Talatin da takwas

87 9 1
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

             *P.W.A✍️*








_________________________

*BABI NA TALATIN DA TAKWAS*
_______________ *ZARIA CITY*
                Yanda Malik yake sharara gudu kafin ƙarfe biyar da rabi ya isa can, dayake ya saka abun a ransa shiyasa ba ya tunanin komai; shi dai Fatansa kawai ya samu abun da ya je nema. Da kwatance bayan ya isa anguwan ya samu gidan su Arab, ya tsaya a bakin gidan yana neman yaron da zai aika

Ya fi kusan minti goma kafin ya samu wani yaro da ya fito a nan maƙotansu, ya kira sa ya aike sa a kan, "ya shiga gidan ya ce ana sallama da A'isha."

Da gudun sa Yaron ya shige ciki, a falo ya tarar da su a zaune suna magana, sai ya faɗa musu abun da Malik yace

"Kai Muhseen waye yace ka kira ta?" Inji Inna

"Wani ne a mota."

"To ka ce ba ta nan."

Har zai tafi sai Zahra tace, "bari in je in duba Inna." Sai ta miƙe ta bi yaron suka fita, nan kuwa ta hangi Malik a jingine da motansa, mamakin ganin sa tayi tunda bata manta fuskarsa ba, tabbas shi ne, shiyasa ta nufe sa tayi masa sallama

Shi kuwa murmushi yayi ya amsa mata tare da faɗin, "ashe dai da gaske ke ƴar uwan A'isha ce? dama na ji a jikina tun lokacin da na soma haɗuwa da ke."

Itama murmushin tayi tace, "kaima ba ka manta Ni ba ashe?"

"Taya zan manta ki? Ai bazan taɓa manta ki ba ko don kamanki da A'isha, kuma dalilin da yasa nayi miki magana kenan a ranan, ga kuma abun da Nawwara tayi miki ai dole in tuna ki." Yayi maganar yana darawa; wanda alamun farin ciki ne yayi masa yawa a lokacin

Zahra tace, "wai dama ka san Ƙanwata ne? Kuma ban taɓa ganin ka a wurin ta ba?"

"Haka ne, nima sai yanzu na san gidan ku ai, lokacin na je gidan Ƙanwar Mummy na a Kano a can na ganta, kuma dama na daɗe ina neman ta gaskiya." Sai yayi shiru yana ɗan jan numfashi, ba tare kuma da ya faɗa mata alaƙar su ba yace, "Allah yasa zan iya ganin ta?"

Jin abun da ya furta shiyasa Zahra ta ɓoye mishi gaskiya tare da ce mishi, "su ma kansu basu san inda take ba, neman ta suke yi."

Wannan maganar ba ƙaramar rikitar da Malik yayi ba, nan da nan ɗan fara'an nasa ta gushe, cike da tsananin damuwa yake cewa, "kuna nufin ba ku san inda take ba? Amma kun bincika ƴan uwa da Abokan arziki but ba a ganta ba?"
                
Shiru Zahra tayi

Sai ya sake cewa, "don Allah ki faɗa min idan kin san inda take, Ni na zo ne domin ta; ba wai don abun da ya faru tsakanin su da gidan Aunty na ba, muna da alaƙa da ita."

"Gaskiya idan na ce maka ga inda take nayi ƙarya, ita da kanta ta bar gidan; mu kanmu neman inda take muke yi, amma mun san dole zata dawo da ƙafafuwan ta tunda halin ta ne."

"Wannan ba shi ne abun dogaro ba, Yakamata ku ɗauki mataki kar wani abun ya same ta."

Dariya tayi tace, "kar ka damu, Arab tana nan wlh amma mu bamu san inda ta ɓoye ba, ko kwanaki ta aiko mana da saƙo kuma ta ce zata dawo."

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now