Saba'in da Biyar

113 11 2
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

        *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

            *P.W.A✍️*



*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    950
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  530
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼








_________________________

*BABI NA SABA'IN DA BIYAR*
_______________Change of life, it is easy for God to change your destiny, you don't know what will happen in your life except what God has written for you. Abun mamaki! Yau ga Arab a wani bigiri da ta kasa gane inda rayuwarta ta dosa, ta kasa gane me ke shirin faruwa a cikin rayuwarta, ga ta a gidan su, amma kuma tunaninta yana ga mutumin da ta rasa gane mene ne dalilin tuna sa a yanzu. Gaba ɗaya ta canza a kwanakin nan da ta dawo, duk wanda ya san Arab tabbas zai faɗa haka, sabida kwata-kwata bata da walwala babu farin ciki a tare da ita, tayi sanyin da ita kanta haƙiƙa mamakin kanta take yi, ƙunci da baƙin ciki ke ziyartan ta a kodayaushe, ta shiga wani yanayin da ta kasa bambance ainihin me ke mata ciwo a rayuwa

Already yanzu halin da take ciki ya gama taɓa mata walwalan ta, su kansu ƴan uwanta sun sha tambayarta a kan abun da ke damun ta tunda ta dawo, amma ta kasa faɗa musu ƙwaƙƙwaran dalili

Inna tana ganin kamar sabida mutuwar auren ta ne ya sauya ta a lokaci guda, shiyasa take faɗa mata, "ta manta komai ta dena saka damuwa a cikin ranta, zata samu wanda ya fi shi tunda ga Malik nan ya dawo wurin ta, don haka da zaran ta gama idda sai ta aure shi."

Bata san cewa kwata-kwata yanzu Arab ba ta son mu'amalar ta da kowa ba, kawai nacin Malik ɗin ne yasa take iya kula sa amma ba don da daɗin rai ba, a kullum yanayin da take shiga yana ƙara bunƙasa ne tunda ba ta da tunani a yanzu sai na Aliyu, tare da zama cikin ƙunci since a ganin ta sakin wulaƙanci yayi mata, shiyasa har take iya damuwa

Don yau ma tana zaune a ɗaki sai ga Zahra ta shigo, dayake su biyun ne a gidan. Ummu yanzu ta samu koyarwa a wata private school tana zuwa, ita kuma Inna ta fita, shiyasa Zahran take ta aiki ita kaɗai, Arab kuma na daki ta kwanta tayi shiru ta ƙi fitowa

Zahra na shiga ta ganta zaune a bakin gadon ta, sai ta nufe ta da mamaki ta zauna a gefen ta, take cewa, "ke lafiyar ki kike hawaye?"

"Hawaye kuma?" Arab ɗin itama ta furta tana kai hannayenta ta shafa fuskarta, ilai kuwa hawayen ta ji kwance male-male a face ɗin ta; wadda bata san ma tayi su ba

"Arab, wai me ke damun ki ne? Gaba ɗaya kin sauya tunda kika dawo, kin canza Arab ki faɗa mana me ke damun ki? Yau kuma har da hawaye haka kawai kina zaune? Ko dai kina ɓoye mana wani abu ne?"

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now