Ranar Juma'a Amirah ta tafi Lagos, da yake saukar Yamma tayi seda Bashir ya tashi daga gurin aiki sannan ya biya ya dakkota suka wuto gida.
Ina zaune dakina Jafar ya shigo da gudu yana cemun
"Mami Abbi ya dawo".
"To sannun sa Jafar" na fada ina duba wani document da aka turomun daga gurin aikin mu."Ai Mami ba shi kadai bane ma tare suke da Anty Amirah" Jafar ya sake fada, se naji kamar an saka mun stop, na dago na kalli yaron kamar me son tabbatar da abinda ya fada se kuwa ya daga mun kai yana sake cewa
"Ita ce tazo gasu Ahmad can ma sun tafi gurinta kuma naga da Akwatunan kayanta qila ta dawo gidan kenan ko Mami?"
"Kaje ka kirawo su magriba tayi" na fada kafin na mayar da kaina kan abinda nake yi amma sam ban gane komai ba. Idan nace zancen zuwan Amirah be dake ni ba nayi qarya ta tabbata kenan dagaske saboda ita Bashir ya sake ni tunda ga ta nan ya kawo ta nan din.
"Allah kaine Allah, kayi mana sakayya akan duk wanda ya cutar damu" na fada a fili bayan na ajiye Tab din hannuna dan sam na dena gane abinda nakeyi. Tagumi na rafka, se kuma na janye nace da kaina "Tagumin fa be ganni ba, tun wuri gara na tattara shirgin Baban Ali a gefe na fuskanci abinda ze tun karo ni a gaba" ina fadar haka na miqe na shiga Bayi nayi wanka.
Ina cikin shafa mai Muhammad ya shigo da leda a hannunsa da ban san ko menene a ciki ba.
"Mami wai gashi inji Anty Amirah ta kawo miki tsaraba" ya fada yana ajiye ledar a kusa dani, har ya juya ze fita na janyo shi, se da na zare masa ido kafin nace
"Dauki ka fitar can bola kayar, idan na kuma ganin ka shiga gidan nan idan sena cire maka kunne, wuce kaje ka kirawo Ahmad daman kune masu shegen yawo ai bini bini kun tafi can".
Haka na cigaba da shiryawa ina mita, seda na sake tara su gaba daya naja musu kunne akan babu su babu zuwa gidan Amirah, idan ma uban suke son gani se su jira ai yana fitowa su ganshi a waje su wuto gida amma ban yarda wani ya sake ya je gurinta ba.
Washe gari da yake Asabar ne bamu tashi da wuri ba se gurin goman safe dan haka kafin muci abinci muyi wanka an fara kiran sallar Azahar.
Aliyu ne ya sa su a gaba suka wuce masallaci da suka tashi dawowa shi kadai ya shigo ba tareda sauran ba.
"Aa Yaya ya naganka kai kadai ina qannen naka" na tambaye shi ina gyara Hijabin jikina dan zan leqa gidan Anty, bata jin dadi kwana biyu itama.
"Mun taho a hanya sukaga Abbi shine ya jasu gidansa" Aliyun ya fada yana zama akan kujera, se nayi qwafa nace "wato basuji abinda na gaya musu jiya ba ko nasan Jafar ne ze jasu za kuwa su dawo su same ni, Faridah taso ki rakani ke kuma Amna idan kin gama cin abincin in zaki zo toh" na fada ina nufar qofa.
Kallo daya nayiwa gidan Bashir shima bisa kuskure na shige gidan Anty, ban zauna ba ganin Baba yana gida dan a zatona yana gidan uwargidansa ne yau dan haka a tsatstsaye nayi mata sannu yana ta in zauna mana nace Aa anjima na dawo muka fito, ina sako qafata waje nayi kyakyawan gani da Bashir tareda matarsa saboda tsabar sabon salon munafunci ta dauki Ahmad se rinjayarya yake kamar zasu fadi suka shiga mota, inajin Ahmad din yana cewa
"Mami, Abbi ga Mami nan ba tareda ita zamu je ba" ko iskar su ban waiwaya na kalla ba na shige gida. Ban kai ga cire Hijabi na ba naji an turo qofar an shigo ga kuma qarar takalmi qwas qwas alamar dai macace se na waiwaya naga waye ido na ya sauka akan Amirah.
Fuskarta dauke da Fara'a ta qaraso cikin palour nidai ina tsaye har ta samu kujera ta zaune tana waige waige. A lokacin Allah kadai yasan abinda nake ji a cikin zuciyata amma na rigada nayiwa kaina fada, badai ni na sake yin wani tashin hankali akan Bashir ba tunda dai yanzu babu abinda muka hada dashi dan haka nima sena fasa cire Hijabin na zaune a kujerar da take kallonta fuskata a hade ba tareda nayi magana ba.
ESTÁS LEYENDO
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.