LUBABATU
05
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
*Bayan shekara d'aya*
Zuwa wannan lokacin mun shiga cikin wani irin mawuyacin hali sakamakon gobara da muka yi, dukkan shanun Baffa sun kare rabi a ciki muka cinye saboda siyan abinci rabi kuma a zaryar kaini asibiti ya tafi tare da siyan wasu kayan amfanin gida, wannan lokacin mun gama tagayyara saukinmu kanin Baffanmu yana taimaka mana da wasu abubuwa, shima dai ba wani karfi ke gareshi ba sai rufin asirin Allah. Har mun cire rai da sake ganin Adda Jidda saboda har lokacin basu zo ba, Baffa shima ya sare tare da gasgata zancen mutanen gari cewar yabi son duniya ya saida Jidda.Muna cikin wannan yanayin ne sai ga su Adda Jidda sun zo, rigar ardo suka fara sauka, a nan ne aka sanar dasu mun bar gari, ganin Jidda cikin shiga ta alfarma da kyawun kamala yasa mutanen gari jin kunyar abinda sukawa su Baffa, Haruna ya yi musu alkhairi suka tawo cikin Baihari, muna zaune da Umma muna gyaran dawa da Baffa Iro ya kawo mana zamu nika a injin dutse mu samu garin tuwo, sai muka ji kugin tsayuwar mota a kofar gida bamu kawo wajenmu aka zo ba, ganin Baffa cikin sauri kamar zai kifa ya shigo bakinsa a wangale yana dariya yasa muka bishi da kallon mamaki, dan rabon da mu ganshi a irin wannan yanayin mun mance ranar, Ganin Jidda na biye da shi a baya tare da Haruna yana na mike da sauri tire din dawar dake ciki ya watse a kasa na mance sam yana kan cinyata, na ruga a guje ina murna da kuka a lokaci guda naje na rungumeta, itama ta kamani tana kukan murna sai da muka dauki minti biyar a haka kafin muka saki juna muna sharewa juna hawaye, Jidda ta kamo hannuna muka dawo kan tabarman dana tashi muka zauna kana duk suma Baffa suka zauna a wata tabarman, aka gaisa da juna tare da nuna tsantsar jimamin rashin ganinsu, Haruna ya bada hakuri tare da fadin.
Baffa kuyi hakuri wallahi ayyuka ne suka min yawa ban cika zama ba, itama Jidda sai ta yi kusan wata bata ganni ba in na fita kasar waje. Amma insha Allah ba zamu sake yin shuru haka ba, yanzu haka ma Ilori zamu je wani aiki, kuma zamu kwana biyu a can shiyasa nace bari muzo mu gaisa.
Ka kyauta amma dan Allah kar ku kuma yin shuru irin haka, dan babu irin abinda ba ace mana ba akan shurunku, shiyasa ma muka dawo nan da zama.
Insha Allah Baffa ba zamu kuma ba.
Yace haka cike da biyayya. Ni da Jidda muka shiga dakin da yake mallaki na muka dasa hira. A wannan ranar ba karamin farin ciki muka kwana cikinsa ba, munyi hira munyi wasa tare da tuno baya. Adda Jidda ta fada min b'arinta uku basa zama ciki harda yan biyu, Kuma cikin duk sai sun haura wata uku take barinsu, likita ya tabbatar mata da mahaifarta ba tada kwari, kuma duk b'ari sai anyi mata karin ruwa da jini, tare da shan kayan marmari na karin jini, tabani labarin daular da take ciki dan gidanta na kaduna yafi wanda ta fara zama a Yola sau uku, sai dai ta ce min.
Lubabatu wlh Abu guda ne baya min dadi zaman kad'aici da nake fama ga shegen kulle da Haruna yake min, yaki bari nayi sabo da kowa a unguwarmu, ke in takaice miki ban taba fita a kafa ba sai a mota, kuma bama fita da rana sai dare, Kuma bamai zuwa min nima ban zuwa wajen kowa, sau daya ya taba kaini wajen yayarsa a abuja, suma basu taba zuwa ba har na gaji da naci, nayi masa korafi harna gaji yace shi haka tsarinsa yake in ina son zama da shi to sai dai nayi hakuri mu tafi a haka.
Na jinjina lamarin kuma hakan ya dameni, amma saboda in kwantar Mata da hankali sai na nuna Mata hakan ba komai ba ne.
Karki damu da haka Adda tunda yana sonki kuma baki rasa komai ba ki cigaba da hakuri watarana sai labari. Amma banda wannan damuwar ba kya fuskantar wata matsala ko?
A'a gaskiya Ina cikin kwanciyar hankali da farin ciki.
Allhamdulillah burina kenan naji haka daga bakinki saboda zuciyata ta samu natsuwa.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...