To Aka ce mata da Miji se Allah dan kuwa Ma'u da Basharin ta suna qulewa a daki sukai muqus aka shiga sharafin soyayya dan dama an dade ba'a hadu ba qarshe har makara tashi bacci sukayi. Safiyar ranar duk su biyun da ka kallesu zaka san suna cikin walwala.
Ta cancada kwalliyarta da skirt and blouse na Atamfa komai ya fito se juyi take tana saka kwakwalwar Bashir jijjiga. haka ta hada musu breakfast me rai da lafiya suka ci suka wuce makaranta dukda sam be so yau ta zama ranar aiki ba ya so ace suna gida yau yaci duniyar sa da tsinke ya more amma ba komai ai Gobe Friday zasu hadu.
Suna fita Qarasa yan abubuwan da suka rage mata tayi kafin ta shiga dakin ta ta kwanta dan huce gajiyar da Bashir ya tara mata, "Bashir is too good" ta ayyana aranta. Wato yasan ta yanda duk ze wanke laifinsa ta wannan fanni gwanin malami neda ta tabbatar samun irinsa se an tona.
Tana tsaka da tunanin shauqin daren jiyan ta jiyo qarar door bell da kuma ringing din wayarta. Wayar ta fara jawowa ta duba, Anty ce matar ogan Bashir dake Flat din da yake kallon nasu, seta miqe tareda daukan Qaramin mayafi dan dankwalin kanta ya zame.
A palour suka zube tare da Anty da ta farayiwa Asma'un tsiya tun daga qofa"
"Kai Ma'u kinga wani kyallin goshi da kike daga fitowa daga Asibiti har za'a maida wani kenan". Daria Asma'u tayi tana cewa
"Haba dai ai na gama nikam wadan nan ma sun isa Allah ya raya mana sisi na kwai zan ci gaba dayi"
"Inafa kika gama kedai ki shirya dan qila wasu biyun ne a tafe"
"Ba amin ba Anty" ta tare Antyn.
Gaisawa sukayi kafin Antyn tace mata"Shekaran jiya na dawo wlh se dare ma nashigo Honey yake cemun Ai kina Asibiti ba lafiya, har zamu zo jiya da magriba kuma yace sun hadu da Baban Aliyu a Masallaci ya ce masa kin dawo gida"
"Eh wallahi jiya da rana aka sallamoni ai gaskiya Anty kinsha gida kusan 3 weeks fa" Asma'u ta fada.
"Ki bari kedai zama nayi na huta nayi gyara sosai dan anan ba wani lokaci kake samu ka baje yanda kake so ba mutum na saka maka ido" cewar Anty tana bawa Asma'u hannu suka kashe
"Kai Anty a ringa tausayin Baba na dai karki qarasa mana tsohon mu"
"Ke barni fa dole na kwaci kaina sarai kin san Uwargida na bata wasa da gyara dole nima na zage kar a raina ni.
Hira suka shigayi Anty ta shiga fito da abubuwan da tayo wa Asma'u tsaraba tana cewa "Gashinan se a ci gaba da gashi ban ce ki raga masa ko na second daya ba atoh" suka tuntsure da dariya Asma'u tana cewa "Anty baki da dama". Se wurin 12 sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta rakata qofa ta dawo tana tattare kayan zuwa dakinta a ranta tana qara jin qaunar Antyn dan yanda ta dauketa take kula da ita kamar qanwarta da suka fito ciki daya.
Anty Suwaiba matar Engineer Abdullahi Gusau ce ogan Bashir.
Itace Matar sa ta biyu uwar gidan ta ma anan Lagos take da zama amma ba unguwarsu daya ba. Mace ce me tsananin kirki dukda ta dan girmi Asma'u amma yanda take mu'amalantarta kaman qawaye ko shaqiqan yaya da qanwa suke dan tunda suka fara haduwa jinin su ya hadu da Asma'un.Ita kanta Asma'u tana ji da Antyn dan Ita tunda suka hadu rabon da tace ta siyi wani abun gyara da kudinta, a koda yaushe Anty cikin yo musu aike kaya gangariya daga Zamfara garinsu take kuma duk sanda Asma'u ta tambayeta nawane ta biya seta nuna bacin ranta. Ta kance da Asma'un
"Ni a qanwa na dauke ki, banida kowa a Lagos seke yanzu".Wasu daga cikin kayan ta fitar ta fara amfani dasu a ranta tana hasaso haduwarsu da Malam Bash dan tasan yau kam se tafi jiya Armashi. Kafin ta gama an kira sallar Azahar dan haka tayi alwala tayi sallar sannan ta kwanta zuwa La'asar kafin tasan abinda zata dafa musu kuma.
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.