Part 52

2.1K 201 65
                                    

ENGINEER BASHIR

Watanni ukun da suka shude Bashir yayi su ne cikin wata rayuwa me cike da qunci da rashin sukunin zuciya. Ya sake zama shiru shiru duk da daman shi ba me yawan magana bane amma a yanzu kana kallonsa zaka san shirun sa yana da nasa ba da tarin damuwa da yake ciki.

Abun ne ya hadar masa goma da Ashirin, kewar Ma'unsa tana neman zauta shi ga rashin kula da rashin abinci me kyau da baya samu a gidansa kullum se tashin hankali da hayaniya idan ya fita har baya so lokacin tashi aiki ya dawo gida.

Gaba daya a yanzu idan ka ganshi se ya baka tausayi yanda gaba daya ya fige ya fita hayyacinsa, hidimomi sun sako shi a gaba, wata daya da rabuwarsa da Asma'u gaba daya ya kasa gane kan cefanen gidansa.

Be taba sanin cewa Neman da Asma'u takeyi rufin asirinsa bane se ranar daya dawo daga aiki ya tarar da Amirah ta dafa masa farar shinkafa ta soya manja da yaji ta ajiye masa a ranar Azumi yayi, kuma kafin ya fita da safe ya gaya mata azumin yakeyi be shigo gida ba seda yayi sallar magriba dan haka yana shiga kan Dining ya wuce kai tsaye dan ya ci abinci.

Yana budewa yayi arba da abinda ta ajiye masa gaba daya se ya gagara bude baki ma yayi mata magana, mai da yaji a gidansa abinda rabon dako a ido ya ganta tun zamanin da yana Jami'a shine yau aka dafa masa a matsayin abin shan ruwa.

Yar gasken kuwa daya tambayeta dalili kai tsaye ta gaya masa cewar kayan miya sun qare kuma ita bata da kati a wayarta bare ta kirashi ta sanar masa shiyasa taga daya dawo bata girka komai ba tunda tana da yaji gara ko fara da mai dince tayi masa.

Yanzu shine ajiye buhun huna, shine cefane, dai da Maggi se ya siyo ya ajiye mata sannan in dai bashi ya duba ya sake siyowa ba babu ruwanta abinda yake da akwai shi zata sarrafa tayi abincin da kusan kullum Asarar sa akeyi dan yaran basa ci shi kuma bashida nutsuwa da kwnaciyar hankalin da zeci da yawa, da ya zauna cin abinci in sha Allahu seta qirqiro abinda zata bata masa rai ya tashi daga gurin.

Ya rasa wace irin macece Amirah da bata taba tashi kawo qorafi da mita se a lokacin da za'aci abinci ko lokacin kwanciya wadannan abubuwa suka taru suka sake dagula masa lissafi.

Be qara shiga uku ba seda Amirah ta fara laulayi. A iya saninsa bayan haihuwar da tayi an saka mata Implant a Asibiti saboda ta huta jikinta ya dawo daidai amma se gashi ba'a rufa shekara ba ta samu wani cikin.

Lokacin da yayi mata magana akan ya haka ta faru kai tsaye tace masa cirewa tayi sanda zata taho saboda itama tana so ta tara Yaya a dena mata gadara dasu, be ja ba ya barta tunda ai jikinta ne ta sani idan dadi taji idan ma wuya ce duk tafi kowa sani shidai tunda ta fara Amaye Amaye da wasu abubuwa ya tattarata ta koma dakinta dan wata muguwar qazanta ta farayi abin dai ba'a cewa komai.

A bangaren matsalar Ma'u kuwa yankewa kansa shawara yayi akan ze saka mata ido ne yaga iya gudun ruwanta, ze jira daga nan har shekara har zuwa sanda zata huce ta saurare shi a sannan baze sha wahalar shawo kanta ba su komawa auransu amma babu qarya yayi kewar Asma'u koma yace yana kan kewarta, fuskarta, muryarta, qamshin ta da gayunta daddadan girkinta ga murmushinta me saka shi manta kowa da komai kai wallahi dole ya maido da Asma'u rayuwarsa dan kuwa tabbas rasata babbar Asarace a gareshi.

Yanzu haka tun daya rabi da ita baya iya bacci saboda tunanin ta, idan kuwa har bacci yayi nasarar sace shi me nauyi to cike yake da mafarkin Asma'un.

Abu dayane yake dan kwnatar masa da hankali yanzu da be sake ganin wannan mutumin yazo gurinta ba, tun waccen ranar ma babu wani Namiji da ya sake gani tare da ita idan ba Yemi ba wanda ya bincika ya tabbatar abokin aikinta ne kawai babu wata alaqa a tsakaninau bayan ta aiki.

Sedai kuma guiwar sa tana yin sanyi irin yanda yaga gaba daya ta ci gaba da rayuwarta babu wata alama da take nuna tana da damuwa ko tunawa da shi dan yanzu ko sun hadu a hanya gaisawa sukeyi kamar wasu maqota, yanda zata gaisa da sauran mutanen da suke cikin layinsu shima irin wannan gaisuwar take yi masa babu wani abu da yake nuna sun taba hada wata alaqa ta soyayya bare har aje ga batun aure amma kuma baze sare ba, zeyi ta binta a hankali har zuwa sanda ita da kanta zata sakko ta neme shi.

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora