LUBABATU
11
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabirEWF.
_*Freepage* yana gabda karewa, zaku iya fara biya domin a saku a cikin paid group. Kamar yadda kuka sani duk paid books dina 200 ne insha Allah wannan ma kudinsa 200 ne babu tsada._
Pay N200 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card a wannan 09034940106, a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.
Hydar yana tsaka da binciken dakin Mami ya bude bedside drower yana dubawa da hannu yaji kamar bandir din kudi a leda da sauri ya cirosu ya bude yaga dalar America bandir biyu wanda yake da yakinin ko wani bandir daya dubu dari biyar ne, kenan million guda ya samu a dakin Mami, ya yi matukar mamaki saboda yadda yaga Mami da kamewa baiyi zaton ganin komai a dakinta ba, ya karasa bincike dakin bai samu komai ba banda wannan kudin, sai ya fito rike dasu cikin leda ya isa babban falo jiki a sanyaye, yadda suka ga ya shigo jikinsu ya basu da matsala ya karasa ciki cike da damuwa a fuskarsa ya ciro kudin a leda ya rike, ko wanne cikin tashin hankali da kosawar suji a Ina yaga kudin, Abba ya jefa masa tambaya.Habawa ni nasan kudin beyi nisa ba saboda jiya da daddare na shigo dasu, haka suke bandir bandir din dubu dari biyar biyar in dollars, lallai da ace nayi sakwa sakwa tabbas da nayi asararsu. Kuma naga bandir biyu ne saura biyu da alama barayon ya raba gurin daya boye kudin. Hydar a wani daki ka samu wannan kudin?
Hydar ya sauke gauron numfashi yace cikin dakiya.
Dakin Mami wato Hajiya babba, a can na samesu cikin bedside drower dinta an sanyasu a leda, na kara bincike ko Ina amma iya su na samu.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun
Mami ta ambata da karfi tana dafe kirjinta cike da gigicewa, suma sauran duk salati suka shiga yi ko wanne cike da ban ta'ajibi, a dai dai lokacin Ubaidu ya fito daga dakin Ummi, ya kammala duba ko ina be samu komai ba, ya samesu a tsaitsaye a cikin wannan yanayin mamaki, ya isa da sauri yana tambayar.
Lafiya? Me ke faruwa?
Babu wanda ya iya bashi amsa sai maganar Abba ne ya tsinkayar dashi abinda ke faruwa.
Hajiya kin bani kunya wlh ban taba zaton mugun halinki ya kai haka ba, dama Hajiya karama tasha gayamin kece barauniyar gidan nan bana yarda yau dai asirinki ya tonu, Kuma kiyi maza ki fito min da sauran kudina dan wlh akansu Zan dauki mummunar mataki akanki. Barauniyar banza kawai.
Haba Alhaji yaushe rabon dana je dakinka? Wallahi tallahi bansan da wannan kudin ba, bani ce na sace su ba sai dai in wani ya sata ya kaimin dakina domin ya kulla min sharri.
Cewar Mami ta fashe da matsanancin kuka ta samu kujera ta zauna domin kafafunta sun mata nauyi ba zata iya tsayuwa ba. Ubaidu ya dafe kansa daya ji ya sara masa ya ce cikin matsanancin damuwa.
Mami na ba zata taba satar kudinka ba wlh sharri ne aka kulla mata, haba Abba kafi kowa sanin halinta, don Allah kar ka yanke Mata hukunci cikin fushi yanada kyau ayi bincike sosai insha Allah gaskiya zata yi halinta.
Dalla rufe Mana Baki, in ba ita ce ta dauka ba taya za a samu kudin a dakinta, yau dai anyi walkiya kowa yasan itace barauniyar gidan nan, Dan haka Hajiya babba ki je ki dauko Masa sauran kudinsa ki kawo ehe.
Cewar Ummi cike da hargagi, Rahima ta ce cikin kuka.
Allah Mami ba zata yi sata ba kazafi ne kawai. Barayo dai yasan kanshi.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...