Hamsin da biyu

114 11 2
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*








_________________________

*BABI NA HAMSIN DA BIYU*
_______________ *ABUJA STATE*
                 Jin abun da suka ce Arab ta fito musu a Mutum babu kunya babu tsoron Allah tace, "baza ta iya auren sa ba, baza ta iya zama da mugu kamar sa ba."

Hajja tace, "yo idan ya aure ki ai bazai miki mugunta ba tunda kin zama Matarsa, yanzu ma don ƙaddara ce ta riga fata, kuma ba ma fatan a tauye miki haƙƙin ki shiyasa muka yanke wannan hukuncin."

Dady ma yace, "daughter kar ki ce haka kinji? Dama muna neman Matar da zamu aura mishi tunda ya ƙi jin maganata; ba tun yanzu ba nake mishi nacin aure amma ya ƙi bin umarni na, amma yanzu abun da yayi miki ya zama wajibi ya aure ki, kar ki damu da abun da zai miki Ni zan ɗauki mataki a kan haka, daughter na yaba da hankalin ki shiyasa nake fatan ki zama Matar ɗana kinji ko? Ki dena tsoron abun da zai faru."

Sosai Dady yake lallaɓa ta, hakan ne yasa Arab bata ce komai ba; ba don ta amince da auren sa ba, a ganinta zasu gaji su bari ne, bari dai ta bar gidan baza su sake ganin ta ba ma

Dady kuma a take a nan ya kira Doctor Mamman yake tambayar sa, "ko Aliyu ya zo asibitin?"

Sai yace mishi, "eh, yanzu ya zo."

"Ok. Ka je ka sanar masa, duk abin da yake yi ya bari ya zo ya same Ni yanzun nan a gida, idan kuma ya ƙi zai ga fushina."

"Insha Allah Dady." Ya furta cikin girmamawa

Shi kuma Dady ya zare wayan daga kunnen sa yana sake kallon Arab tare da cewa, "ki yi hakuri daughter ki dena jin tsoro, babu abun da zai sake faruwa, mun san cewa idan muka bar ki a haka kamar mun zalunce ki ne, amma idan kika aure sa tamkar mun miki gata ne, a nan gaba za ki gane hakan."

Shiru Arab tayi tana tunani, ba tare da ta ce musu komai ba sai ma dena sauraron maganar nasu da tayi, gaba ɗaya ta lula duniyar tunanin abun da yakamata tayi

Ana haka sai ga Aliyu ya shigo, tamkar ba shi ba, kamar babu abun da ya dame shi, yana sanye da ƙananan kaya da suka fito mishi da tsantsan kyawun sa, sai dai rashin walwala da ke kan fuskarsa. Gaishe su yayi bayan ya samu wuri ya zauna ba tare da ya kalli ko ɗaya a cikin su ba bare ya san akwai Arab a wurin

Ita kuwa sai bin shi da kallo take yi a ranta tana cewa, "mugu azzalumi kawai, sai na rama abun da kayi min, bazan taɓa yafe maka ba, da ƙaton hancin sa sai ka ce na biri." Tayi ƙwafa tana ɗauke kanta, tare da ninyar tashi a wurin, domin a yanda take jin haushi da tsanar Aliyun kamar ta rufe shi da duka

Dady ne yace, "ta koma ta zauna su yi maganar a gabanta."

Hakan ne yasa ta dawo ta zauna

"Kai kuma, abun da ka aikata ba wai ka ci bulus bane, ban taɓa tunanin tarbiyyar da muka baka za ka iya watsi dashi haka ba, ka bamu kunya Aliyu, tunda haka ka zaɓa dole mu ɗauki mataki a nan take gudun sake jawo mana wani abun kunyar, auren ka da Humaira shi ne abun da zai faru."

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now