Talatin da shida

97 7 1
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*








_________________________

*BABI NA TALATIN DA SHIDA*
_______________ *ABUJA STATE*
                Maganganun Doctor Aliyu gaba ɗaya sun hautsina ma Malik zuciya da gangar jiki, kuka ne kawai bai yi ba a lokacin nan amma gaba ɗaya ya gama sauya wa, idanun nan sun yi ja ko magana ya kasa yi

Shi kuwa Aliyu ko a jikinsa, tunda ya gama sanar mishi ya ɗauki waya ya soma latsa wa yana kara wa a kunne

Hakan ne yasa Doctor Mamman ya soma ba wa Malik haƙuri yana nuna masa yarda da ƙaddara

Numfashi ya ja tare da cewa, "ba komai, haka Allah ya so, please ara min wayanka in kira gida saboda basu sani ba."

Ciro wayan yayi ya miƙa masa, sannan ya mayar da hankalinsa a kan Aliyu ganin ya gama wayan yake cewa, "Doctor yanzu babu wani taimako da za a yi sai an juya mahaifar nata?"

"To wanne taimako kenan kake nufi? Since ita ta ja ma kanta ba wani ba, mutanen da suke ɗaukar ciki ba sa ƙaunar su haife sai su bi hanyar saɓa wa Allan su suna zubar wa, don Allah ya kama su ta wani fannin ai ba laifi bane, domin wata rana da kansu suna buƙatar haihuwar amma babu hali, sai hakuri." Ya ƙare maganar yana juyawa a kan kujeran da yake kai batare da damuwa ko kaɗan a kan maganar da yayi ba, in fact ma brown eyes ɗin sa masu ɗaukar hankali suna a kan Malik

Wanda shima ya ɗago ya kafa mishi nasa idon, sai dai a ransa kai kawo maganar Aliyun yake masa yana jin tamkar ya san abun da suka aikata ne

Shi kansa Doctor Mamman shiru yayi ya kasa magana saboda jin abun da ya faɗa, ya san halin Abokinsa zai iya yin ma fiye da haka kasancewar sa Mutum da ba ya ɓoye abun da ke ransa, kuma ba shi da tsoro a lamurran sa

Sai shi Aliyun ne yayi magana saboda jin sun yi shiru kamar ruwa ya ɗauke su, sai yace, "ka san dai ina da ƙarancin lokaci a yanzu zan bar ƙasar." Ya ɗago hannunsa yana duban time

While Malik kuma sai ya miƙe saboda peacking ɗin da Abba yayi na kiran da yayi masa, hakan ne yasa ya nufi ƙofa yana mishi magana

"So if he agrees, the work will be done for her, then we can start now before I leave." Aliyu ya sake maganar batare da ya kalli inda Malik yake ba, idanunsa a kan Doctor Mamman

Doctor Mamman yace, "ok bari ya gama wayan sai muyi maganar. Ina zuwa." Ya miƙe yana bin bayan Malik da yanzu ya fice a office ɗin.



                Bayan kamar mintuna Talatin; lokacin gaba ɗaya ƴan uwa sun zo asibitin, daga iyayen Nawwara har iyayen Malik, hankalin su gaba ɗaya a tashe da jin abun da ke faruwa, kowa yayi zugum cike da alhini a ransa

While su Doctor Aliyu suna ciki suna yi wa Nawwara aiki; wanda ya ɗauke su tsawon mintoci a ƙalla arba'in, kuma suna fitowa Doctor Aliyu ya bar asibitin ko ƙara minti biyar bai yi ba, kasancewar lokacin tashin jirgin su zuwa Germany yayi, zai kai mahaifinsa a kan rashin lafiyan da yake fama da shi; wanda duk bayan wasu lokuta suna komawa can ana duba sa

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now