🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA BIYU*
______________Wayanta ne ta soma Ring, sai ta ɗan dakata daga tafiyar yauƙin da take yi, tare da ajiye Robbern awaranta ta soka hannun ta a cikin Aljihun doguwar riganta; tare da zaro wayanta tana kallon me kiran. Sunan Besty ne ya fito ɓaro-ɓaro a kai, ba tare da jan lokaci ba tayi peacking tana karawa a kunne da cewa, "ya dai Besty?""Lafiya, ke nake jira tun ɗazu gani a wajen suyan ki, ko dai yau baza kiyi bane don naga time yana wucewa?"
Yamutsa kyakkyawar fuskarta tayi cike da yanga irin nata tace, "No gani nan a hanya ai, ina zuwa."
"Ok kiyi sauri da Allah, akwai labari wlh."
"Haba nawan?" Tayi maganar tana ɗan sakin fuskarta kaɗan
"You just have to come and see for yourself. "
"Ok. I'm coming" Sai ta zare wayan a kunnenta tare da zura ta a cikin Aljihun, sannan ta ɗauki Robbern awaran ta ci gaba da tafiya. A haka tana yi kamar baza ta taka ƙasar ba har ta fita layin gidan su, duk inda ta wuce gungun maza kallon ta suke yi, majority wasu gulman ta suke yi, ƙalilan kuma suna mata magana kasancewar mutanen ta ne. Sai dai ta gaisa dasu kawai ta wuce har sanda ta kai babban titi inda take yin tuyan awara
Da sauri Ibrahim her friend; ya taso daga saman wani benci da ke gaban shago a wajen; ya sauke mata farantin saman kanta yana dariya tare da cewa, "Oyoyo my Besty, I've seen you before everyone."
Murmushi tayi tana ajiye Robbern tace, "uhm Ni ban ga alama ba, bayan yau kwata-kwata ban ganka ba sai yanzu, ina ka shige ne?" Ta ƙare maganar tana narkar da manyan idanuwanta a cikin nashi, tare da sauke mishi wani kallo da ke rikitar da duk wanda ta yiwa shi
Shima ɗin kafe ta yayi da idanun yana cije leɓe cike da tsantsan sha'awar ta da ƙaunarta yace, "oh my Besty! Me kike ci na baka na zuba? Ai abun da yasa na kira ki kenan ki ƙariso don in shafa miki labarin abun da yake faruwa... Amma tukunna dai bari in soma hura miki wutan nan don naga time na gudu." Sai yayi saurin ɗaukar kafi-tankiyan ya ajiye sannan ya soma jera itacen a ciki, a haka ya gama ya hura wutan
Ita kuma har ta saka kujera ta zauna suna magana a tsakanin su. Wani almajiri ta kira ta kalli Ibrahim ɗin tare da cewa, "Besty ba shi kuɗi ya ƙaro min icce, don wannan bazai ishe Ni ba."
"Ok nawa kike buƙata?" Yayi maganar yana ɗago kai tare da kallon ta
"Two hundred is ok." Sai ta kalli Yaron tace, "ka siyo min iccen ne na ɗari, sai yajin hamsin."
"To." Yace yana amsar kuɗin a wajen shi
Komai Ibrahim yayi mata hatta da ɗaura mai a wuta, sai da yayi zafi sannan ita ta soma jefa waran tana cewa, "My Besty bani labarin in sha na ƙosa."
Dariya yayi yace, "Arab Sarauniyar son labari! Yanzu kuwa." Sai ya gyara zama a saman bencin da ya ɗauko
Har zai soma maganar kuma sai wani saurayi ya iso wajen yana kiran sunan shi, tare da ba shi hannu suka gaisa, sai ya zauna a kan bencin shima yana kallon Arab tare da cewa, "Ƙin fi ƙarfin Yaro ya ne?"
YOU ARE READING
RUƊIN DUNIYA!
RomanceThe lives of some sisters. Haƙiƙa Ina matuƙar son kuɗi, ji nake yi idan babu su kamar bazan iya rayuwa ba, ɗaukar da nayi musu su ne suke kare mutunci, sannan kuma su ne suke sa wa a yi maka soyayya, ashe ba haka ba... Tabbas kuskure. nayi su da dam...