🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼♀️*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA ARBA'IN DA ƊAYA*
_______________A sanda suka zo sun tarar da Ummu a lokacin sosai ta cakwume shi, kuma yayi-yayi ta sake shi but ta ƙi, sai rantse-rantse take yi, "wlh sai ya mayar da ita gidan su, sai ya sake ta."Jama'ar gidan fa hankalin su ya soma tashi, duba da yanda basu san me ke faruwa ba, shiyasa aka yi kiran Baban su Anwar ɗin tunda shi ne babba; saboda duk yanda suka so Ummu ta sake shi ta ƙi, suna ta bata haƙuri amma furr ta ƙi sauraron su, sai kuka take yi tana zagin shi
Babansu da ya zo; shi ya tambayi Anwar ɗin da cewa, "mai yayi mata haka?"
Yace, "wlh Baba babu abun da nayi mata."
"Babu abun da kayi mata ne take maka wannan cin kashin? Ka sanar dani ba na son iskanci ka ji ko?"
Kame-kame ya soma yi don ya kasa faɗan amsa ƙwaƙƙwara
Baban ya kalle ta yace, "ke sanar min mai yayi miki?"
Ba tare da ta sake shi ba ta soma rattafo mishi komai na yaudaran da yayi mata wajen auren ta
Da yawan mutanen wurin salati suke rattafa wa tunda ba haka Anwar ɗin ya sanar musu ba
"Shikenan sake shi, ai abun ma baza ta kai ga haka ba, ki kwantar da hankalinki zan ɗauki mataki a kansa, tunda har ba kya son zama dashi duk abun da kika yanke shi za a aiwatar."
"Amma Baba..."
"Yi min shiru mutumin banza kawai." Baban ya tari numfashinsa cikin tsananin ɓacin rai, "ba dai mu za ka zubar wa da mutunci ba? Ban san haka kake ba Anwaru sai yanzu da ka nuna halin ka. Ka san girman aure da har za ka yi wasa dashi? Ka je ka auro yarinyar mutane ba tare da ka sanar mata ainihin ko kai waye ba saboda tsantsan yaudara irin naka? to abinda yarinya ta yanke dole shi za ka bi, ke kuma ki yi haƙuri zuwa gobe sai a san abun yi."
Jin hakan tuni Ummu ta janye hannunta daga jikin Anwar ɗin tana share hawayen ta, ko sauraron su bata yi ba ta shige ɗakin ta bar su nan
Su ma kowa sai ya watse yayinda Baban nasu ya kira Anwar ɗin suka wuce a tare
Bai jima ba kuma sai ga shi ya dawo cikin ɗakin, fushi ne sosai a kan fuskarsa
Sai dai ko kallo bai ishi Ummu ba, tunda tayi mishi kallo ɗaya ta ɗauke kai
Shi kuma ya kalle ta murya a kausashe yace, "ba dai Ni kika yi wa wannan tozarcin ba? Kin manta da duk soyayyar da kike min kika kunyata Ni a gaban ƴan uwana, ashe dama ba ƙaunata kike yi ba ke ma duk tsaban yaudara ce tunda har baza ki iya zama da Ni ba? To shikenan mu zuba dani da ke wlh idan har Ni ne zan sake ki sai dai ki dauwama da aure na, duk inda kika je za ki dawo dole za ki dawo gare Ni baza ki taɓa auren wani ba face Ni."
Maimakon maganarsa ta bata haushi sai dariya, ta bushe da dariya tana kallonsa cike da nishaɗi, sai tace, "uhm a banza dai, duk ihun da kake yi da haushin karnukan naka a banza ne, saki dai sai ka sake Ni, wlh tallahi Ni Ummu Kulsum bazan taɓa zama da kai ba koda sonka zai kashe Ni ne, ina Ni ina wahala? Ka rasa ma inda za ka kawo Ni sai daji? Don bani da hankali saboda soyayya na kashe kaina, ai ka makaro tunda ka yaudare Ni da ƙarairayi; to, ka kashe auren ka, bazan taɓa zama da ɗan ƙauye ba domin na fi ƙarfin ka."
YOU ARE READING
RUƊIN DUNIYA!
RomanceThe lives of some sisters. Haƙiƙa Ina matuƙar son kuɗi, ji nake yi idan babu su kamar bazan iya rayuwa ba, ɗaukar da nayi musu su ne suke kare mutunci, sannan kuma su ne suke sa wa a yi maka soyayya, ashe ba haka ba... Tabbas kuskure. nayi su da dam...