LUBABATU
08
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir_Afwan sisters da jina shuru kwana biyu hakan ya faru ne sanadin jiki da jini. Insha Allah daga yanzu zaku rika samun update akai akai. Nagode da kulawarku gareni_
KADUNA.
Haruna ya isa kaduna da wuri, ba bata lokaci ya kira driver yazo ya dauke shi suka wuce zaria. Bayan sun isa wani gidansa dake can, sun samu komai na gidan a gyare yake saboda akwai mai gadi da me kula da cikin gidan, falo ne madaidaici da daki uku a ciki duk da bayi sai kitchen a falo, akwai komai na bukata a gidan tamkar da macen aure dake rayuwa a ciki. Koda Haruna da yaga babu wani gyara sai ya kira number wata mata ta dauka ya tabbatar mata da sun iso suma su karaso. Minti ashirin wannan matar da ya kira ta iso tare da wasu mata uku wanda suke a matsayin yan uwansa, sun zo tare da kulolin abinci na tarban baki, suka tsara komai tamkar a gidan suka yi girkin. Haruna ya kira driven su Lubabatu ya gaya masa address din gidansa yace in sun karaso ya kira shi koda bai gane ba zai sa azo a dauke su, daga nan sai ya wuce zuwa cikin garin Zaria.____
4:46pmMotar amarya ta karaso basu sha wuyar gane gidan ba, wa'innan matan suka fito har wajen motar suka yi musu iso zuwa cikin gidan, suka yada zango a falo cikin gajiya ko wannensu yana wash saboda zaman mota, sunyi saurin isowa saboda babu tsaitsaye a hanya, sun samu kyakkyawar tarba fiye da zatansu, sai suka zama kauyawa sunata raba ido gidan mai dankaren kyau, ga abinci kala kala da nama har sai da suka ture duk kuwa da yunwar da suka kwaso, bayan sun huta sosai sai suka gabatar da sallar azahar da la'asar, kana suka zauna zaman hira da wa'innan matan tare da gabatar da juna. Gabda magrib ne matan suka wuce gida da nufin zasu Zo da safe su kawo musu abin kari kafin su wuce. Lubabatu tunda suka iso fuskarta tana rufe da mayafi, gabatar da sallah shine ya dagata a inda ta zauna, ruwa kadai ta iya kurba ta kasa cin abinci duk yadda su Inna suka matsa Mata data ci Amma taki, dole suka rabu da ita. Da dare yayi suka kwanta a falo kan kafet suka ce Lubabatu ta shiga cikin daya bedroom din ta kwana tunda gidanta ne Amma fir taki dole suka kyaleta. Su dai sun samu barci amma Lubabatu bata runtsa ba har asubahi sai mugun tunani barkatai daya addabi zuciyarta duk yadda taso ta yakicewa kanta ta kasa, sai ma kuka data yi ma'ishinta ba mai lallashi dole tayi shuru dan kanta. Koda aka kira Sallah ita ce ta tashi sauran matan suka gabatar da farali.
***
Da safeWa'innan matan sun kawo musu abin kari, bayan gun gama suka yi wanka suka shirya, hatta Lubabatu itama tayi wanka ta shirya cikin wani leshi da matan suka kawo mata, tayi mamakin yadda kayan suka zauna a jikinta ganin basu san girman jikinta ba sai dai tasan kila Haruna ya gaya musu, ba wani kwalliya tayi ba sai mai kawai ta shafa fuskarta ta fayau kamar wcce ta tashi daga cutar shekara idanunta sun firfito waje saboda rama, karfe tara da rabi Haruna ya zo gidan da yake be kwana anan ba, bayan sun gaisane yace su fito mai motarsu yazo, cikin hanzari suka mike dan dama tuni sun gama shiri, su Inna suka dankawa Matan Nan amanar Lubabatu, suka amsa tare da jaddada musu zasu rike amana, sun hada musu sha tara na arziki danginsu atamfofi da kayan abinci sai da suka cikasu da mamaki sosai, suka rakosu har mota suna yi musu godiya, Lubabatu taso fitowa Amma sun hanata, sai kuka take tana gunji, ji take ta rabu dasu kenan ba zata sake ganinsu ba, gaba daya taji ta tsani kanta da rayuwar, mutuwa Jidda ya zame mata sabo, komai gani take kamar a mafarki. Tunani da damuwa sun mata yawa kanta ya yi zafi sosai da tsananin ciwo, wani irin jan numfashi tayi wanda taji kanta yana yawo a sama, nan take jiri ya kwasheta ta fadi a sume, su kuma duk suna waje Haruna ya basu makudan kudi nashan ruwa a hanya suka wuce. Sai da suka daina ganin motarsu kafin suka dawo ciki suka samu Lubabatu a wannan halin, Haruna ya isa gareta da sauri yana cewa daya daga cikin matan.
Hajiya Hindu suma ta yi, ina ga kuje kawai zan tura muku kudi ta account nagode da kokari.
Ok ba damuwa, muke da godiya Allah ya baku zaman lafiya ya sanya alkhairi.
YOU ARE READING
LUBABATU
General FictionDuk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hank...