DANDANO DAGA LITTAFIN *MATAR MUTUM*
Mallakar Maryam Farouk (Ummu-Maheer)
Marubuciyar
1-RUBUTACCIYAR QADDARAH
2-WATA KISHIYAR
3-HALIN KISHI AND NOW
4-MATAR MUTUMA qarqashin qungiyar FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
Shiru falon ya dauka banda qarar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare daya, seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar ba wai ita ta assasa yin taron ba dan qaddamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta miqe tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai qasa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taba haka?
"Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kudi kamar barawo?" Hajiya Bintan ta fada, Momy ta dago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jibanci gudan jinin nata da ita wai Barawo,ita kuwa Hajiya bata dakata ba fusace taci gaba da cewa
"Wallahi tallahi ko sama da qasa zata hade banga uban daya isa ya qulla auran nan ba yar Bakanike Amadu? Mu zamu hada surukuta da Yar Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba, iyakar irin tsiyar da aka dakko mana sun isa BA's an hado mana da wanda zasu zo suna mana dauki daidai suna ciyayya ba"
"Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma'auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun qi da ze saka a hana shi auranta ba" Alhaji Audu dake kishingide kan kujera ya fada. Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani danta tace
"Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman"
Mamaki kamar ya shaqesu jin abinda Hajiyar ta fada masa, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze dauka amma sukaji muqus sema Hajiya data ci gaba da sababi tana cewa"Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka kuma Mayya".
"Amma Hajiya talauci baya cikin sharuddan da suke hana aure, sannan maita da kike jifanta da ita kinsan cewar ba qaramin abu bane idan sukaji zasu iya yin qararki akan hakan" tsautsayi ya saka Anty Amarya magana tamkar kuwa Hajiyan na jiranta daman tace
"Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu qarin yar uwa ko Ahalul fuqara'u za'a qara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tartibiyar sa'ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa qaya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta fadi daka fita ka bashi kudin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya qare yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi dan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar tasa ta zarce misali ashe da walakin yaje an zarge kurwa tab" Hajiya Binta ta fada tana tsaida idonta akan Alhaji
Baqin cikin maganganunta suka saina Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru goma sha tara kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake qara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar qoqari yanayi cikin su uku ita kadaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kudin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar dabi'arsa ta yawon maula gidajen Masu kudi anci sa'a ya dena amma fa kullum yana take gidan Alhaji Audu, sabulun wanka wannan se yazo ya roqa an bashi.
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.