"Ban gane ba Nafi me kike nufi da ta haqura da binsa ko baki gane halin da yarinyar nan take ciki bane, yarinya na buqatar mijinta a kusa idan kuma ba halaka ake so ta fada ba se naji, nifa dama na gane take takenki kina so ki fifita bare akan yar uwarki ko Nafi. Kuma da kike zancen za'a shiga haqqin Asma'u ita Amirar daba uwace ta haifeta ba ai ba'a shiga nata haqqin bako" Adda Fatu ta fada cike da jin haushin Dada, se Dadar ta gyara zama tareda cewa
"Ni ba haka nake nufi ba amma gani nayi ai tun farko tare suke a can, yanzu ko cewa akayi suringa yi idan wannan ta je ta kwana biyu se wannan taje kinga bame yiwuwa bane tunda Asma'u tana aiki a garin bakuma ze yuwu muce tabar aikin ta ba tunda idan Amira ce a matsayinta muma bazamu bari a mata ba ko?
Ni dai a nawa ganin Adda ayi haqurin shi yafi a zauna lafiya tunda har komai ya daidaita tsakaninsu bana son wata rigima ta sake tasowa kindai san sharadin da Malam ya kafa mun dan Allah bana so ya sake ganin laifina akan lamarin gidan Bashir".
Se Adda Fatu ta miqe nan da nan ta fara sababi da fadan maganganu ta inda take shiga bata nan take fita ba, ga baqin cikin rashin samun biyan buqata a gurin Bashir gashi da Alamu wannan Karon Nafi na nema ta bata matsala amma ina bazata sabu ba wallahi dole tasan abinyi. Miqewa tayi still tana masifar ta nifi qofa,
"Wato Nafi kina ganin yanzu kinkai matsayin da zaki qalubalance ni ko? Kin manta duk halaccin da nayi miki a rayuwa saboda qasa ta dade da cinye Naman Baffa da Inna dole ki watsar da maganar su tunda kina ganin yanzu kema Kin kawo qarfi. Na gode zan kuma tafi amma daga yau kisa a ranki baki da sauran wata yar uwa data rage miki a duniya tunda kin zabi Matar danki akaina da Yata shikenan Nafi na yafewa Duniya ke" ta qarasa tana rushewa Kukan munafunci wanda dashi take cin galaba akan Nafin.
Ta kuwa samu yanda take so dan nan da nan hankalin Dada ya tashi ta shiga son nuna mata ita fa ba abinda take nufi ba kenan,
"Idan har da gaske kike kuma kina so na haqura nida kawai kiyi yanda zakiyi Bashir ya dauki Amira ta koma kusa dashi, kuma baze yuwu yace Ze kwashe su su dukka ya kai can ba se dai ki saka shi ya dawo da daya ya dauki daya idan kikayi haka shine kadai Ze sa na haqura in ba haka ba wallahi ki saka a ranki baki da wata Yar uwa Fatu a raye"Ita dai Dada son su rabu lafiya ya saka ta amince mata, dole ta hado yan kudaden hannunta dubu 30 ta bata tace gashi nan ta kaiwa Amirar ta riqe kafin Bashir din yazo se a san yanda zaayi haka ta rakata har get Addan na sake jadda da mata fa akan tana nan tana jiran saka mako da haka suka rabu.
Numfashi ta sauke bayan ta dawo cikin palour ta tazauna, gaba daya ta tasa ina zata kama akan wannan al'amarin. Har ga Allah bata so ta sake yin wani kuskuren akan na baya amma ya zatayi da Adda Fatu yar uwarta tilo a kaf fadin duniyar nan bata da kamarta. Addan tayi mata komai a rayuwa ya kamata ace ita ma ta saka mata da abinda ta mata. A zatonta Auran Bashir da Amira ya isa ga tukuicin kyautatawar amma se yanzu take dana sanin ma aikata hakan domin kamar ta bude wata qofa ce da Addan ta mayar da ita tamkar birin wasanta.
Ko da yaushe cikin daga mata hankali take tunda akayi wannan auran da ita dai bata ga amfaninsa ba in banda bacin rayuka da ya janyo da yawa, shigowar Nazir Autan ta ya sakata dagowa ta kalle shi
"Yanzu na hadu da fitinanniyar yayar ki a hanya seda tayi mun fashin 10k wallahi, gaskiya Dada ki ringa yiwa Adda fada abubuwan da takeyi basa dacewa. A yanzun fa ga kudi a hannunta amma ta tsaya suna fada da Dan Napep dan yace a 200 ze kaita gida""Hmm Allah ya rufa asiri kawai Naziru amma ni lamarin Adda ya fara bani tsoro, yanzu ma fa kaji abinda ya kawo ta" tiryan tiryan ta labarta masa yanda sukayi.
"Wallahi Dada ki kiyayi matar nan, ni dai ina ga Asiri take yi miki ma kike wasu abubuwan idan ba haka ba dan ta riqe ki ai ba baiwarta bace ke da kuma zata ringa juya ki yanda taso. Tun farko abinda muka guda a hadin wannan auran kenan amma kika rufe ido kika ce se anyi zumunchin ku ya qara qarfi ko ai gashi tun ba'aje ko ina ba kinzo kina dana sani. Shima Yayan banga qaddarar daya gani a jikin wannan mara mutunchin yarinyar ba daya yarda ya aure ta"
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.