Parta 64

2.4K 208 29
                                    

BAYAN WATA UKU

"Wallahi nagaji, ka gayamun kawai SH idan so kake na mutu kawai ka huta amma wannan jan ran ya isa" na fada dakyar saboda yanda nake jina kamar wadda take yawo a gajimare.

"Ki mutu fa kika ce ni kuma in zauna dawa?" Ya fada da saurin sa,

"Ka zauna da baqin halin ka irin na yan Bauchi mana ai naga alamar abinda kake jira kenan safiya tayi ace maka Asma'u ta mutu"

Wata muguwar dariya ya sheqe da ita dukda nasan shi kansa qarfin hali kawai yake dakiyar zuciya ce kawai irin ta yan maza amma nasan ya fini a zabtuwa da kewa yace

"Da wuri haka haba Asmy karki bawa mata kunya mana, wata uku fa kacal kike cewa kin gaji dame kika gaji toh?" Ya yi tambayar cikin sigar zolaya yana dage mun gira daya.

Baki na zumbura gaba kamar yarinya na kwabe fuska ina harar screen din wayar nace
"Wallahi nasan Asiri kawai kayi mun amma ta yaya yaushe ma ni na fara sonka haka da har nake jin kamar zan zauce saboda ban ganka ba"

Wannan karon ina kallonsa tsabar dariya seda ya fado daga kan kujerar da yake zaune wayar ta kife a qasa, iya quluwa na qulu banyi aune ba sejin hawaye kawai nayi suna diga daga idona dan wallahi kamar wadda aka kunnawa wuta a zuciya haka nakeyin wani irin so da kewar Yusuf suna qonani. Idan za'a saka mun bindiga bazance ga sanda hakan ya fara ba abu daya kawai dana sani A cikin watanni ukun nan  Yusuf yayi nasarar yin rugu rugu daduk wani qashi da tsoka da suke a cikin jikina.

"Haba mana Asmy kuka kuma ki bari dan Allah bana so" ya fada a rikice kamar ze fito daga cikin wayar. Sena qarawa kukan shagwabar tawa qaimi ina cewa

"To ba kaine ba saboda kaga na damu dakai shine na zama abin tsokanar ka kake mun dariya, ai Allah yana kallonka wallahi kuma nima duk ranar muka hadu sena rama duk irin abinda kayi mun".

"Me zaki rama bayan duk wanda kikayi mun Asmy, wata na uku ba da zama ango amma nida qaton gwauro bamu da maraba saboda tsabar mugunta fa korata kikayi kika ce karba sake zuwa inda kike ya kike so nayi? Ina son ki da yawan da zan iya miki duk abinda kike so koda ace ni bazan ji dadi ba indai ke zakiyi farin ciki burina ya cika" ya fada cikin sanyi da taushin muryar da ya yaqi duk wani burnishin taurin kai daya rage mun"

"Nace kayi haquri lokacin ina cikin jin haushin an mun auran dole ne kamar wata wadda ba'a so daga zuwa tambaya kawai aka daura mun aure" na fada cikin shagwaba yanda kasan wata Sweet sixteen, koda yake idan ina tareda Yusuf, yanda yake shagwabani yana riritani jina nake kamar jaririyar da aka haifa yanzu baje kolina nake ina barje shagwaba yanda raina yake so.

"Ni daman baki mun laifi ba, kuma haryanzu kece baki so dana zo inda kike ba tunda baki bani dama ba"

"Ni wallahi naqi jinin wannan halin ayiwa mutum abu yace ba'a masa ba amma kuma yabi ta qarqashin qasa yayiya gallazawa mutane, indai da gaske banyi maka laifi ba ko ka haqura kusan wata yara kenan fa ina baka haqurin nan amma kaqi kazo kullum kuma kace kai banyi maka komai ba" na fada cikin shashsheqa kamar wadda take kukan gaske.

Seda ya dauke wuta na dan lokacin, yana yin kallon da yakeyi mun kansa ya canza kafin qasa qasa yace mun

"Ki bari karki jawo mun kuma ki rasa yanda zakiyi dani, kuma yaushe kikayi wata goma kina bani haquri banda qarya fa Asmy"

"Mugu aini ka iya saka ni a ukun ka barni da jiyi akan gado ai" na ayyana a zuciyata a fili kuwa nace

"Toh ai ni duk wata daya ba tareda kai ba a matsayin wata uku yake, kasan kuwa yanda nake rayuwa a nan? Ikon Allah ne kawai yake riqe dani amma qila da tuni an dade dayinsadakar arba'in dina"

"Asmyyyyy" yaja sunan seda tsigar jikina gaba daya suka miqe kafin yaci gaba da cewa
"Asmy baki so ki ganni ba, kawai fada kike amma ba dagaske kike ba"

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now