Part 22

1.3K 102 3
                                    

Gudu ya ringa fellawa dasu kamar masu barin gari sanda ya tsayar da motar a bakin Get kuwa har qauri takeyi, a Get din ya watsar dasu yai gaba dan Amirah bata ko samu damar daukar Akwatinta ba Asma'u ta saka key din hannunta ta bude musu Get suka shiga.

Yanda taga Amiran tana tafe tana layi se ta bata tausayi dan haka ta qarasa ta riqo kafadarta ai kamar me jiran majingini kawai ta fashe mata da kuka tana cewa"Dan Allah Anty ki bashi haquri, wallahi ba laifina bane Addah ce kema kin santa ita tace se anyi".

Asma'u bata tanka ta ba har suka shiga dakin Amiran ta zaunar da ita akan Kujera tana qarewa palour kallo baki bude saboda mamaki. Duk wani abu daya danganci glass an fasa harda Tv ba'a barta ba daidai da labulaye duk duk an sauke su qarafunan sun karyo.

Ajiyar zuciya tayi kafin ta Kalli Amirah da har sannan kukan take tace "Kiyi shiru komai zai daidaita Insha Allah, ina zuwa".

Part dinta ta koma, Farfesun Tsokar rago ta ciro a freezer ta dumama kafin ta hada Shayi a qaton Mug ta dora su a kan Try hade da Bread ta dauka ta koma part din Amiran. Bayan ta ajiye su ta sake komawa ta debo mata tuwon semo da miyar danyar kubewa da tayiwa Bashir bema ci ba ta sake komawa part din Amiran.

Tana zaune a qasa ta zamo daga kan kujerar riqe da cikinta tana murqususu, da sauri Asma'u ta ajiye try din ta nufeta tana "lafiya Amirah meya same ki?" Ita dai se juyi take tana malele
kuwa akan Tiles saboda bala'in qullewar da cikin yayi mata.

Dakyar ta nutsu ta kamata ta koma kan kujerar, Shayin ta fara bata a baki tana karba, kurba uku tayi Amai ya taso mata ko kafin ta miqe tayi shi a Gurin Asma'u na tsaye se sannu take mata. Bowl babba ta dakko ta debo ruwa a babban kofi da dawo gurin Amiran, ta zuba mata ta kurkure baki da dauraye fuskarta Ta koma yaraf ta kwanta tana sauke Numfashi.

Abincin ta ajiye mata nan ta shiga ci kuwa dan Aman ya taimaka ya bude mata ciki ita kuma ta dauke robar ta tafi dakko mopper da packer, Duk Kyankyami irin na Asma'u haka ta daure ta kwashe aman tsaf ta zuba ruwan omo ta goge Gurin kafin ta sake saka ruwa ta goge tas ta nemi freshener amma bata samu ba sanda ta gama itama ma Amirah ta cinye farfesun tsaf ta shanye shayin se ajiyar numfashi takeyi.

"Nagode Anty Allah ya biyaki" ta fada tana sunkuyar da kai, se Asma'u tayi murmushi kawai tace "bakomai, ki samu kisha magungunan ki se ki kwanta ki huta. Ga ragowar abincin nan koda zaki buqata anjima Allah ya qara kiyayewa" ta fada tana nufar qofa.

Tashi tayi ta rakata tana sakeyi mata godiya ta kulle qofarta gam ta ciki karma ya dawo kenan ya shigo bata kwashe kwanukan ba ta haye kan kujera se baccin wuya ya kwashe ta.

Asma'u ma tana komawa part dinta kulle qofar tayi idan Bashir ya dawo da akwai key a hannunsa dan sunyi waya yaran sunce a can zasu kwana ma bazasu dawo ba. Sama ta wuce ta shiga wanka, seda ta gyara jikinta tsaf lokacin har sha daya tayi ganin Bashir be shigo ba yasa tayi kwanciyarta kawai dan daman dai yau koya dawo tasan bazasu kwashe qalau ba.

Bashir
Yana sauke su kai tsaye tsohuwar unguwar da suka taso ya wuce gurin Bala, Abokinsa ne tun na yarinta tare suka tashi a unguwarsu su Hudu Bashir, Marigayi Aliyu, Bala da Sadiq yayan Asma'u su hudun Abokaine na rai da rai tun daga Primary ajinsu daya har jami'a sannan suka rabu kowa ya karanci course dinsa daban.

A qofar gida ya tarar da Bala da yan majalisar sa kamar yanda yayi tunani, kashe motar yayi tareda jan kujerar baya sosai ya tokare qafarsa da stiyarin motar ,  zafafan numfashi yake saukewa a jere a jere  zuciyarsa jinta yake tamkar ana soyata a mangyada.

Me yasa meye dalili daya kasa samun nutsuwa tunda ya auri yarinyar nan? A shekara biyu an tafi ta uku da qara auransa be sakeyin sati daya na cikakken farinciki ba wai dama haka qarin auran yake ko kuma shine beyi dace ba.

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now