LUBABATU
12
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabirEWF.
_*Freepage* yana gabda karewa, zaku iya fara biya domin a saku a cikin paid group. Kamar yadda kuka sani duk paid books dina 200 ne insha Allah wannan ma kudinsa 200 ne babu tsada._
Pay N200 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card 09034940106, a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.
Lubabatu ta farka bayan fitarsa da kusan minti arba'in, ta dinga kallon silin tare da shiga dogon tunani me tsawo, ta dauki kusan minti ashirin a haka kana taji motsin bude kofa da sauri ta maida Ido ta rufe ta yi kamar tana barci, Haruna ne ya shigo yazo kanta ya tsaya yana kare mata kallo ya tabbatar da barci take bata farka sai ya duba ledan jininta yaga yayi rabi sai kawai ya koma ya zauna ya cigaba da danne danne a waya. A takaice dai a ranar sun wuni tare a dakin yana jinyarta, da jinin ya gama shiga jikinta ya cire mata kana ya tasheta ta tashi ta jingina jikin pillow, ya kira aka kawo mata abinci ya bata taci kadan kana ya taimaka mata tayi wanka ya sauya Mata wasu kayan, ya maidata kan gadon jinyar sai taji jikinta yayi mata dadi har wani karfi taji, a zuciyarta tana mamakin irin kirkin da yayi mata yau, shine ya maida mata wani jinin ya cigaba da shiga jikinta, da yake ya iya komai akan Jidda domin likita ya koyar da shi.Kwanan Lubabatu biyu tana jinya saida tasha ledan jini hudu kafin taji sauki sosai, a kwana biyu Haruna ya shayar da ita ruwan mamaki yadda yake bata kulawa na musamman har addu'a take a ranta Allah yasa zamansu ya daure a haka wata kila da zata samu farin ciki ko kadan ne a rayuwarta, tasan dai duk yanayi ne domin cikin dake jikinta wanda take da yakinin akwai mugun shirin da yake akanta. Hawaye ya cika mata ido ta shanye su bata bari sun zubo ba, tana zaune jikin pillow shi kuma yana zaune a wannan farar kujerar kamar yadda ya saba, yana jiran likita yazo domin sunyi waya dazun ya bukaci ganinsa. Minti goma sai ga Dr. Amiru yazo suka gaisa yana cewa.
Amarya ta samu sauki sai sallama ya rage.
Yana zancen ya isa jikin gadonta yana dubata tare da yi mata sannu ta amsa tana gyada kai, Haruna ya daura kafa daya kan daya yace cikin murmushi.
Dama saukin nake jira ta samu domin cikin jikinta nake so ka cire, kuma kaga sai ta sosai samu lafiya hakan zai faru.
A cire cikin kuma?
Dr. Amiru yace yana kallonsa, Lubabatu taji gabanta yayi mummunar faduwarsa nan take tsoro ya rufeta ta tashi zaune cikin rikicewa tana kallonsa. Haruna ya mike ya zuba hannunsa a ajihun wando yace cikin dage gira.
Kwarai cirewa nake so ayi doctor, ko ka mance aikinmu na baya ne? To ya kamata ka tuna domin zan daura daga inda na tsaya kamar yadda nayiwa Jidda to ina so itama na aiwatar da komai akanta.
Abokina baka ganin ita wannan tana dauke da lalura, Ina ganin ka bari cikin yayi kwari sai a cire a duk lokacin daka bukata.
Hmmm nifa yanzu nake so a cire shi. Lubabatu Bari na baki labari gutsire yadda aka yi Jidda ta rasa cikinta na farko.
Ya kare maganar Yana kallonta hankalinsa kwance fuskarsa dauke da annashuwa, ita ko idonta sunyo waje ta shiga matsanancin firgici yadda take zaune a kan gadon kamar za a ce mata ket ta ruga a guje. Haruna ya zauna ya cigaba da cewa.
Likita hada kayan aiki domin yau nake so a cire cikin nan.
Angama ranka ya dade.
Cewar Amiru ya isa wani bangare ya soma ciro kayan aiki, Lubabatu fitsari ta saki akan gadon tsabar firgici, wani irin dunkulallen Abu ya tokare mata zuciya ta kasa motsin kirki balle ta samu halin kuka. Haruna ya cigaba da cewa.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...