🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼♀️*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*DATA SHARE*
Call, message or whatsap 07065334256
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 daysAirtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 950
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days._________________________
*BABI NA SITTIN DA BIYU*
_______________Kamar yanda Arab ta yanke shawarar fasa auren; hakan ne kuwa, ta sanar da Inna, "ta fasa yanzu Malik zata aura."Kuma babu abin da Inna tace tunda ta ji ra'ayin ta, so bata matsa mata ba sai cewa tayi, "ta kira su sai su zo su amshi kayan su kawai."
Kiran Hajja Arab tayi ta faɗa mata, "ita a yanzu ta fasa auren Aliyu."
Amma me? Sai Hajja ta hau salati tana sallallami tare da furta, "don Allah faɗa min idan wani abu yayi miki amma zancen fasa wa ai sai ki ruɗa min ciki Humaira? Ai wannan maganar ma bata taso ba sai da abu ya kusa? Wata ɗaya fa?"
"Hajja Ni fa ba wai saboda wani abu zan fasa ba, kawai dai na canza ra'ayi ne, tunda kinga shima ba ya so na, nima haka. kawai a bar zancen auren nan."
"Haba ƴar albarka. Don Allah ki dena wannan zancen, ki yi haƙuri a yi auren nan Humaira, yanzu idan Dadyn shi ya ji zancen ma hankalin sa tashi zai yi tunda kinga ba ishashshen lafiya ya cika ba, ai mu muna son ki kar ki wani ɗaga hankalin ki, Aliyu taurin kai ne dashi kuma ke kaɗai za ki iya dashi tunda wlh kun dace da juna, ai bazan so mu rasa kyakykyawa kamar ki ba, haba A'ishatu ki yi koyi da mai halin mana."
Dariya Arab tayi tace, "kai Hajja, kina da abun dariya wlh."
"To ba dole ba, ai yanzu farin ciki nake yi da auren nan, amma kuma idan kika fasa duk za ki ɓata mana murnan namu, ki yi haƙuri a yi auren nan komai zai wuce, ke ma za ki so shi tunda Aliyu yana da kirki na rantse da Allah."
"Lallai. A hakan?"
"Ƙwarai kuwa wlh, yana da kirki, daga baya ne ya sauya hali, amma ina ganin har da rashin Mata, dama an ce Maza idan sun soma zama tuzurai to kansu ma kwance wa yake yi, za ki ga suna wasu abubuwa kamar somin hauka."
Sosai Arab take dariya a yanzu, cike da farin ciki tace, "wato Hajja shima ya soma haukan ne?"
"Ke rufa min asiri kar ya ji, amma dai ki yi a hankali, Ni dai gani nake yi har da firgita na rashin samun natsuwa. To amma yanzu kin haƙura ko?"
"Shikenan Hajja ya na iya? Zan yi tunani a kai."
"Ai babu maganar tunani, tunda ma kika soma wannan tunanin dole in yi wani abu, domin na tabbata Aliyu ya soma ba ki tsoro ne, kina tunanin irin zaman da za ki yi dashi, but babu komai sai alkhairi, raina Ni dai yana son wannan auren wlh."
Arab dai babu yanda ta iya haka nan ta yarda ta amince da maganar Hajjar. Daga ƙarshe tace mata, "ta tura mata numban Aliyu zasu yi magana."
Hakan yayi mata dad'i. Da sauri kuwa tace, "yanzu zata saka Muhibba ta tura mata."
YOU ARE READING
RUƊIN DUNIYA!
RomanceThe lives of some sisters. Haƙiƙa Ina matuƙar son kuɗi, ji nake yi idan babu su kamar bazan iya rayuwa ba, ɗaukar da nayi musu su ne suke kare mutunci, sannan kuma su ne suke sa wa a yi maka soyayya, ashe ba haka ba... Tabbas kuskure. nayi su da dam...