Part 33

1.3K 103 9
                                    

ASMA'U
Mun rubuta jarabawar Jamb cikin Nasara kuma ko wannen mu ya samu isashshen makin da ze samar masa gurbin karatu a fannin daya zaba yanzu se jiran sakamakon SSCE mukeyi.

A dan tsakanin Baffa ya taramu, daman munsan maganar bazata wuce ta aure ba dan haka tun kafin ranar kowa ta fitar da zabin ranta dan dukkan mu wannan karon yan Aure ne maci gaba da karatun a can.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa ni, Alawiyya, Yaya Fati, Yaya Bilkisu se Junaidiyya mune yan candyn Bana, cikin sakin fuskar da Baffa yake da ita a cikin iyalansa muka dan taba hira kafin ya gabatar mana da maqasudin kiran namu.

"Na kiraku ne dan naji ra'ayinku dukda dukkan ku nasan kunyi jarabawar shiga Jami'a me kuka zaba aure ko kuma Bokon za'a ci gaba?"

Seda muka kalli juna muka qara sunkuyar da kawuna kafin muka hada baki gurin cewa "dukka gaba daya muka zaba Baffa".

Alhaji Qarami da yake gurin ne ya shiga tsokanar mu da cewa "wato gaku cinye du ko zaku ce wani dukka kuka zaba to baze yuwu ba sedai ku dauki daya" se Baffa ya katse shi yace

"Aa bana so karka takuramun yara, shiyasa bana saka iyayenku mata a cikin magana ta dan karma wata ta tilasta su fadar abinda ba ra'ayinsu ba shine kai yanzu zaka zo kana tsokanarsu ko, gasunan se su gaya maka su waye surukan naka idan yaso se ka ci gaba da bincike muga abinda hali zeyi".

Da daddaya kowa ta fadi sunan rabin ranta, nice ta qarshe harda gyara zamana na bude baki zanyi magana Alhaji Qarami ya tare ni da cewa
"Ai ke nasani Amaryar ta Excellency ko?" (Yusuf kusan abokin Alhaji Qarami ne dukda a shekaru Alhaji Qaramin ya girme masa sosai, yaro ne a cikin manya da Allah yayi masa nasibi sosai a rayuwa, Asalinsa dan Bauchi ne kuma guri daya suke aiki da Alhaji qarami a Abuja tunda yaga Ma'u yace a duniya nan shi yaga mata haka kuwa take garashi kamar kwallo amma be sare ba kullum yana kan binta.
Yanzu haka ya shiga siyasa ne ya tsaya takarar Dan Majalissar Taraiya dan yace se ya kai har shugaban qasa in Allah ya yarda shiyasa suke kiransa da Excellency).

Lokaci daya na hade fuskata kamar ban taba murmushi ba ina kallonsa nace "Ni Bashi bane Alhaji Qarami ai na gaya masa ni ina da wanda nake so".

"Haba Ma'u yanzu kice bakyason Yusuf duk yanda yake bala'in sonki kullum cikin hidimar ki yake yana hanyar zuwa gidan nan" Alhajin ya fada, sena tunzura baki gaba kaina a qasa nace

"To ni nace yayi mun ne ai tun ranar da ya fara zuwa na gaya masa nacin sa ne yasa kashi ci gaba da zuwan ai".

Ze sake magana Baffa ya tare shi da cewa "ya isa Muhammadu barta ta fadi zabinta babu dole a al'amarin aure".

Karkacewa nayi ina murmushi nace "Ni Baffa Yaya Bashir nake so".

Se Baffa ya kalli Alhaji Qaramin da son qarin bayani, cikin takaicin qin zabar Abokinsa da banyi ba yace "Wai wannan yaron Bashir Abokin Abubakar dan gidan Alhaji Ahmad na qasan layin nan take nufi".

"Toh toh na gane dan waje Amadu me Mota kenan toh ai babu laifi se aje a cigaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da Alkahiri gaba daya"(Inkiyar Baban su Bashir ce saboda ya tabayin Direban Babbar mota yana saurayi tun sannan ake kiransa haka)".

Godiya mukayi wa Baffa kafin muka fice kowa ranta qal.
"Amma Ma'u baki kyauta ba tayaya Babban Yaya ze miki magana ki musa masa" Bilkisu ta fada bayan da muka yi gaba nida ita, sena kalleta nace "kiji ki Yah Bilki da wata magana, so kike nayi shiru haka kawai a cuceni yanda yake so na auri abokin nan nasa tsaf ze iya zuga Baffa, yanzu kuwa dana fada a gabansa kinga ai nayi maganin abun".

"Dukda haka da kin sani bari kikayi ki same shi ke dashi ki gaya masa, kuma ni wallahi nafi miki sha'awar Yusuf din ma gashi Kyakykyawa dan gaye ga Kudi".

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora