Part 34

1.3K 113 11
                                    

Ranar Juma'a aka daura aure na da Bashir, Juma'ar data shiga cikin jerin rana kun tarihin rayuwata na farin ciki da bazan taba mantawa da su ba. A qa'ida ranar da aka daura aure a gidan mu ake kai Amare amma mu ba'ayi haka ba saboda Dinner da manyan Yayyenmu suka shirya zasuyi a daren ranar sauran Yayyen mu mata se tsiya sukeyi wai an fi son mu su kuwa kamar ana jira da an daura ake kwashe su.

Da yake tun ana sati daya da biki muka san da shirin Dinner, nasan dole sauran Angwaye zasu gwangwaje suyi shiga ta alfarma tunda suna dashi dukda Bashir ma nasan ze yi iya qoqarinsa amma baze iya kamo su ba saboda tattalin arziqinsu ba daya bane su duk masu dashi ne.

Haka na samu Baffan mu na tasa shi da naci seda ya bani shadda yadi goma cikin irin wadanda yake dinkawa ni kaina bansan kudinta ba kawai dai nasan suna da kyau kuma ko cikin Mutane ina dadewa banga wanda ya saka irinta ba sefa manyan irinsa.

A gurin Yah Mustapha  na samu hula harda takalmi daya siya dan daurin aure saboda duk gidan mu ya fisu gayu, dakyar ya bani wai order su yayiwo takanas seda mukayi ma zan biya kudin rabi nidai dana samu suka zo hannuna nace a gudunmawar sa, yana ji yana gani na masa fin qarfinsu se na bawa Yah Abubakar shaddar nace ya kaiwa Bashir dinki tunda abokinsa ne yasan Size dinsa na roqeshi dan Allah karya gaya masa ina so na bashi mamaki ne.

"Ma'u kenan, yanda kike son Bashir kike tattalin sa Allah yasa kar wata rana yayi miki halin mu na maza" abinda Yah Abubakar ya gaya mun kenan a lokacin da se naji jikina yayi sanyi.

Gaba daya daman na lura dashi kamar hadi na da Bashir beyi masa ba na rasa dalili dan har tambayarsa na tabayi yace mun babu komai, da yake daman shi ba mutum ne me yawan magana ba se na bar maganar kawai nasan idan da Bashir nada wani mugun abu baze barni na aure shi ba.

Tsaf na hade kayan nan bayan an dawo daga daurin aure angwaye sun shigo aka dauki hotuna, masha Allah gaba dayan mu munyi kyau kuma ko wacce ta dace da zabin ta se fatan Alkahiri dangi da abokan arziqi suke yi mana. Suna shirin ta fiya nayiwa Sadiya qawata rada dan daman ita na bawa ajiyar Kayan tayi maza taje ta dakko su, seda suka fita tabi bayan Bashir din ta bashi.

Muna zaune a bangaren da qawayen mu anan ta hira irin wadda ko wanne qawayen Amarya sukeyi idan ana biki, hayani ya na tashi wayata dake hannuna tayi qara, Bashir ne daman zaman jiran kiransa nakeyi sena miqe da sauri na shige bandaki na kullo qofar ko naji maganar sa dakyau.

"Ma'una kayan menene wadannan, ina kika samo shadda me bala'in tsada haka?" ya tambayeni bayan dana gaishe shi.

"Kamanta an jima akwai Dinner da za'ayi, kalar kayan da zan saka ne zamuyi Anko".

"Ina sane har ma nayi dinki nima, mantawa nayi sam ban ma gaya miki kalar nawa kayan ba ai" ya fada daga daya bangaren, sena marairaice nace

"Se ka ajiye su gobe ka saka idan za'ayi budar kai nidai yau wannan nake so na gani a jikinka".

"Shikenan an gama Amaryata, na tabbatar yau ke kadai ce zaki fini yin kyau a gurin nan"

"Haka nake so Angona yafi na kowa, se anjiman idan kunzo, kar dai ku bata lokaci qarfe takwas zuwa Goma Baffa yace za'a tashi" daga haka mukayi sallama na kashe wayar.

A filin tsakar gidan mu aka shirya za'ayi dinner, tun la'asar masu decorashan din da aka dakko suka katange iya inda suke buqata suka fara aikin su, kafin magriba sun gyara guri tsaf se ka rantse wani babban dakin taro ne.

Seda mukayi sallar magriba sannan aka fara shirya amare, munyi kyau har mun gaji cikin dinkin riga da skirt na wani hadadden material da akayi mana kowa da kalar nata da ze dace da shigar Angonta, munsha daurin goggoron mu me kyau dan fa fashion designer guda aka dakko ta shirya mu dukda a sannan ba'a fara kwalliya me fente fenten nan ba amma ta tsatso mana kyau da iya abinda ake amfani dasu a sannan.

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now