Part 13

1.2K 84 1
                                    

Addah, abinda ya faru waccen ranar.

Kuka riris Addah ta shigayi bayan data tabbatar da cewa Malamin nan dan damfarane, qarin tabbacin data samu tana tsaye wata da ta yankawa kanta kazar wahala ita ma ta zo neman malam Wizy anan suka samu daya daga cikin Almajiran ya fede musu abinda yake faruwa.

Wato dama shi ance aikinsa kenan kuma takamaimai basu san dan wacce unguwa bane. Haka yakeyi duk sanda suka tashi zasu je inda ba'a sansu ba su kama guri idan sun gama cin kasuwarsu ta watse ba zaka san ina sukayi ba.

Haka suka dauki hanya da me Adaidaita tana faman rusa masa kuka batayi aune ba taga yayi kwana da ita wata hanya daban, da taso tayi masa ihu ya zare mata wuqar dake boye a qugunsa dole Addah tayi shiru se yan idanu tana hawaye haka tana ji tana gani seda sukaje inda babu mutane ya kwace jakarta data zubo kudin raguna biyu ga kuma wadanda Hajia Balaraba ta bata na nata aikin duk ya kwamushe harda wayar ta sannan ya buga mata abu akai ta suma kafin ya kwasota ya kawota Asibiti ya tsere abinsa.

Seda ta kwana 4 a Asibitin sannan aka samu kanta ta dena iface ifacen kudinta da takeyi shima se bayan da Alhaji Murtala yayi mata horror sannan ta dauki dangana a fili a zuciya kuwa baqin ciki kamar zeyi ajalinta. Abu goma da ashirin gashi babu damar ta raba baqin cikin da wani ayi mata Allah shi qara dan ko Amirah bata jin zata gayawa bare tsautsayi yasa wani yaji zancen.

Amma fa wallahi an cuceta, Dubunta fa har dari da sittin dan iskan yaron nan ya lashe ga Hamsin din Balaraba. Wai ma wace toshewar basira ce ta same su kai wannan ibtila'i da yawa yake, amma bazata haqura ba wallahi insha Allahu seta nemo wanda ze mata aikin da Wizy ze kawo kansa da kansa ya biyata kudin ta (baki daddara ba ashe 😂😂).
Haka dai tace a sallame ta ta warke suka koma gida taci gaba da jinyar zuciyarta.

Dama damanta ma yanda Bashir yake ta rawar jiki akan ciwon nata, kamar yanda yace ya turowa da Naziru dubu dari yace ayi hidimar Asibiti dan ko babu auran Amirah ai Addah uwa take a gurinsa ze kula da ita kamar yanda zeyiwa Dadansa dan ma dai Addar se a hankali dai, already kuma Alhajin ya biya komai dan haka Nazirun ya danqawa Amirah kudin yace ko zasu buqaci wani abu inji Bashir. Wadan nan kudi ta qudure a ranta da taji dama dama zata kaisu a shaqo mata wuyan wizy kuma (Ai me rabon shan duka baya jin bari dama 😂).

Ganin yanda Bashir din yake ta tasu dan kullum sau biyun nan Safe da Dare se ya kira yaji ya jikinta yasa taga dama ta samu na yadda zata tura Amirah gurinsa, (wai nikam dole ne 😂😂 Allah sa dai ba rabon wahala ke kiran Amirah ba itama). Tunda sun gwada wacceb hanyar bata yuwu ba dan haka suka sake wata.

Sun san yanda Bashir yake da son yara ya kuka kwallafa rai akan cikin jikinta dan haka yanzu shine target dinsu, Addah batayi sanya ba ta karanta mata duk yanda zatayi, da Bashir din ya kira waya zata langwabe yau tace kanta anjima cikin ta, Aa jiri ne yake damu ta shidai se yace mata taje Asibiti ta kuma rage yawan zurga zurga saboda halin da take ciki. Ganin an kwashe sati biyu ana haka be ce ze zo ba ko ita ta tafin yasa suka shirya sabon plan.

Ranar Juma'a data kama Sati biyu kenan rabonsa da Gombe da daddare suna cikin waya tace bari tayi fitsari, bata kashe wayar ba ta ajiyeta akan sink ta dauki hand shower tana tsiyayar da ruwa kaman me fitsari se kawai ta fasa ihu.

Bashir da acan bangare yana riqe da waya yana jiran ta gama ya miqe a sukwane jin ihunta har yana tunkude cup din da Asma'u ta cika masa da Kunun Aya ya tuntsure a qasa take kuwa ya fashe.
"Lafiya meya sameki" ya tambayeta a kidime, seta fashe masa da kukan qarya tana cewa "Jini, jini ne yake zubomun" ta ci gaba da kukan.

Sosai hankalin Bashir ya tashi, idan be manta ba wancan karan da haka ta fara zubar da jini kafin Wani lokaci jaririn ya mutu a cikinta se inducing dinta sukayi ta haihu dan haka yake taka tsan tsan da abinda ze sake janyo faruwar hakan.

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now