Arba'in

116 8 0
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

_Don Allah ina matuƙar buƙatar addu'ar ku saboda abun da ke faruwa dani, don Allah don Allah ku taya Ni da addu'a Allah ya yaye min damuwa ta; da duk wanda ke cikin ta.👏👏_








_________________________

*BABI NA ARBA'IN*
_______________Tana fita ta hangi wata budurwa wacce baza ta wuce sa'ar Arab ɗin su ba, tana zaune a kan sofa; gefe ɗaya kuma ƙaton trolley ne ajiye a wurin, tana sanye da wani jan less da aka yi mata ado da milk color, kayan sun amshe ta duk da ba fara bace, irin Choco color ɗin nan ne skin ɗin ta, kuma kyakkyawa ce ga manyan idanu da take dasu farare sol, su kaɗai ne abun da zasu fi ɗaukar hankalin Mutum idan ya kalle ta saboda kyawun su da tsananin hasken su, fuskarta babu MakeUp tana sanye da milk color ɗin gyale da ta yafa a kan kafaɗunta, haka ma takalmanta da ƙaramar jakarta duk milk ne

Tunda Zahra ta fito take bin ta da kallo, sai tayi turus a wajen saboda ko ba a faɗa mata ba ta san ita ce Juwairiyyan da yace

Ilai kuwa budurwan ta ɗan yi murmushi cike da kisisina da yanga tace, "sannu Aunty."

Kamar baza ta amsa ba Zahran sai kuma tace, "yauwa." Tana ci gaba da bin ta da kallo ba tare da ta saki fuskarta ba

Itama Juwairiyyan ganin haka ne yasa ta ɗan janye murmushin nata before tace, "Allah yasa Yayana yana nan?"

"Waye kuma Yayan ki? Ya za a yi ki shigo min gida ba tare da kin yi min bayanin kanki ba amma kike tambayar wani Yayanki?"

"To ai naga shi mai gidan ya san da zuwana, and ba na tunanin bai sanar miki ba ke ma." Tayi maganar tana yatsina fuska cike da iyayi wanda da alamu ta saba

Ai kuwa Zahra sai ta nufi wurin ta tana cewa, "Nan gidana ne yarinya baza ki zo ki ce za ki yi min cin kashi ba, bazan ɗauka ba, tashi ki bar min gida tunda baza ki yi bayani da bakin ki ba, idan ya zo shi wanda kika zo don shi sai ya shigo da ke, but now ba na son ganin ki."

"Ai kuwa babu inda zan je wlh, nan gidan Yayana ne kamar yanda kike da iko dashi haka nima nake dashi."

"Oh! Kina so ki nuna min kin isa ki ja da Ni kenan? To mu zuba tunda kin ce kina da iko da gidan." Tayi maganar riƙe da ƙugu ranta a mugun ɓace, dama da cikin Haidar ɗin take, shiyasa yanzu take son juye wa a kanta

Itama tuni ta tashi tsaye saboda ganin yanda Zahran ta tsaya mata a kai kamar zata faɗo mata, sai dai bata yi magana ba ta ja jiki zata koma wani kujeran

Itama Zahran bata ce mata uffan ba ta ɗauki trolley ɗin ta tayi waje dashi

Da sauri Juwairiyya ta bi ta tana ce mata, "ina za ki je min da jaka?"

A waje ta ajiye mata tare da juyawa ta shiga ciki, tana ganin Juwairiyyan ta nufi wurin trolley ɗin sai ta garƙame ƙofan ta; bata sake bi ta kanta ba

"Lallai kam wannan Matar." Ta furta itama cikin baƙin cikin abun da tayi mata, har da cije yatsa, sai kuma ta ciro wayanta a jaka ta kira numban Haidar

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now