Babi na Goma sha ɗaya

121 10 0
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️*








_________________________

*BABI NA GOMA SHA ƊAYA*

_______________Wankan tayi ta fito ɗaure da towel da ta gani a rataye a toilet ɗin, sai dai tana fitowa idanuwanta suka faɗa kan gadon but babu Jakar kuɗin, tuni ya kwashe kayan shi ya adana, tsaki ta ja tsaban takaici, tana nan tsaye ta ji motsin shi zai shigo, sai tayi saurin nufan dressing mirror tana zama

Yana shigowa ya hange ta zaune, sai ya taho wajen ta; baki a washe yana cewa, "Baby ga abincin an kawo miki."

Murmushi tayi masa tana kallonsa da cewa, "ok bari in shirya sai in fito."

"No Baby kinga yanda kika yi kyau a haka? Wlh na rikice ba na jin zan iya jira har wani lokaci, a hannu nake babyna ki gane mana." Sai ya sa hannu ya ɗago ta yana haɗa ta da jikinsa, tare da kai mata sumba cikin ƙwarewa yana sake cewa, "mu je a haka ki ci abincin a hannu nake Baby, zan fi jin daɗin ganin ki a haka."

Murmushin yaƙe tayi tana kawar da kai sabida yanda taga yana lashe ta kamar maye, da alamu mayen ne wannan bazai ɗaga mata ƙafa ba, a ranta tace, "banza kawai, mutum ko fasali." But babu yanda ta iya haka ta bi shi a haka suka wuce Falo

A saman cinyoyinsa ya ajiye ta; ya hana ta yin komai sai shi da kansa yake mata, abincin ma a baki ya bata sai shafa ta yake yi kamar zai cinye ta. Tun daga wajen wasan ya soma canzawa

Ita kanta Arab sakin jiki tayi sosai ta jiyar dashi daɗi, ai kuwa ta sha ihu sosai, sai sambatu yake mata, tun tana jin daɗin abun har ta gaji tsaban ya ƙi ƙyale ta, ga shi yayi mata girma da yawa, sai can da dare ya tsala sannan ya haƙura da ita, daga nan barci ya ɗauke shi kamar kasa. Tsaki kawai ta ja ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka don baza ta iya zama da najasa a haka ba, alwala tayi ta rama sallolin da ake bin ta sannan ta soma neman inda zata samu kuɗin shi, ta tabbata idan ta gani sai dai ya neme ta a daren ya rasa guduwa zata yi, but duk neman da tayi bata samu damar gani ba, da alamu ya rufe su a cikin drower ne kuma ya ɓoye keys ɗin. Duk ta duba bata samu ba dole ta koma ta kwanta

Da asuba ya sake damun ta sai da suka ƙara yi, ta gane Mutumin shegen maye ne ba ya gajiya ko kwana zasu yi, duk da itama ɗin ƙwaruwa ce a harkan amma sam shi Mutumin ne bai yi mata ba, ga shegen girma da yake dashi da nauyi, shiyasa duk ya dame ta, amma haka nan ta haƙura take biye mishi suna shan Love; sabida ko a ranan sai da ya tura mata 100k a account. Sai murna take yi kamar zata haɗiye shi don daɗi

Shi kuwa murmushi yayi yace, "ai wannan ma kaɗan ne Baby in har za ki kasance dani a duk sanda nake so, ban taɓa jin daɗin Mace kamar yanda nake jin ki ba Baby, gaskiya ke ta musamman ce, zan so mu kasance a ko yaushe domin zumar ki yana ruɗa Ni, ba ki da matsala da kuɗi Baby ko nawa ne zan kashe miki."

Daɗi ne ya ratsa ta, sai ta sake shigewa jikinsa cike da kissa tace, "nagode Yallaɓoi, gaskiya naji daɗin samun ka nima Alhaji, Ni bani da damuwa idan har zaka sakar min kuɗi ko meye zan yi maka, bazan taɓa guje maka ba, ka saka a ranka Ni Arab taka ce sai yanda kayi dani ya Alhajjjj." Sai ta ja sunan kamar ta sha yaji tana kai harshenta saman bakinsa ta soma lashewa har zuwa saman hancin sa, inda tafukan hannun ta ke tallabe da fuskar tashi; tana mishi salo da zara-zaran ƙumbunan ta

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now