WASHE GARIWashe garin ranar da wuri muka shirya saboda su basayin African time irin namu na yan Arewa. Sosai nayi kwalliya da Doguwar rigar Lace baqi me Golden din zare na yafa mayafina a kafada na saka coge nida kaina na yaba kwalliyata dan na fito cas dani.
Da muka fito zamu tafi Anty se tsokanata take wai taga alamar fa Zawarcin nan me lasisi nake zuba to dai nayi a hankali kar na sa maza suringa karo a hanya a garin kallo na.
Bashir ne ya tafi da yara mazan a motar sa harda Amirah suka tafi, daman bamu hadu ba a bakin Amnah naji cewar da Amiran aka tafi nayi murmushi kawai a raina ni kadai nasan tsiyar da zan qulla mata tunda nidai ban gayyaceta ba ai, A motata muka tafi tareda Anty da yammatan harda sabuwar yata da tasha kwalliya dan tun dare na gyara musu gashin su ita da Farida sunyi kyau sosai cikin rigar jiya kamar wasu Yaya da qanwa haka muka rankaya muka tafi.
Sanda muka isa lokacin an fara shiga dakin taron, sallama Amnah ta mana ta wuce gurin Yan ajinsu ni kuma na tsaya dakko Get pass dan suna motata tun ranar da aka kai mana ban cire su ba nasan su Bashir ma basu shiga tunda dole su jira pass din, murmushi nayi sanda na fito dasu na qirga.
Guda goma ne cif, daman guda hudu suke bawa ko wanne dalibi idan kana son qari seka siya dan haka na qara guda shida ya zama teburi daya muka kama kenan, nida yarana banda Amnah mu bakwai se Anty ta takwas ga Bashir tara ragowar daya kuma daman na siyane kawai dan teburin me Goma ne to yanzu ga sabuwar yar da nayi shi kenan mun cike shi.
Haka kawai naji dariya ta kama ni sanda na hango Amirah yanda taci uwar kwalliya kai ka rantse wata dinner auren qawarta zata tafi se wani karairaya take a gefen Bashir hannunta cikin nasa, wani ikon Allah se banji komai a raina ba illah ma dariya data bani kawai dan a yanda take abun kana gani kasan irin da gayyar nan take dan ta bata mun bata san ko a kwalar rigata ba.
Mijin nata ma da da na dauka na dora akai yanzu na sauke nima na huta.Seda na qara gyara fuskata tsaf kafin na kulle motar na fito ina gyara zaman gyalena a kafada daya, cikin takun yauqi da yanga na qarasa inda su Bashir suke ina jin yanda idon mutane yayi mun caa a raina na shiga karanta 'A'uthubikalimatillahi tammat min kulli shaydanin wa hammatin wa min kulli aynin lammati' saboda mugun ido haka na qarasa inda suke kallo daya nayiwa Bashir daya watso mun idanunsa da suka fara rinewa da bacin rai nan take na dauke kaina ina murmushin qeta.
A saitinsa na tsaya fuskata dauke da murmushi na gaishe shi, be amsa ba se matsowa da yayi bayan ya saki hannun Amirah da tunda ta ganni ta shaqa tayi fam se wani harare harare takeyi kuma dai baze wuce tsabar hassada da baqin cikin gani na bane ya saka. A daidai kunnena ya tsaya idonsa akan fuskata yace
"Meye kike yi haka Ma'u baki kalli kanki a mudubi ba da zaki fito a haka cikin wannan kwalliyar? Jifa yanda maza suke kallonki dan Allah ki koma nasan bazaki rasa Hijab ko Abaya a mota ba ki saka".
Wata siririyar dariya nayi kafin nayi qasa nima da murya yanda shi kadai ze ji abinda na fada nace masa
"Ai daman saboda mazan su kalleni nayi, ko ka manta a kasuwa nake yanzu ne?"
Ina fadar haka na janye daga kusa dashi ina ji ya na kira sunana amma nayi kamar ma banji ba, katinan hannuna na fara bawa yaran da akwai table Number dan haka sukayi gaba, na miqawa Anty nata na miqawa Bashir daya sannan na juya ina cewa Anty"Muje toh, Baban Ali seka shigo koh" nayi gaba abuna dan ban nuna nasan da wanzuwar wata halitta ma a kusa dashi ba, hannuna ya riqo da sauri na waiwaya na watsa masa wani mugun kallo da ni kaina bansan na iya shi ba, se yayi saurin sakina yana cewa
"Yi haquri amma dan Allah kije ki.."
"Karka sake mun haka, da mutunchi na kazo kana kamani a gaban mutane bana so, sannan baka da hurumin da zaka gaya mun abinda zanyi yanzu ko wanda zan bari ka gane" na fada ina qara daure fuska.
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.