09

55 5 0
                                    

LUBABATU

09

Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir

EWF.


Da Ubaidu ya dawo daga masallaci ya samu Sarah tana drying kanda da hand dryer, cike da mamki ya karasa ciki ita kuma tsoro ya kamata dan ba tayi zaton zai shigo a wannan lokacin ba, dan ya saba in ya dawo masallaci sai ya fara isa sashin Maminsa kafin ya dawo side dinsu, ya zauna gefen gado.

Diamond me ya hadaki da drying kai ke ba janaba ba ko haila? Kuma nasan shekaran jiya kika je saloon.

Um dazun na sakarwa kaina shawa ne da ruwan zafi saboda sanyin dana kwaso a lambu, shiyasa nake tsane sumar da dryer. 

Tace cikin in-ina da boye tsoronta a fili.

Ok in kin kammala kije ki dibo mana abinci bana jin zuwa dinning.

Da to ta amsa masa ta cigaba da gyaran cikin sauri tana hamdala a zuciyarta da karyarta ta shiga, ko da yake tasan zai yarda tunda a kwai kyakkyawar aminci a tsakaninsu.

*
Da safe

Ubaidu ya fito zai wuce aiki Sarah tayi masa rakiya ya shiga mota ya tafi sai ta wuce side din Mami ta sameta suka gaisa kana ta zauna suka cigaba da hira, ta kai kusan awa guda a gunta kafin daga bisani ta dawo dakinta tana budewa ta yi arba da Hydar ya daura kafa kan center table yanata danna remote din tv hankalinsa kwance, da sauri ta shiga ciki ta danne kofar da bayanta ta sauke gauron numfashi cike da faruwar gaba, ta kasa yi masa magana tsabar yadda ta firigita da ganinsa, Hydar ya taso cikin tafiyar takama ya iskota har inda take tsaye ya lakaci hancinta da yatsa ya soma magana cikin sanyin murya.

Akan Idona kika raka mijinki, na shigo na budaki ashe kin fita, na jima Ina jiran dawowarki. Sarah na kamu da sonki tare da tsantsar shawararki, dan haka Ina so ki shayar dani irin ruwan koramar da kika bani jiya domin bai kashe min kishin ruwa ba, nayi harka da mata sosai amma ke naki lanbun na musamman ne domin ya kunci kayan alatu iri iri.

Sai ya ja fasali tare da rausayar da kai gefe yana yi mata kallo kasa kasa mai kunshe da sakonni da yawa, Sarah ta sauke numfashi.

Bana tunanin wannan boyayyen alakar zai cigaba, duba da irin kalubalen da zamu muskanta duk da na samu nishadin da ban taba damu ba a jiya, Zan jure iya wanda ka bani ya wadatar dani, zaifi kyau mubar wannan sirrin a haka.

Dako kin yi babban nadama.

Ya fada cikin izza tare da kamo wuyan rigarta ya fincikota ta fada kirjinsa ya maida hannunsa zuwa bayanta ya rungumeta tsam a jikinsa kamar zai maidata ciki, Sarah ta dago kai sai kawai ta hade bakinsu domin bata jin zata iya hakura da shi, haka suka shagala a wajen tare da lulawa wata duniya. Bayan minti sha biyar suka ji ana kokarin bude kofar da sauri suka saki juna tare da danne kofar dukansu su biyun suna danne numfashinsu, da kyar Sarah ta lalubo natsuwarta ta ce cikin sanyin murya.

Waye ne?

Ni ce Anty.

Cewar Rahima da sauri Sarah ta nuna masa ya shiga kitchen da hannu, bai musa ba yaje ya boye a can, sai ta budewa Rahima ta shigo.

Anty dama pink din gyalenki zaki aramin saboda yau muna da birthday din wata friend dina. Daga makaranta zan wuce.

Ok ta ce sai ta wuce daki ta je dauko mata, ita kuma ta zauna akan kujera tana kallon tv, karar waya taji kamar daga kitchen sai ta juya da sauri tabbas daga can taji kara, an kira Hydar ne sai ya yi saurin kashe kiran yana dafe kai. Rahima kamar an ingizata ta mike tana cewa.

Su anty kenan sarkin iyayi harwani sauya ringing tone ta yi, saboda shiririta wayar ma a kitchen ta bari.

Ta isa kitchen din kenan ta kama handle sai ga Sarah ta fito daga bedroom ta ce da karfi.

LUBABATUWhere stories live. Discover now