Sittin da Tara

104 10 0
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

        *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

            *P.W.A✍️*



*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    950
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  530
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼








_________________________

*BABI NA SITTIN DA TARA*
_______________Yanda ya tunkaro ta da Motan, bata taɓa tunanin zata iya kufce masa ba, domin ita kanta bata san sanda ta faɗa cikin kwalbati da ke wurin ba, sai ga ta tsamo-tsamo cikin kwata

Shi kuwa wawan birki ya ja ganin ta tashi a wurin. Wani mugun kallo ya watsa mata da idanunsa da suka fita a hayyacinsu, sun yi jazur alamun tamkar ba ya cikin tunanin sa, motan ya bama wuta ya bar wurin a sukwane

Yayinda Arab ta bi motan da kallon takaici zuciyarta na tafarfasa, ta kasa ma fitowa a cikin kwatan duk da tana jin hayaniyar mutane da suka fara taruwa, suna tambayar ba'asin abun da ke faruwa har ta tsulmiya kwata? Sai sannu suke mata. Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta sannan ta fito ta soma tafiya, baƙin ciki duk ya cika mata zuciya sabida yanda yasa ta ɓata kayan ta, ranta a ɓace ta tsaya tana duba wayanta, ganin babu abun da ya same ta sai ledan maganin ta ne ya ɓaci, abun hawa ta soma tare wa. Daƙyar ta samu ta hau ya nufo da ita gida

Mai gadi yana buɗe mata gate, ya soma mata sannu cikin girmamawa sai kallon munafurci yake mata

Amma ko kallonsa bata yi ba ta wuce ciki. Kai tsaye sashin ta ta wuce ranta a ɓace, sai dai da alamun babu Aliyun a gidan, shiyasa ta ja ƙwafa tana shigewa nata ɗakin, tayi wanka sannan ta canza kaya

A lokacin ne Muhibba ta shigo ɗakin tana cewa, "Aunty yau ina kika je muna ta neman ki? Aka ce mana kin fita?"

Sai da ta yatsina fuska before tace, "asibiti na je wlh, na manta ban sanar muku zan fita ba."

"Subhanallah... Ba ki da lafiya ne?"

"No kar ki damu, a kan wata matsalar ce ya kai Ni."

"Ok to, yanzu in kawo miki abinci ne? Tunda na ga kin dawo kamar a gajiye."

"A'a, ba na ci." Ta furta idonta a waya tana latsa wa

Sai Muhibban bata sake cewa komai ba ganin ta kanga wayan a kunne, sai zama tayi a gefen ta tana kallonta

"Aunty Ummu."

"Na'am Arab, me ya faru ne ɗazu har na ɗauki wayan kuma kika katse? And na kira ba ki ɗauka ba?"

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now