🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA ASHIRIN*
_______________Koda ta isa wurin motan sai da ta gama zagaye ta har tana leƙe-leƙe, sai dai ba ta ganin kowa sai na ciki ne zai gantaTana cikin dube-duben ne wani matashin saurayi ya fito daga ciki yana murmusawa tare da yin mata sallama
Ta amsa tana kallonsa tare da ƙare masa kallo, "lafiya Malam? Kai ne kake kira na?" Ta furta da mamaki sabida ganin yanayin saurayin kuma a cikin wannan motan, wacce a ƙiyasinta duk da bata gama sanin ire-iren waɗannan tsadaddun motocin ba; amma tabbas wannan zata iya kai wa miliyan takwas ko goma
Saurayin ne ya sake magana sabida ganin tayi shiru hankalin ta ma ba ya wajen sa
Hakan ne yasa ta ɗan yi firgigit tana ɗan waro kyawawan idanuwanta a kansa, tare da ƙirƙiro wannan Shegiyar murmushin nata tana cewa, "ina jin ka Malam, mai kace ne?"
Murmushi yayi yace, "ba suna na Malam ba, suna na Ahmad, kuma Ni ɗan saƙo ne wajen ki, aiko Ni aka yi."
"To fa. Wane ne ya aiko ka?" Tayi maganar tana ɗan gyara tsayuwar ta, tare da ƙara kafa mishi idanuwanta ko ƙyafta su ba ta yi
"Kar ki damu za ki sanshi ai, sai dai shi bai bani damar bayyana miki kansa ba, abun da ya aiko Ni kawai na zo yi, shi uban gidana ne shi ne yace in kawo miki wannan." Sai ya buɗe motan ya ɗauko wata ƙatuwar jaka ja mai kyau da burgewa a ido, ya zagayo yana miƙa mata
Ta saka hannu ta amsa tana bin Jakar da kallo, kana kuma ta mayar da kallonta gare shi
While shima idanuwansa a kanta yana cewa, "wannan shi ne saƙon, sannan akwai waya a ciki idan kika kunna za ku iya magana a ciki don zai kira ki." Sai ya miƙa mata key ɗin mota ya ƙara da faɗin, "sannan wannan ma shi yace in ba ki, motan nan taki ce."
"Ban gane ba?" Ta furta tana zare idanu tare da shiga ruɗu da jin zancen nasa
Murmushi yayi shi kuma yace, "kar ki damu za ki gane ai, Ni dai abun da aka ce in Yi kenan, kuma na aiwatar da aiki na, Ni zan tafi sai kuma wani lokacin."
Da kallo ta bi shi har ya juya ya wuce a ƙafa, ta kasa motsawa sabida mamakin da ya cika ta tare da tunanin waye wannan? Wane ne ya aiko sa? Amma kuma tuna furucin sa na ƙarshe da cewa motan nan nata ne; tuni fuskarta ta sauya nan da nan ta washe baki ta soma zagaye motan tana shafawa, cikin wani irin farin cikin da ya tabaibaye ta har jikinta rawa yake yi ta juya gida da gudu. Tana shiga gidan ta soma kwaɗawa Zahra kira
Zahra da ke wurin inda ta bar ta tana shan waƙa, sai tayi saurin zare earpis ɗin da ta sanya saboda yanda taga ta sukwano wajenta a guje. "Lafiya mene ne?"
Arab ta kasa ma magana sabida yanda bakin ta ya ƙi rufuwa tsaban daɗi, sai yarfa hannu take yi tana son yin magana but ta gaza. Daƙyar ta natsu ta furta, "wlh na yi kamu.. na yi goshi.. na yi kasuwa ne ina tunani."
"Faɗa min mana me ya faru ne don Allah? Kin saka Ni a cakwakiya." Zahra itama ta furta cikin zumuɗi da son sanin abun da ya faru
"Mota... Mota... Mota ce wani ya kawo min Alkur'an, kin ganta ne kuwa? Wayyo Allana! Daɗi zai kashe Ni wlh." Tayi maganar cikin tsantsan farin ciki tare da tura mata Jakar tana cewa, "kinga har da wannan ya bani." Sai kuma ta soma ƙoƙarin buɗewa
YOU ARE READING
RUƊIN DUNIYA!
RomanceThe lives of some sisters. Haƙiƙa Ina matuƙar son kuɗi, ji nake yi idan babu su kamar bazan iya rayuwa ba, ɗaukar da nayi musu su ne suke kare mutunci, sannan kuma su ne suke sa wa a yi maka soyayya, ashe ba haka ba... Tabbas kuskure. nayi su da dam...