya ta juyo tana kallonta cike da tsantsar tsana mafi muni.
Ni zaki wulakanta har haka? To bari kiji wlh sai kinyi dana sanin abinda kika aikata min, wawuya mara tarbiyya, kila bata hanyar sunna aka haifeki ba shiyasa kike watsewa a waya kamar karuwa. Kuma kisa a ranki ko bajima ko ba dade sai kinyi nadamar abinda kika min.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...