Takun kumi Bashir ya sakawa Amirah na daga gida se makaranta hakan ya taqaita duk wata firirita data fara dan yanzu ba inda take zuwa ba kuma wanda yake zuwa gurinta ban dai sani ba ko idan ta tafi gidansu tana yin hirar a can. wata rana nayi baquwa, maqociyata ce Maman Ahmad ta shigo muna zaune su Amirah suka shigo daga makaranta.
Uniform dinsu irin me guntun skirt din nan me da riga me dogon hannu se doguwar safa da dan qaramin hijabi dan haka sosai kayan suka bayyana qirar jikinta musamman ga wata tafiya data samu a kwanakin nan takeyi tana gantsaro qirji.
"Maman Aliyu wai qanwar kice wannan ma" Ta tambaye ni bayan da suka wuce ciki, se na kalleta ina murmushi nace
"Eh, qanwata ce me kika gani?""Qanwarki ciki daya ko kuma ta dangi?" Ta sake tambayata ba tareda ta bani amsa ba,
""Gaskiya ba qanwata bace,qanwar Baban Ali ce diyar yayar mahaifiyarsa"
"Lallai Maman Aliyu se a barki, yanzu duk yayan danginsu qanana ki rasa wa zaki dakko se wannan qatuwar budurwar zaki ajiye a gida wai cousin din mijinki kina kallon Yarinya wanda be sani ba in ya kalleku ma se yace kishiyoyine wallahi nidai bazan iya ba, kema kuma tun dare ne miki ba kisan abinyi tam" Maman Ahmad din ta fada.
Se nayi murmushi nace "Girman jiki ne fa kawai Maman Ahmad ko sha shida bata cika ba ina ga idan ma Bashir kike tunani nasan babu abinda zeyi da ita ko aure zeyi baze nemi qaramar yarinya ba balle wannan da sam ba tsarar sa bace"
"Ai wallahi ta wuce kice mata yarinya dan duk abinda mace take taqama dashi gashi nan a jikinta dadin da dawa ga quruciya meze dami namiji da qananun shekarunta bayan kina kallo yanzu yayin yan sha shidan sukeyi, shiyasa randa kika aiko su da Amna ko palour ban bari sun shiga ba dan Abban Huzaifa yana nan shi daman ido a farar fata, tun wuri kisan nayi wallahi kafin kiji kidan Janaral a sama".
A lokacin jin Maman Ahmad kawai nayi bawai na dauki abinda take fada da muhimmanci bane dan na yarda a zuciyata Bashir baze taba kallon Amirah a matsayin mace ba balle har yayi sha'awar auranta.
Yarinyar da banda kyara da tsangwama babu komai tsakaninsa da ita har haushi nakeji idan yayi mata wani abun, barar magi na bawa Amirah idan har na kuskura Bashir ya sani to ranar baze ci abincin ba saboda yanda yayi mata tambarin qazanta balle har takai ace ze aureta na tabbatar wannan ko a mafarki ba abu ne me yuwuwa ba.
Shigarta SS3 yasa ta qaro wani sabon tsagwaron rashin kunya da fitsara. Ganin ta takeyi kai daya dani dan yanzu idan na gaya mata magana ma se ta ga dama zata aikata, fita kuwa ko Bashir ze kasheta idan ta dawo setaje daman tuni ta sallama Islamiyya ta dena zuwa qarin daurin gindin data samu a gurin Addah harma da Dada kanta dan sunce data kammala makaranta aure zasuyi mata dan haka dole a barta ta fara tsayuwa da samari ta samu wanda zasu daidai ta a ciki.
Nima banqi ta tasu ba tunda har aure za'ayi mata ya kamata a barta ta farayin zancen dan haka koda Bashir yace sedai tabar masa gida ko kuma in zatayi zancen ta ta tafi gidan su se nace masa baza'ayi haka ba.
Dakyar na lallashe shi ya yarda sedai ya kafa mata sharadan kar ta kuskura ta mayar masa da gida centre tara samari duk randa ya ga sama da mutum biyu suna zuwa gurinta se ya mugun saba mata daga nan ta fitar da wanda take so a ciki ta sallami daya amma da yake me kunnen qashi ce kullum da wanda zata gayyato yazo gidan.
A cikin samarinta akwai wani Yaro Sadam, irin fitinannun yaran masu kudin nan ne. Tana bala'in sonsa musamman yanda yake mata barin kudi duk sanda zezo haka ze ciko ledoji niqi niqi da kayayyaki ya kawo mata sannan haka zebi su Aliyu da kudi idan sukaje suka gaida shi wani sa'in harni yake shiga ya gaisar,
yana da kirki amma idonsa a bude yake na kuma tabbatar ita kanta Amiran ba dagaske yake son ta ba duk yanda kuma naso na nisar da ita qarshe dukda ba kai tsaye ta fada ba se jin ta nayi tana cewa duk baqin cikin mutane seta auri Sadam da kowa ze ringa wani ce mata ba auranta zeyi ba, daga ranar na cire bakina a sabgar samarinta, Allah Allah nake ma ta qarasa makarantar ayi mata auran kowa ya huta.
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.